Lifeless

449 38 27
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.


                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:-* https://www.wattpad.com/story/216211172?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=REAL-SMASHER&wp_originator=iDULEr4cbYBaNlbu1Jn%2Fk8DX2nZbRtRMTAcg2pxFMMfUGFk1z9aFc6%2Fd9W2e6A2RnIQZKGv9Ardrz4mEgzIHUGGWJPVZvHBymyNE3gmbgqze7v0Ckkh4LkBJdFvKDeF9

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.* 

      '''TSOKACI! Ban san ya ya al'amarin zai kasance ba,ko zan iya haɗa muku books biyu lokaci ɗaya 🤔,ga IN-LAWS nan tabbas,but i really don't think zan yi posting ɗinsa kullum,though shima KALLO YA KOMA SAMA ba kullum bane,but shi zan yi posting ɗinsa a working days,IN-LAWS kuma zai na zuwa muku a weekends,dan Allah kada a tambayeni littafin da ba shi nake updating a ranar da ba nasa ba,idan na samu dama kuma za ku iya ganin IN-LAWS har cikin working days,duk yanda Allah ya tsara haka ne zai kasance,but comments ɗinku zai iya canja min ra'ayi.'''

 
                               01

#Lifeless

*KANO STATE!*
'''@Zaria Road,Dangi Roundabout .'''
'''(Before the constructing of flyover)'''

         ***Tsananin zafin rana gami da ƙosawar al'ummar dake cikin cunkoson vehicles ɗin gurin,a ƙoƙarinsu na son su wuce daga cikin ranar da ake tsagagawa,tsayuwa cikin traffic jam shi ne abu mafi muni da tada hankali,wanda yake addabar talaka da duk wani mutumin dake tsaye wajen traffic light protocol dake roundabout na dangi,Zaria road a birnin Kanon dabo. Tun daga nesa kafin danja ta kai ga bawa mutane damar wucewa,ƙarar jiniyar ambulance ɗin da yake tunkaro gurin ya sanar da jimillar jami'an *KAROTA* gami da road safety dake wajen,hakan ya basu damar dakatar da gefen da suke wucewa suka saki hannun da motar ambulance ɗin ta biyo,kafin motar ta ƙaraso tuni vehicles da suke cunkushe sun wuce motar ta wuce ba tare da an samu wani matsala ba,kasancewar kowa ya san dokar titi ne motar asibiti da motar ƴan kwana²  ba'a tsare su a traffic jam,wannan dalilin yasa jama'a basu yi wani cece kuce ba,face addu'ar fatan alkhairi da kiyayewar ubangiji da suka bi motar da shi,da mugun gudu motar dake sharar uban gudu ta wuce,a bayanta wani haɗaɗɗen Tokunbo mai tinted maroon colour honda accord da muke ciki ya rufa mata baya,tun da motoci biyun suka biyo titin basu tsaya ba sai a cikin *AKTH*,direct muka nufi maternity ward,kafin motar ta samu damar tsayawa tuni nurses sun fito da gadon shiga da majinyata,a gurguje suna ƙarasowa aka buɗe bayan motar ambulance ɗin,lokacin da suke ƙoƙarin fito da ita daga cikin ambulance,a tare muka buɗe ƙofofi biyu na gaba na motar dake biye da ambulance ɗin muka zuro ƙafafuwanmu waje,dai² wannan lokacin kai baza ka iya tantance wane ne yafi wani shiga tashin hankali tsakanin kyakkyawan matashin ɗan kimanin 32yrs ko ni da nake kuka ba,a hakali na waiwaya na kalleshi idanuna cike da wasu hawaye,kafin nayi magana tuni ya juya ya barni tsaye a gurin,juyawa nayi nima na sauke fararen idanuna dake cike da tsoro akan nurses dake ƙoƙarin fito da matar dake cikin ambulance ɗin,wacce tsananin azabtuwa yasa cikin ƙaraji gami da azabar ciwo ta saki wani ihu tana sake dafe cikinta,ta ƙwalo min wani razanannen kiran da yasa ni nufar gurinsu da sassarfa *"FADWA!