💧💧 *RUGUNTSUMI..!🎄*
💥
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*💡*MALLAKAR :- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm*SADAUKARWA GAREKU..*
*SAFIYYA HUGUMA TARE DA KHALEESAT HAYDAR**KARAMCINKI DABAN YAKE SISTER FATIMA MAROK'I💞*
*GAISUWARKI BADAN TAKE MOMMA (XOXO) DAKE DA DAUKACIN MEMBERS D'INKI❤️*
*05*
*DA GA BANA SAI BADI...*
Wata al'adace da mukeyi duk shekara waccen mazan da suka rasa masoya da mata suke fitowa zindir haihuwar uwarsa su jera layi suna kallon juna, sae a basu umarni su rugu su had'e, to a wannan had'uwar da zasuyi duk namijin da yayi sa'ar yiwa wadda ya kama ciki to idan ta haihu zasuyi aure, idan kuma bata samu ciki ba sae a tari shekara mai zuwa har sai lokacin da ta samu ciki...
Saboda haka tunda daddare aketa shirye shirye da kid'e kid'e, shiyasa ba kowa ke samun damar bacci ba, wanda nima hakan ce ta faru dani, ina kwance bakin kofar d'akin mama Asabe na tattake bujena saboda kar sauro ya cije ni, na jiyo muryarta suna fira da Asabe sama sama..
Tashi nayi na rarrafa kusa da tulu na k'wank'wad'in ruwa sannan na matsa na d'aga labile ina fad'in "Maman Asabe in shigo.?
Tace " Wani abu zaki d'auka.?
Na girgiza kai kamar tana kallona yayin da nayi k'asa da murya nace "A'a maganar Barnabas zan maki."
Ina jin tacewa Asabe "K'wanta kiyi bacci bari in dawo."
Sannan ta fito taja Hannu na muka matsa bakin dirimi yayin da tayi k'asa da murya tana fad'in "Yi maza ki fad'a Mani? Me yace maki? Ko cewa yayi kije ki tayasa k'wana.?
Na girgiza kai nace " A'a shi da ma ba so yake yana tab'awa ba."
Murmushi tayi ta janyoni bisa cinyar ta zaunar dani yayin da ta k'wantar da kaina saman kafad'arta tana shafa bayana tace "Banda abunki Rahilata idan baya so bake zaki k'wad'aita mashi ba? Ki bari gobe kafin mu tafi shagali zan gwad'a maki yadda a ke fari da idanu da kisisina irin ta mata.."
Dad'i ya kashe ni yau nice zaune a cinya kuma har da k'wantar dani bisa kafad'a abunda tunda nake duniya ba'a tab'a mani ba, na kai hannu na sosa k'asa na dake k'yaik'yayi sannan nace "To Maman Asabe."
Tace "Yauwa d'iyata me kike so ki fad'a mani.?
K'asa nayi da murya sannan nace " Kinsan Jocep.?
Ta shafa gadon bayana tana fad'in "Ni kam nasan Jocep, shima sonki yake Rahilata? To ai dama kamar ki k'yak'yk'yawata ya kamata ace kina da samari fiye da goma, idan kunyi da wannan da safe, da hantsi kiyi da wani, haka da rana da kuma marece da daddare, kinga kenan bazaki yi zaman banza ba kuma kud'i ko ta ina ( _kamar wata akuya_ ) .."
Washe baki nayi yayin dana lissafa iyayen kud'in da zan samu a rana sannan nace "To kuma shi ce wa yayi yana son Asabe, kuma takassanta zai tab'a.."
Wani uban dundu ta sakar mani a gadon bayan, yayin da ruwan da nasha ya biyo ta hanci ya fito, sannan ta ture ni ta kuma bini da dank'washi ta murd'e mani kunne tana fad'in "Idan na kuma jin sunan Asabe a bakinki sae na cicci ubanki, shegiyar yarinya tsinanna, mai shegen hali.."
Ta take mani k'afa da takalminta na danko ta wuce abunta, kuka na saki jin bayana ya rik'e ga uban zugin da kirjina ke mani, daga d'aki babana yajiyo sautin kukana, ya fito da Sauri yana haska tocila