💧💧 *RUGUNTSUMI..!🎄*
💥
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*💡*MALLAKAR :- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm*SADAUKARWA GAREKU..*
*SAFIYYA HUGUMA TARE DA KHALEESAT HAYDAR**KARAMCINKI DABAN YAKE SISTER FATIMA MAROK'I💞*
*GAISUWARKI DABAN TAKE MOMMA (XOXO)*❤️
*09*
*****Ya kalleta sama da k'asa yana dariyar mugunta tare da lashe baki kamar wani tsohon maye sannan ya bud'e wagegen bakinsa mai cike da jajjayen hak'ora yace "To nawa ni kuma zan bada Asabeta.?
Kafin in yi magana ni da na had'a naji tayi karaf tace " Rabin jikka (100)."
Na kai mata duka cike da takaicinta ina hararanta sama da k'asa sannan nace "Ke Asaben nan dalb'eb'iya ce
! ai ba haka ake ba, tab'i uku ake yi a wazobia."Ta watsa mani harara tana fad'in "To ke ina ruwanki..?
Kallona Joceb yayi yana fad'in "Zan bata haka, je ki jiramu bakin gona idan mutane sun taho sai ki k'wala mata kira."
"A nawa.? Na tambaya don ni yanzu bana aikin banza..
Kai tsaye yace " Wazobia.."
Wani dad'i ya kamani samun wazobia a banza haka?Lallai babu Sana'a mai riba irin ta..
Ga kuma wadda zata dinga bani kullun in sukayi? Idan na had'a ta tashi rabin jikka kenan fa? Na washe fararan hak'ora na nufi bakin gonar da gudu na zauna ina wasa da duwatsu....
Ban dad'e da zama ba na jiyo ihun Asabe daga bayan iccen baure, na gyara zamana ina fad'in "Wata k'ila matsa mata yayi da k'arfi shi yasa take ihu, kai Asabe banza ce daga tab'a takassai sae wannan ihun.? Na saki tsaki ina wulla duwatsu sama.
Lokaci guda na saki yar dariya mai sauti ina fad'in "Idan ya bani wazobia ita ma ta bani tata wazobiar sae in dinga had'awa ina kaima Innarta, kud'ina kuma in dinga kashe abina ina tarawa, idan Kirismeti tazo sae dae kawae su ganni da sabon buje.."
Na buga k'afa k'asa ina dariya....
Har na fara gajiya da zaman jiranta, amma Asabe bata fito ba, don haka na mik'e da niyyar zuwa dubota, zaune na isketa bakin iccen tana matsar k'wallah yayin da jini duk ya b'ata mata buje, na zare idanu cike da tsoro ina kallon Joceb..
"Me ka mata Joceb..? Na tambaya lokacin da na kai hannu na rik'o bujen ina kallo.
Kallona yayi a raunane yana fad'in " Ba abunda na mata.."Nace "Karya kake, kai da aka ce ka tab'a takassai mai ya kai ka ji mata ciwo? Ko dambe kukayi.?
" Wane irin dambe Rahila.? Ya tambaya a sanyaye.
Na k'watsa mashi tsawa kamar d'ana ina fad'in " Idan ba dambe kuka yi ba to me ya kawo jini a bujenta? Na san dae kai ba maye bane innarku kad'ai ce mayya bare ince tand'eta kayi.."
Ya dallah mani harara tare da mik'ewa tsaye yana kallonta "Idan banci ubanki ba anan tsinanne nake, komai ya faru ai laifinku ne, yara da shegen maitar kud'in, ni sani nayi da wannan ne yinta na farko?
" K'wal uba.."
Na fad'a tare da d'age bujena na rik'e gefen rigarshi ina fad'in "Shine kuma zaka mani masifa Joceb? To da inyi kushewa (Mutu) yau sae ka biyata, sae ka maidata yadda na kawo maka ita, lafiya lau babu ko d'igon jini a tare da ita, yo banda kana maye d'an iska, ba cewa nayi kawae ka tab'a ba? Me yasa jini ya fito mata, ai nima Barnabas na tab'a mani kuma jini bai tab'a fita ba, tashi Asabe gurin babansu zamu ki gwad'a masa abunda ya maki, kuma dole sae sun biyaki..."