* Kina ina? Ki zo kusa da ni please,ki zo ki riƙe ni,kada ki bari su tafi da ni,mutuwa zan yi,kice su barni zan haihu da kaina,ga shi nan zai fito wallahi,zan haihu da kaina!" Ɗaya daga cikin nurses ɗin tana shafa gashin kanta da ya watse,cikin salon kwantarwa da mutum hankali take  faɗin "sorry madam ba za ki mutu ba,sai kwanan ki ya ƙare,za ki haihu lafiya" muguwar harara ta aika mata cikin masifa tace "ke dallah rufemin baki maƙaryaciya,kin san me nake ji ne?" Nurse jin haka tayi murmushi tare da jan bakinta tayi shiru,suka ƙarasa tattarata da ƙaton cikinta wanda ya sauka ƙasa suka ɗorata kan gadon a gaggauce suka fara turata zuwa cikin ward,har lokacin banda juya kai,ihu gami da kiran suna na babu abunda take yi,shi kam Yallaɓan yana biye da mu yana buga waya,a haka muka bisu cikin ward,hawayen tausayin ƴar uwata suna zubowa fuskata,lokacin da ake ƙoƙarin shiga da ita ɗakin haihuwa nayi baya a hankali na tsaya,da ƙarfi ta ɗago tana miƙo min hannu da faɗin "don't leave me.. Please ƙanwata" tafiya na ci gaba da yi zan nufeta,da sauri naji an riƙo min hannu,nayi saurin ɗaga manyan idanuna masu cike da tashin hankali na sauke a kansa,a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe,kyaunsa da cikar kamalarsa suka bayyana,dogo ne skin ɗinsa mai duhu,idan ba magana yayi ba ka kalleshi sai ka rantse irin black americans ɗin nan ne,muryarsa a low tone kamar ba ya son magana yace "kina da hankali za ki je kusa da ita,kin san yanayin da take ciki? Idan baki sani ba,ta riƙe ki ba za ta sake ki ba sai ta haihu" idanuna suna sake ciccikowa da hawaye na rausayar da kai gefe,kafin na yi magana cikin wani irin muryar dake tattare da nutsuwa da jan hankali ya kira suna na *"FADWA!"* Wani irin faɗuwa gabana yayi saboda yanayin da ya kira ni,ba tare da na iya ɗago kaina na kalleshi ba saboda kwarjininsa na amsa muryarta a sanyaye,yayi shiru kamar ba zai ce komai ba duk da ya ji na amsa,then a hankali yace "sit down here" ya nuna min kujeran kusa da shi,babu musu na fara ɗaga ƙafata a hankali har na ƙarasa kusa da shi,tun da na zauna ban yarda na sake ɗagowa na kalleshi ba sai ita nake kallo tana miƙo min hannu,banda hawaye babu abunda nake sharewa akai²,har nurses suka shiga da ita suka rufe ƙofar,daga nan muna kijo ihunta da kiran da take min "wayyo Allah! *FADWA* zan mutu,mu koma gida pleasee! Ku zo ku ɗauke ni mu tafi.. Sai da na faɗa muku ba na son zuwa nan kuka takura,ai ga shi nan za su kashe ni!" Dai² nan allurar da suka mata yasa maganarta ya fara yin ƙasa sai salatin da take da different addu'o'i. Tunda aka shiga da ita,banda addu'o'i babu abunda nake jerawa,tsabar kukan da nake idanuna har sun sauya launi sun tasa,ganin yadda ƴar uwata take cikin azaba,hakan ya fi komai tayar mun da hankali,dai² lokacin Dr Abraham ya ƙaraso yana gyara zaman lab coat ɗinsa,a gaggauce yana zuwa bai jira sunyi magana ba ya ɗago mana hannu ya shige cikin ɗakin,sai lokacin yayi ajiyar zuciya,then a hankali ya zauna yana shafa fuskarsa. Almost 1 hour and half muka ɗauka zaune a gurin,shi kam idan ya gaji da zama sai ya miƙe yana ta zagaye gurin,a haka