💧💧 *RUGUNTSUMI..!🎄*
💥
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*💡*MALLAKAR :- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm*SADAUKARWA GAREKU..*
*SAFIYYA HUGUMA TARE DA KHALEESAT HAYDAR**KARAMCINKI DABAN YAKE SISTER FATIMA MAROK'I💞*
*GAISUWARKI DABAN TAKE MOMMA (XOXO)*❤️
*10*
Last Free Page...** Tun daga wannan ranar Asabe ta samu hanyar samun kud'in kashewa, Yayin da na zame mata y'ar rakiya dan nakan jirasu bakin gona har sae sun gama iskancinsu, Idan kuma na ga wani ya tunkaro gurin da suke sai in k'wala mata kira, to da taji na kirata tasan abunda nake nufi, Idan suka gama kuma ta ciri wazobia ta mik'o mani yayin da shima Joceb d'in zai bani rabin jikka (100) in had'a abuna in mak'ale a buje, don haka na bud'e sabon asusu a bakin dirimi inda nake zuba kud'in a leda sannan inyi rami mai zurfi in saka abina..
Idan kuma muka koma gida tayi kamar bata sanni ba, a cewar ta idan Innarsu taga muna mutunci rana tsaka zata zargi wani abu, ita kuma bata so Innarsu ta sani wata k'yil kuma don bata so ta dinga k'arb'e mata kud'ine don haka muke banza da juna a cikin gida..
Lokaci guda ta fara murjena, tayi k'yau abunta don ina jin wata rana Rabeka na tambayar Maman Asabe sirrin wannan k'yau da Asabe keyi sae dae tayi dariya tana hura hanci tace "Dama can Asabe k'yak'yk'yawa ce don kawae kuna ganin waccen jajakuwar d'iyarce shi yasa baku gannin k'yanta." Tayi maganar tana cinno ni da baki.
Ni kam dae nasan sirrin domin nama Joceb ke kawo mata ga kuma cima iri iri da yake taho mata da ita idan ya shiga birni shiyasa tayi bul bul abunta gwanin ban sha'awa..
Muna zaune ta mik'o mani tsokar nama guda biyu tana hararata k'asa k'asa ba abun tace bata bani ba in ce zan fad'awa Innarsu, na k'arb'a ina jujjuyawa tare da mayar mata da abunta cikin leda na mik'e tsaye ina kakkab'e bujena.
Ta kalleni ta dalla mani harara "Amshi na k'ara maki biyu.."
Na buga buje ina wak'ar "Yesu almashiwu madogarana, mai cetona almashiwu..."
Mik'ewa tsaye tayi tana tambaya ta "To ina zaki.?
Kai tsaye nace "Innarku zan fad'a mawa abunda kuke da Joceb."
Ta mik'o mani ledar tana fad'in "Amshi gaba d'aya mayya.."
Banji komai ba na k'arba ina washe baki to menene don race mani mayya? Tunda ni nasan ba mayya bace don haka na mik'e k'afa ta na cigaba da k'wasar abuna hannu baka hannu k'warya, sae da na cinye naman tas sannan na d'ago ina kallonta wanda har lokacin tana tsaye tana kallona tana harara ta sama da k'asa..
Na saki tsaki ina fad'in "A banza yarinya."
Ta dallah mani harara "To kema ai sae ki ce Barnabas ya sayar maki ba."
Na k'watsa mata tsawa ina harararar ta cike da tsiwa nave "Ai ni ba y'ar bak'in ciki bace kamarki yarinya da zance komi akawa y'ar uwata sae an mani."
Tsaki ta ja ta kada kai tayi tafiyarta ta barni tsaye a gurin, yayin da nima naja nawa dogon tsakin na kama hanyata daban..
Ta kusa da gidan mai gari na bi na iske babana zaune Cikin zauren gidan su biyu kadai, na gifta zan wucesu ya k'wala Mani k'ira " Yaki zilleliyata."
Na turo baki ina fad'in "Shi wannan baban dole sae ya bawa mutun kunya yayi ta kiran mutun gaban baban saurayin sa.."
Na matsa bakin k'ofar zauren ina ta faman turo baki a hankali nace "Sannun ku.."