01

3K 94 4
                                    

💧💧 *RUGUNTSUMI..!*

                     

 
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*

*MALLAKAR :- FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  *GAISUWARKU DABAN TAKE, UMMI AISHA, PHARTY ZARAH, MOMMA (XOXO), AUNTY HAJJA CE DA DUKKAN YAN K'UNGIYAR HASKE.*

  *KARAMCINKI DABAN NE SISTER FATIMA MAROK'I*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.*
  _Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talakai, Wanda ya bani damar fara rubuta wannan littafin, kura kuran da zamu rubuta Ubangiji ya yafe mana...._
  _Ban rubuta wannan littafin domin cin zafari ko take hak'k'in wani ba, kamar yadda kuka Sani ko wane Dan Adam yana da hakkin zab'awa kanshi rayuwa da Addinin da yake so, babu ruwana da kowa duk abunda yayi dai dai ta rayuwarka ko ta wani na kusa da kai ka dauka hakan na faruwa a ko'ina_

   *01*


      ****Tunda na dawo daga d'ebo ruwan safe nake k'wance gindin bishiyar dirimin dake tsakar gidanmu, ni ce ban farka ba sae da zafin rawa ya fara gasa mani fatar jiki.

  Yayin da na kaiwa cinyata duka na kori k'udajen dake yayyab'e da ni sannan naja bujena na take shi da k'afata tare da k'ara mayar da idona na kulle..

  Muryar Asabe da naji tana fad'in "Innarmu ga k'uli k'ulin na sawo." Ta saka na zabura na mik'e ina kallonsu, na saki hamma tare da gantsaro k'irji sannan na mik'e na juya masu baya yayin da na d'age d'an bujena wanda iyakarsa guiwa tare da ware k'afafuna na d'an duk'a kad'an na saki fitsari, sannan na saki bujen na juyo na sake zama bisa gefen  dirimin ina kallon saitin su ina lashe baki kamar tsohuwar mayya..

Ci wake ya kai mani mazga ta k'eya yana dariyar mugunta, ya bud'e wagegiyar muryarshi yace "Ke dai shegiya aka d'ima anan Rahila, Don bala'i ji yadda kike lashe baki kamar tsohuwar mayya.."

    Ko kallonsa  banyi ba har ya wuce ta gabana domin azababbiyar yunwar dake cikina kad'ae ta isa a kirata da bala'i, Har wani hantsinawa cikina yake yayin da juwa ke niyyar kaini k'asa. Har ga Allah rabon da na sawa baki na abincin tun tuwon jiya da daddare...

  Na kai dubana ga Asabe dake zaune kusa da mamanta, tana k'wasar dambun dawar da yaji k'uli k'uli da man gyad'a hankalinta kwance, a hankali na rik'e gefen cikina Ina lashe baki wata zuciyata na kitsa mani ina ma nice haba da kwanon zan d'aga in juyeshi a bakina, na lashe busassun lab'b'ana ina kallon k'wanon.
   Duk ilahirin mutane dake cikin gidan babu wanda ya damu da ci na bare shana, kowa ya samu daga shi sai ya'yan'sa yayin da ni kuma ko oho..
  Gefe guda kuma Rabeka ce zaune da yaranta suna cin sabuwar dabuwa da taji albasa wadda suka dafa da safe sae k'amshin daddawa ke tashi. wadda idan anso adalci tare dani za'aci ta saboda ni na samo tuwon da aka shanya shekaran jiya, hararar da ta balla mani ce ta sa ni d'auke idanuna daga kanta yayin da na had'iye tsinkakken miyan da ya taru a bakina..

  A hankali na rarrafa kusa da Maman Asabe domin ta fi Rabeka mutunci, Murya k'asa k'asa nace "Mama Asabe ki taimaka sammani mana ko loma d'aya ce, kinga ko tuwon safe ban samu ba, Innarsu Ci wake ta kwashe shi."

   Tayi banza dani kamar bata san dani a gurin ba yayin dana k'ara langwab'e murya ina fad'in " Maman Asabe anjima zan d'ebo maki ruwa, kuma zan maki tallar gyad'a da daddare kuma bazan b'atar maki da kud'i ba, sannan kuma gobe ma idan zakiyi girki zan lallab'a na d'ebo maki karan ci wake babu wanda zan bari ya ganni." Na k'arashe maganar idona na kan lomar dambun da Asabe ta d'ebo, yayin da nake ji kamar na fad'a a cikin k'wanon

   Ta watso mani harara sannan ta d'ebo ci kin hannunta d'aya ta dangwale mani a hannu, ban damu ba na lashe jikina har k'yarma yake, sae da na lashe hannuna sannan na tuna da wahalar da na janyowa kaina akan loma d'aya ta dambu.

RUGUNTSUMIWhere stories live. Discover now