Dr Abraham ya fito yana cire mask dake saman fuskarsa ya ƙaraso inda muke,ya fara miƙa masa hannu da faɗin "Congratulations *TAFEEDA* it's baby girl" wani irin sanyayyan murmushi yayi yana yin ƙasa da idonsa yace "thank u Dr,yaya suke?" Dr Abraham yayi ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah! Duka suna cikin ƙoshin lafiya" ya sake yin murmushi yace "maa sha Allah!" Dr Abraham yayi masa murmushi yace "haka ne,but akwai wani ɗan problem idan babu damuwa muje office na ganka" yana lumshe idanuwa a hankali yace "Ok!" Sun fara tafiya ya waiwayo yana kallona,silently yace "ki jira zan dawo yanzu" a sanyaye na gyaɗa kai ban yarda na ɗago mun haɗa ido ba,sanda suka bar wajen na tuna ya kamata na kira gida na faɗa musu zancen haihuwar,sai kuma nayi shiru saboda ni dai ba waya ne da ni ba,gaba ɗaya na rasa tunanin da zanyi,saboda na san idan ban kira na faɗa ba tawa ce za tayi zafi,ni Hjy Umma za tayi ma faɗa tace dan ba ƴar uwata bace shi yasa nayi shiru,a hankali na rufe idona ina jin zuciyata tana tsinkewa,ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba ina zaune shiru ya ƙaraso gurin,ban san ya zo ba sai maganarsa naji,a tsorace na buɗe idona da suka ciko da hawaye,yana kallona kamar zai tambayi abunda yasa na firgita sai kuma naga ya fasa,ya miƙo min waya mai idon mujiya yace "ki kira gida ki sanar musu" haɗiye wani yawu nayi da kyar na gyaɗa masa kai,na kai hanuna ta karɓa ya bini da kallo kafin ya sake barin wajen,ina ganin ya tafi na buɗe wayar,naga babu security akai,a hankali na ƙurawa screen ɗin ido ina kallo,picture ɗinmu ne ni da ita a kai munyi murmushi,kallo ɗaya za kayi mana ka san muna da alaƙar jini,saboda kamar da muke yi,sai dai na fita haske sosai,ita kuma ta fi ni girma da shekaru,ajiyar zuciya nayi a hankali na shiga contact list,sunan Hjy Umma na lalubo na danna mata kira,time-time nake maimaita haɗiyar saliva's ƙirjina yana bugawa da ƙarfi,kiran yana shiga nasa wayar a handsfree saboda wajen babu mutane,daga ɗayan ɓangaren ana ɗauka ko sallama babu muryar matar ta furta *"SHAHEED!* Yanzu nake cewa a kira min matarka naji,kuna lafiya?" Daurewa nayi ina runtse ido saboda sanin masifar matar,muryata tana shaking nace "ba shi bane Fadwa ce,ina yini?" Tsaki mai rai da lafiya Hjy Umma tayi,zuciyarta tana tafarfasa a fusace tace "me wayar mijin ƴata yake yi a gurinki? Kinibabbiya munafuka,me kika kira ni kice min?" Hawaye suna zubowa fuskata na daure zan yi magana,kafin na kai ga yin hakan muryar Hjy Umma ta katse ni cikin masifa "ina Fatiman take,me yasa baza ta kira ni ba sai ke? Uban me wayarsa ya shigo hannunki yake yi?" Sake haɗiye saliva's nayi cike da tsoro ina share hawaye cikin in'ina nace "uhmn! Dama muna asibiti ne,ya ce na kira na faɗa ta haihu" guɗa Hjy Umma ta rangaɗa cikin shewar murna tun ban gama faɗa mata maganar ba tace "me muka samu?" A hankali nace "basu fito da ita daga ɗakin haihuwar ba,amma likitan ya ce *MACE* ta haifa" da wani irin murya mai cike da sanyi Hjy Umma tace "Mace kuma?" Na gyaɗa kai kamar ina gabanta nace "ehh! Haka Dr ya faɗa" wani irin taɓe baki tayi jikinta a sanyaye tace "toh ga mu nan zuwa" tana faɗin haka ta kashe wayar haɗe da yin tsaki,su Mardiyyah