👑
👑👑
👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
SARAUNIYA BILƘIS(jarumar mata)
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑
👑
NA
BILKISU ALIYU KANKIA
QUEEN BK.
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))
SADAUKARWA
Farida B. Muhammad 😘yakumbota.
Kada ka sake ka bama shukan wani ruwa da niyyar idan ta fito za'a baka amfanin gona, idan kayi haka to lallai ka zamto sakarai marar tunani, idan kayi domin Allah kai zaka fi mai gonar samun riba.
Book👆
Page0⃣3⃣
Dogan nazari tayi kamin ta ɗago ta kalli mahaifiyarta tare da furta "amman Mama taya kike ganin sarki Shizun zai yadda da abunda su yaya Zaydeen za su gaya masa akan sarkin Saffron?".Sai da ta ƙara kurɓar shayin hannunta kamin tayi ƴar taƙaitacciyar dariya haɗe da goge bakinta da ɗan tsabtacaccen ƙyallan goge baki sannan tace "kar ki damu yayanki Haruno shi zai kula da wannan ɓangaren" sarauniya Reenah tayi dariya cike da jin daɗi da mugunta.
******************************
ULMAN
Sodojin garin Ulman ne suka taru kansu da ƙwarƙwatarsu a wani babban fili dake can bayan gari, sai dai abin mamaki sanye suke da kaya irin na sodojin garin Zareen ko me yasa?, da ka gansu kaga masu shirin shiga filin daga wato yaƙi domin sanye suke da rigunan ƙarafe a saman rigar dake jikinsu sai kawunansu dake ɗauke da huluna suma na ƙarfe wanda cikinsu katifa ce mai laushi akasa yadda ko an bigi kan mutum bazai ji rauni ba sai ta kasance kariya a garesa, duk wani wuri mai rauni a jikinsu sun tare sa da abun kariya sai wuƙaƙensu dasu ka sha fiƙa dake rataye a ɓangaren su na haggu, jere suke a layi sun ƙame basu ko motsawa aƙalla ba aka sara ba za sukai su ɗari biyar wajen yayi tsit ba kajin kukan komai sai iskar dake kaɗawa a hankali a cikin dajin har zuwa lakacin da wani cikakken ingarmar mutum ya fito daga ƴar bukkar dake bayan sodojin hannunshi riƙe da safar hannu wadda ta tafi kala ɗaya da duka tufafin dake jikinsa kasancewarta baƙa, nan ya shiga zurata a ƴan yatsunsa, kallo ɗaya zaka mashi kasan ba ƙaramin gawurtaccen jarumin namiji aka aje a wurin ba, bayan fitowarsa wasu bayi maza biyu suma suka fito daga bukkar hannunsu riƙe da sauran karikitansa da alamu hadimansa ne, gyaran murya yayi fuskar shi a murtuke babu ko alamun dariya irin dai mutanen nan ne da sam dariya bata masu kyau, koda jin gyaran muryarsa da sauri sodojin suka juyo a tare suna fuskantarsa take kuma suka haɗe baki wajen faɗin "Barka da fitowa yarima Zaydeen".
YOU ARE READING
SARAUNIYA BILƘIS
Random#35 Soyayyah 14 June 2020. "Ya kai mai martaba sarkin Saffron, anyi kusan kwana biyu kenan ana wannan guguwar a garinnan amman daga haihuwar sarauniya guguwar ta tsaya cak rana ta fito komai ya koma yadda yake, wannan alamu ne na nasara a rayuwar s...