04

1K 32 1
                                    

💧💧 *RUGUNTSUMI..!🎄*

                      💥

 
©️ *HASKE WRITER'S ASSO*💡

*MALLAKAR :- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm

*SADAUKARWA GAREKU..*
*SAFIYYA HUGUMA TARE DA KHALEESAT HAYDAR*

  *KARAMCINKI DABAN YAKE SISTER FATIMA M0RIK'I💞*

*04*

    ****Wajen k'arfe 5:40 na marece, Abbi yace yaje ya d'aukota tana can tana jiransa, yayin da ya  bashi phone numberta..

    Lokacin da yaje airport d'in bai wani sha wahalar ganeta ba saboda ita kad'ae ce mace a guri, tana sanye da doguwar riga red colour wadda tabi duk ilahirin jikinta ta manne gashi duk ta fiddo mata k'iran jikinta yayin da saka veil ta nad'e kanta iya fuska, sannan ta had'e da uban glass bak'i, ga uban gashin doki kwance a gadon bayanta, tana d'an jiki amma ba sosai ba sannan fara ce tas sae da da alama na kanti ne, da ka kalli fuskarta kad'ai zaka fahimci ba yarinya bace, ta hakimce sae taunar cingum take k'as k'as....

  "Ikon Allah.." Ya fad'a lokacin da yaga wan k'aton k'wae ya fito a bakinta ...

   Sallama ya mata, ta d'ago ta kalleshi ta watsar ta cigaba da taunar cimgum d'inta.

  "Sunana Oppah, Abbi ya turoni in d'aukeki." Ya fad'a yana k'ok'arin danne dariyar dake neman sub'uce mashi, don shi har ga Allah dariya ma take bashi yadda take cin magani tana yatsina kamar ta ga kashi....

   Ta kalleshi sama da k'asa sannan tace "Sae yanzu ka ga dama.?

  " Go slow aka samu.." Ya fad'a kai tsaye ba tare da ya kawo komai ba a ranshi.

  Gaba yayi yana k'ok'arin bud'e mota ya tsinkayi muryarta tana fad'in "Wa zai d'aukar maka jikkan.?

   Cike da mamaki ya juyo yana kallonta kamar zaiyi magana sae kuma ya fasa ya saki murmushin yak'e yace " Ban lura akwae jikka bane." Sannan ya dawo baya ya d'auka ya saka a mota..

  Har suka isa gida babu wanda ya k'ara magana, yayi horn aka bud'e mashi gate, yayin parking ya fita ya barta cikin motar yayin da yayi gurinsu Indi da ya hango suna wasan tsere da Abbi.

    Ita kam mutuwar tsaye tayi a gurin ganin yanayin gidan, don ya bala'in tafiya da imaninta asalima bata d'auka haka zata tarad ba, ajiyar zuciya ta saki ta fito a sanyaye, sae ganin Oppah tayi ya jone da su Abbi suna tseren, kusan daskarewa tayi a gurin...

  Abbi ya baro su ya nufo gurinta yana fad'in "Welcome D'iyata, Ya Hanya.?

  Gabanta ya fad'in a ranta take fad'in Allah dae yasa ba wannan bane Dr Sherrif d'in, Allah ya taimakeni shima d'ansa me

  A fili kuma d'an duk'awa tayi tana fad'in "Yauwa Dad, Hanya kam babu d'adi."

   Yar dariya yayi ya k'walawa indi kira ,yana fad'in "Zo ki shiga da ita ciki ."

  Suka taho tana goye a bayan Oppah, sae da suka zo gurin sannan ta dire tana dariya a hankali tace "Aunty Hauwa'u sannu da zuwa."

  Hankalinta naga Abbi ta amsa da "Yauwa.."

  Jan hannunta Indi tayi tana fad'in "Oppah ka d'auko mata jikkar Dan Allah.."

  Ya gyad'a kai ya sunkushi jikkan suka shige ciki a tare, a falo suka iske Ummi tana yanka fruit, ta tare ta cikin fara'a kamar dama sun saba tana tambayarta ya mamanta..

  Ita kam kamar gunki haka take binsu, domin bazata iya boyewa ba domin har ga Allah zuciyarta ta kamu kuma tana k'wad'ayin wannan gidan...

  Muryar Ummi ta tsinkaya tana fad'in "Indi ki shiga da Ita d'aki ta watsa ruwa sae ku fito ta sha fruit kafin a gama abinci.."

RUGUNTSUMIWhere stories live. Discover now