dake zaune suna jira ta gama wayar har rigegeniya suke wajen tambaya "Hjy Fatima ce ta haihu?" Ta taɓe baki tace "itace,sai dai muradin mu bai cika ba" taɓe baki suka yi suma suna harare² kamar da wani suke yi,sai dai babu bakin magana. A hospital kuwa bayan Hjy Umma ta kashe wayar,ajiyar zuciya mai nauyi nayi haɗe da yiwa Allah godiya,not too long aka fito da Aunty Fatima aka wuce da ita special room,nabi gadon da take kai da ido ina sakin sanyayyan murmushi,can bayan wani lokaci nurses ɗin suka fito,na tashi da sauri na ƙarasa gurin wanda tayi fitowar ƙarshe,a sanyaye na mata sallama ta amsa,nace "ina yini?" Murmushi tayi min tace "lafiya lao ƴan mata,ya kike?" Nace "lafiya lao" tana kallona tace "ya akayi?" Ina ƙiƙƙifta idanuwa a hankali nace "arghm! Dan Allah zan iya shiga na gansu yanzu?" Murmushi tayi tace "why not? Ba tare kuke da Shaheed ba?" Na gyaɗa kai nace "tare muke" tace "u can,but kada ki dameta da surutu kin ji?" Nace "bazan yi ba" tace "good! Shiga tou" nayi murmushi a hankali nace "thank u!" Tayi min murmushi itama then ta wuce ta bar gurin,da sauri na ƙarasa ina sakin murmushi na ɓude ƙofar na shiga ba tare da na bari ya yi making any sound ba tunda ance min kada nayi abunda zai tasheta,sanda na shiga ɗakin a hankali nake tafiya har na ƙarasa gurin gadon,na kalli fuskar Aunty Fatima ganin tana bacci nayi murmushi,then na ƙarasa kusa da baby'n dake cikin lallausan abun ɗaukan jarirai pink color an shiryata cikin kayan sanyi,overall riga sai hula da hand socks,ina kallon kyakykyawar fuskarta da murmushi nayi kissing baby pink lips ɗinta,wani irin son yarinyar na dunga ji mara misali yana zaga jinina,a haka na koma kan kujeran dake ɗakin na zauna ina ɗauke da ita,na fara yi mata addu'o'i ina tofa mata,buɗe ƙofar akayi kafin na ɗago ƙamshin da naji ya sanar min Yaa Shaheed ne,sai ban ɗago ba har ya ƙaraso,sanda ya wuce ya fara duba Aunty Fatima,kafin ya waigo ya kalle mu ni da Baby'n,kamar mai counting words ɗinsa yace "tun yaushe suka canja musu ɗakin?" Ban ɗago ba har lokacin nace "ba'a jima ba" ya gyaɗa kai a little,har ya juya sai kuma naji ya ce "kin kira kin sanar musu?" Na gyaɗa masa kai nace "ehhh!" Yace "wa kika kira?" Ɗagowa nayi na kallesa muka haɗa ido,da sauri na sauke kaina nace "Hjy Umma!" Tsayawa yayi yana kallona sai dai bai ce komai ba,da naji shiru na ɗago a hankali kamar munafuka,yana min wani kallo yace "me yasa baki sanarwa Aunty ba?" A hankali nace "ai su ya dace su fara sani" bai ce min komai ba kawai ya juya min baya,ina kallonsa na ɗan taɓe baki ina ƙunƙuni nace "to ba itace mamarta ba,so kake na faɗawa Aunty suji a bakinta aga laifinta?" Saurin juyowa yayi yana buɗe idanuwa yake kallona kamar yana zazzaro min su yace "what did u say?" Da sauri nace "ni fa ban ce komai ba,addu'ah kawai nake ma Baby" ya min wani kallo ya juya,a hankali na murguɗa bakina ban sake magana ba na tashi na kai masa Baby'n nace "ga ta" bai juyo ya kalle ni ba yace "na ganta" daga haka bai karɓeta ba ya juya zai fita,na bishi da kallo baki sake ina mamaki,sanda yaje ƙofa zai fita bai juyo ba ya ɗan tsaya yace "what are u looking for?" Da sauri na zaro idanuwa nace "no.. Nothing" yace "zanje na dawo