chapter 2

535 35 6
                                    

👑
👑👑
👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑

👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
SARAUNIYA BILƘIS

(jarumar mata)
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑
👑









NA

BILKISU ALIYU KANKIA
QUEEN BK.




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))







SADAUKARWA

Farida B. Muhammad 😘yakumbota.




Book👆
Page0⃣2⃣











BAYAN SHEKARA 18





A hankali na shiga mitsitsike idanuna cikin ƙoƙarin fitar da sauran baccin dake kaina, badan komai ba sai dan yau ta kasance rana ta farin ciki a gareni kasancewar yau za a sauko mahaifina daga kurkukun garin Zareen wanda aka saka shi shekaru sha takwas da suka wuce wanda yayi dai dai da ranar haihuwata, sanin kaina ne babana adalin sarki ne kuma ya ɗora ma kanshi laifin da ba na shi bane har yai sanadin zaman ƙarangiya, duk da har yau bansan laifin da ya ɗaukan ma kansan ba, ni dai kawai abunda na sani ina matuƙar san mahaifi na duk da ban taɓa sa shi a idanuna ba amman muna yawan magana dashi ta wasiƙu, kakata Mairi wadda nake ce ma Anna jarumar mace ce me jida sarauta tana matuƙar sona fiye da zaton mai katatu, ita ce wadda ke riƙe da karagar mulkin Saffron tsawan shekaru sha takwas da suka shuɗe, na taso cikin gata da sarauta kasancewar nice sarauniya mai jiran gado, miƙa nayi duk cikin ƙoƙarin kora bacci daga jikina dan ban saba tashi da wuri ba, da sauri na buɗa idona tuna yau ne ranar murnar zagayowar shekarar Anna, kai amman farin cikin wannan ranar yana nema yamin yawa.





Na zuro ƙafafuna daga kan lausassan gadona, kamar ko da yaushe muryar Naiyana ce ta daki dodon kunnuwana a inda take faɗin "Barkanki da tashi sarauniya ƴar sarakai, kyakyawar da ba na biyunki, barkanki dai sarauniya mai jiran gado, ciki sannu a lafiya bango madafar bayi, lafiya kwankwasan jimina mai wuyar shafawa.....".


Gyaran murya nayi wanda hakan ya sanar da Naiyana cewa kirarin ya isheni haka, Naiyana amintacciyar hadima tace duk cikin hadimai na banda na biyunta zan iya cewa kusan tare muka taso dan duka duka shekaru uku ne ta bani tare mukai wasan yarinta da ita hakan yasa nake jinta kamar wata ƴar uwata duk wani sirri nawa ita nake fara sanar mawa haka ma a ɓangarenta sai dai abu ɗaya ne bai taɓa daidaituwa a tsakanin mu ba wato matsayinmu, Naiyana ita ɗaya ce ɗiya a wajen babanta wanda yake shine mai tsaron fada, ita baiwa ce ni kuma sarauniya, amman duk da kasancewata sarauniya hakan bai sa ina wulaƙanta na ƙasa da ni ko zaluntarsu ba ina matuƙar ƙaunarsu kuma bana ƙyamarsu, ba kamar dai yadda za kuga wasu masu sarauta a hannu suna wulaƙanta na ƙasa da su ba.


Kamar kullum hadimai nane suka shiga shiryani bayan na dawo daga gurin da nake motsa jiki wanda ya zame mani wani ɓangare na jikina domin a duk safiyar rana sai na motsa jikina nake jin daɗi yanzu ne ma dana sa wasa dan sati biyun da suka wuce Naiyana ta fara koya mun faɗa da wuƙa, bayan sun gama kimtsani wasu suka bini a baya yayin da wasu suka shiga gyaran turakartawa, muna fitowa nan bayi da hadimai suka shiga zubewa suna gaishe ne da murmushi kawai nake binsu duk da ban iya wulaƙanci ba amman ina ji da sarauta domin jinin sarauta ne ke yawo a jikina, dan tunda aka kafa garin Saffron tsatson mune suke mulkinshi har kawo wa yanzu, turakar Anna na wuce zuciyata fari ƙal, ina isa na isketa cikin shirin shiga fada, faɗawa nayi jikinta ina gayyar da ita kamin nace "Annah gimbiya uwar sarakuna ina taya ki murnar zagayowar shekarunki" hanci na taɗan ja kamin tace "ina godiya sarauniyata".


SARAUNIYA BILƘISWhere stories live. Discover now