💧💧 *RUGUNTSUMI..!🎄*
💥
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*💡
*MALLAKAR :- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm*SADAUKARWA GAREKU..*
*SAFIYYA HUGUMA TARE DA KHALEESAT HAYDAR**KARAMCINKI DABAN YAKE SISTER FATIMA MAROK'I💞*
*GAISUWARKI DABAN TAKE MOMMA (XOXO)*❤️
*07*
Iya rud'ewa Babana ya rud'e ganin za'a sace mashi yarinyar shi wadda yake wa kallon jari babba, yayin da ya d'auki alhakin saceta ya d'aura akan ilahirin mutanen garin, ya danganta shi da mugun bak'in ciki da hassada da suke mashi don yana da yarinyar da babu kamar ta duk garin...
Gungun mutanen da suka kawo mani d'auki ya kalla, wani haushinsa ya turnik'esu ya saki tsaki yana fad'in "Munafukan banza da wofi."
Sannan ya ja hannuna ya nufi gidan pastor da dani, a bakin k'ofa muka tsaya aka mashi iso, sannan muka shiga cikin gidan kai a k'asa.
Sae da muka cire takalma a bak'in k'ofa sannan suka shiga cikin d'akin da yake zaune wanda ke cike da littattafai barkatai kamar su Al Qur'ani, Hadissai, Da duk wasu littafan addini da muke dash, yayin da babana ya zub'e saman guiwar sa had'e da sadda kai k'asa...
Hannuna ya janyo ganin nak'i tsugunnawa, na kuwa turo bak'i tare da zama k'asan carpet na mik'e k'afafuna ina kallon shi.
Littafin Holy Bible dake hannunshi shi ya aje a gefe, yana satar kallona, sannan ya kalli babana a hankali yace "What has brought you here.?
Yayi k'asa da kai cikin girmamawa yace " I required your assistant.."
Tab'oshi nayi da hannu ina fad'in "Aiyoo Ashe kaima ka iya wannan iskancin maganar Baba.?
Ya dallah mani harara.
Jin abunda nace ne ya saka Pastor d'in kallona sannan yace " Me kake buk'ata..?
Cike da ladabi yace "Akwae yan bak'in ciki da suke lullube da d'jyata, har ta kai ga suna son sace ta, please I need your help, ka taimake ni ka mata addu'a ita kad'ai ce dani."
"Ji k'arya, Su Asaben fa.? Na tambaya ido a bud'e.
Dallah mani harara yayi sannan yace " Rufe mani baki! Su wad'annan mutane ne? Ko wace da fuska kamar takashin rak'umi.?
Kallona Pastor yayi, yayin da ya runtse ido yana surutai, tsawon minti biyar sannan ya bud'e idonsa yana fad'in "Akwae bala'i da masifa dake bibiyar d'iyar."
"Yesu...! Ya fad'a a razane tare da hangame baki yana kallona
Yar dariya Pastor yayi ya nuna shi da hannu yana fad'in "Wait Outside.."
Ya mik'e jikinsa har k'yarma yake fita, yayin da na biyoshi da sauri har ina tuntube, sae dae kafin na kai k'ofa har ya fita ya ja mana kofar, juyowa nayi ina kallon Pastor a tsorace ganin d'akin ya fara duhu kuma yayo gurina..
A hankali nace "Nima zan bi Babana, ba zama zanyi ba."
D'an murmushi ya sakar mani yana fad'in "Calm down, addu'a kawae zan maki ki tafi daughter, akwae bala'in dake dabaibaye dake"
Da sauri nace "Wa ya fad'a maka.?
Kai tsaye yace " Yesu.."
Hannuna ya rik'o ya zaunar dani k'asa sannan shima ya zauna muna kallon juna, a hankali yace "Close your eyes.."
Na tab'e baki ina kallonshi, har sae da ya k'ara fad'in "Rufe idonki." Sannan Na rufe yayin da ya cigaba da fad'in " _We confess our need for you today. We need your healing and your grace. We need hope restored. We need to be reminded that you work on behalf of those you love, constantly, powerfully, completely. Forgive us for trying to fix our situations all on our own. Forgive us for running all different directions and spinning our wheels to find help, when true help and healing must be found first in You. Forgive us for forgetting how much we need you, above everyone and everything else. We come to you and bring you the places we are hurting. You see where no one else is able to fully see or understand. You know the pain we've carried. The burdens. The cares. You know where we need to be set free. We ask for your healing and grace to cover every broken place. Every wound. Every heartache. Thank you that you are Able to do far more than we could ever imagine. Thank you for your Mighty Power that acts on behalf of your children. We reach out to you, and know that you are restoring and redeeming every place of difficulty, every battle, for your greater glory. Thank you that you will never waste our pain and suffering. We love you. We need you today_.