yanzu" ina turo baki nace "tohh!" Yanda na amsa yasa shi juyowa yana kallona yace "ko da akwai wani abu?" Nayi saurin kaɗa masa kai nace "a'a babu!" Yace "sai na dawo" a hankali nace "Allah ya tsare hanya" yace "ameen!" Yana taɓe baki then ya fita,bayan tafiyarsa ina ta zaune a ɗakin ni kaɗai na yi shiru sai kallon Baby'n dake hannuna nake wanda take motsi alamun tana son tashi,akayi knocking ƙofar,a hankali nace "yes! Come in" aka buɗe ƙofar,kyakkyawar matar dake shigowa fara wanda baza ta wuce 45yrs ba ta shigo,na ɗago ina kallon ta na buɗa idanuwa da muryar excitement nace "Aunty oyoyo!" Tana min murmushi ta ƙarasa shigowa then Yaa Shaheed ya shigo a bayanta yana ɗauke da manyan ledoji a hannunsa,da sauri na miƙe na nufeta na fara miƙa mata Baby'n,tana karɓarta na matsa na ƙwaƙwumeta kamar zan koma cikin jikinta,da kallo ya bimu musamman ni,yanda na shige jikin mahaifiyata ina sakin murmushin jin daɗi,na ɗaga idanuna ina kallonsa nace "sannu da zuwa!" Ya amsa yace "sannun ki!" Kaina ajikin shoulder mahaifiyata nace "sannu da zuwa Aunty!" Tace "yawwa ƴar albarka" tun bamu zauna ba nace "ina yini?" Tace "lafiya lao,ya kuke?" Nace "muna nan lafiya lao" tace "ashe an samu ƙaruwa?" Nayi murmushi nace "ehh Aunty" tace "maa sha Allah! Allah raya bisa sunnah" nace "Ameen²" ina ta murmushi nayi ƙasa da muryata nace "Aunty ya naga ke kaɗai,ina Hjy Umma baza ta zo ba?" Kallona tayi tace "tazo ta maki me?" Turo baki nayi nace "tou ai na ji ta ce sai sun zo" tana yiwa Baby'n addu'ah tace "ke raba ni da wannan shirmen na ki,tazo tayi me kuma bayan ga ni Abbanku yasa ni zuwa" a hankali na gyaɗa kai,sai ban sake cewa komai ba muka fara hira rabi duk tambayoyi ne make mata,tun yana biye min tana amsa min har ta gaji tayi min shiru,sanda Baby'n ta tashi Aunty ta ɓata dabino data saka a zamzam yayi laushi,da ta ƙoshi ta koma bacci abunta. Ana fara kiran sallar Asr Yaa Shaheed ya tashi yace "Aunty zanje masjeed" Aunty tace "toh! A dawo lafiya" ya amsa ya fita,na tashi nima na wuce toilet na ɗauro alwala na fito,ƙaton dadduma family size da ya kawo mana na shimfiɗa na kabbarta sallah,sanda na idar Aunty ma tayi sallah,lokacin ƴan gidan su Yaa Shaheed suka zo,ƙannensa maza biyu da mata,Yaa Ameer da Yaa Safwan,sai Ihsan da Nafisa autarsu,su suka kawo mana abinci,muna zaune muna ta hira har gurin ishaa sannan suka ce za su tafi,suka yiwa Aunty sallama tana musu addu'ar komawa gida lafiya,muka fita rakasu tare da Yaa Shaheed Ihsan tana kallona tace "kin ƙi zuwa gidanmu kou? Sai dai ki biyo Aunty Fatima,amma baki taɓa zuwa ke kaɗai ba" ƴar dariya nayi cike da kunya nace "eyyahh! Kiyi haƙuri kin ga ai bazai yiwu na bar Aunty ita kaɗai ba,amma tunda ta haihu yanzu zan tambaye ta na zo idan an kwana biyu" murmushi tayi tace "Allah sa da gaske za ki zo ɗin" nace "in sha Allah,zan zo sai dai ki ganni" a haka muka ƙarasa inda sukayi parking suka shiga muna ɗagawa juna hannu,sai da suka tafi sannan muka dawo ward ɗin,ni ce a forefront yana biye da ni a baya,sanda muke shigowa Aunty ta ɗago tana kallona tace "Fadwa ina Shaheed ɗin?" Nace "gashi nan tare muke" lokacin yana shigowa ta kallesa fuskarta da damuwa tace "yawwa Shaheed ka kira Dr ta farka" bai