👑
👑👑
👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
SARAUNIYA BILƘIS(jarumar mata)
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑
👑
NA
BILKISU ALIYU KANKIA
QUEEN BK.🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))
GABATARWA
Na fara da sunan Allah magamin kyauta a duniya makeɓin kyauta a lahira, dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, ubangijin talikai, magami, makeɓi, mai iko ranar sakayya, wanda yake shi muke bauta mawa kuma gare shi muke neman taimako, tsira da aminci su dawwama ga shugaban annabawa anabi Muhammadu bawan Allah, manzon Allah, tsira da aminci su tabbata ga alayansa da sahabbansa da dukkan annabawa da manzanni, aminci ya dauwama ga duk wanda ya bi tafarki madaidaici.
Bayan haka ina farin ciki in gabatar da wannan littafin nawa ga dukan makaranta, wannan littafin ƙagaggen labari ne wanda na ɗauko shi daga zamanin jahilci bawai dan ya faru ba sai dai kawai dan in nishaɗantar, faɗakar, ilimantar da kuma tunasarwa dai dai gwargwadon ilimin da Allah ya bani, sannan ina so in ja hankalin mai karatu cewa ta sigar da musulunci zai shigo a cikin labarinnan bawai haka yake a zahiri ba kamar yadda na faɗa a farko labarin ya ta'allaƙa ne akan hasashe, tunani da ƙirƙira ta, dan bana son sai mun fara in riƙa jin ƴan gustiri tsomi duk wanda labarin bai masa ba there are many more other options pls, kamar yadda kowanne ɗan adam yake tauyayye ba cikakke ba zai iya yin dai dai haka kuma zai iya yin kuskure, Allah shi kaɗai shi ne ya keɓanta da siffar cika, don haka labari ma zai iya zama ya yi dai dai da ra'ayin mai karatu kuma zai iya zama akasin haka, inhar an samu ɗaya daga cikin haka to ba laifin marubuciya bane, dan dama abincin wani gubar wani ne dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ni dai kawai abunda bana so baƙaƙen maganganu by Allah i can't bear them, fatana shine ya zamanto waɗanda suka samu damar karanta wannan littafin su ƙaru da sannin wani abu ko da ƙalilanne, ya kuma yaye duhun jahilcin haɗa Allah da wani a wurin bauta.
Wannan littafin na rubuta shi cikin lafazi da ganewa irin nawa ba tare da ƙoƙarin gamsar da son zuciyar wani ko wasu mutane ba, yadda na sa shi haka na gane haka nan kuwa nake son mutane su gane, abin da nake fata dai shine wannan littafin ya zamana karɓaɓɓe ga Allah, karɓaɓɓe ga makaranta, karɓuwar da zata ƙara ƙarfafa mun gwiwa in cigaba da rubutu, kuma zan yi farin ciki da karɓar shawarwari, gyara da nasihohi daga gare ku makaranta.FAƊAKARWA
Ƙirƙira tun ma ba ta labari irin na zube ba, aba ce wacce ta ke ƙulluwa da zururruka masu kishiyar juna ta fuskar halaye da ɗabi'u waɗanda sukan sha bam bam daga wannan mutum zuwa ga wancan mutum, daga wannan gida zuwa ga wancan gida, daga wannan gari zuwa ga wancan gari, daga wannan ƙabila zuwa ga wancan ƙabila, daga wannan al'umma zuwa ga wancam al'umma.
Don haka wanda wani hali a cikin wannan labarin ya yi kamanceceniya da nasa/nata, to arashi ne aka samu, kamar yadda na cikin labarin ba zai ce wani mutum da yake a wajen labarin ya ɗaukar masa hali ba to shima wanda yake waje kada yace an aikata halinsa, idan an samu kamanceceniya arashi ne aka samu.
YOU ARE READING
SARAUNIYA BILƘIS
Random#35 Soyayyah 14 June 2020. "Ya kai mai martaba sarkin Saffron, anyi kusan kwana biyu kenan ana wannan guguwar a garinnan amman daga haihuwar sarauniya guguwar ta tsaya cak rana ta fito komai ya koma yadda yake, wannan alamu ne na nasara a rayuwar s...