fasa shigowa ba yace "toh! Aunty" kukan da Aunty Fatima ke yi da riƙe cikinta tana wani irin tumbling yasa shi ƙarasawa da sauri yana kllonta yace "what happened?" Aunty tace "ta ce cikin ke mata  ciwo" sannu yayi mata yace "Fadwa ina waya na?" Wucewa nayi na ɗauko na kai masa da sauri,ya karɓa ya kira number Dr Abraham ya sanar masa,na matsa kusa da ita ina mata sannu kamar zan kece da kuka,ba'a jima ba Dr Abraham ya shigo,yanda yaga tana yi da sauri ya kira nurses biyu yace mu fita,hankalinmu duk ya tashi da yanda muka ga ta fita hayyacinta cikin ƙanƙanin lokaci,hankalin Aunty a tashe ta kira Abbanmu ta sanar masa halin da ake ciki,can nurse ta fito ta wuce,bayan wani lokaci ta dawo ta sake shiga,muna ta zaune sai can Dr Abraham ya fito,Aunty tana kallonsa tace "Dr ya jikin na ta?" Yana sauke ajiyar zuciya yace "alhamdulillah! Ta samu bacci,but ɗinkin da akayi ya buɗe,mun dai gyara yanzu,amma dan Allah a kula sosai,idan ya sake buɗewa za'a samu matsala" hawaye cike idonta tace "ɗinki?" Dr Abraham ya gyaɗa kai yace "ehh! Dole sai da aka ƙarata ta iya haihuwa" Aunty ta lumshe ido tace "subhanallah!" Dr Abraham ya gama duk bayanin da zai yi,ya mana sallama ya tafi,jikin Aunty a sanyaye tace "ƙari.. Tun daga haihuwar farko?" A hankali na matsa jikinta nace "Aunty mene ne?" Ta girgiza min kai tace "kije Shaheed ya mayar dake gida da safe sai ki dawo" na amsa jikina a sanyaye nayi mata sallama,Yaa Shaheed ma yayi mata sallama bayan mun sake duba jikin nata muka tafi,a hanya babu wanda ya yiwa wani magana tsakaninmu,sanda muka shiga unguwar Sharaɗa ya kai ni har ƙofar gida,na sauka a hankali na masa godiya na rufe motar,na juya na shiga cikin gida then ya ja motar ya tafi. Ɗan madaidaicin gida ne mai ɗauke da  get,sai compound ba wani babba ba,ɗakin Hjy Umma na fara shiga da sallama,na tarar da su zaune a parlour suna hira,sanda na sake maimaita sallama sannan suka juyo suka kalle ni,a yatsine suka amsa min,na durƙusa ina gaishe da Hjy Umma nace "ina yini?" A daƙile ta amsa da "lafiya" daga nan suka ci gaba da hirarsu babu wanda ya sake bi ta kaina,na gaji na tashi na fita na tafi ɗakinmu,na buɗe na shiga parlour ina kallon ko ina,almost 8 month rabona da gida,a hankali na ƙarasa shiga na wuce bedroom na cire hijab da kayana,hijab ɗina na sake ɗauka na mayar na fita,sanda na watsa ruwa kafin na saka sleeveless da wando na kulle ƙofa na kwanta,not too long bacci ya ɗauke ni. Da asubah sanda na tashi nayi sallah na sake komawa na kwanta,around 7:00am Aunty suka shigo gidan,direct ta shigo ɗakinmu,ban san me yake faruwa ba a gidan,ina kwance ina bacci naji ana tashi na,da sauri na buɗe ido ganin Aunty yasa na miƙe na zauna,ina murza ido nace "sannu da zuwa" ta amsa min a sanyaye na gaisheta,a hankali ina binta da wani kallo nace "Aunty lafiya?" Jikinta a sanyaye tace "mun dawo gida" buɗa idanuwa nayi nace "ya mai jiki? Ina Aunty Fatima ya jikinta?" Hawaye ne suka zubo idon Aunty ta kai hannu ta share,a tsorace jikina yana kyarma nace "Aunty me ya faru? Wani abu ya sameta?" Girgiza kai Aunty tayi a raunane tace "Allah yai mata cikawa.."

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

IN-LAWSWhere stories live. Discover now