part 9

1K 45 6
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Assalamu alaikum my fans, ina baku hakuri bisa jina da kukai shiru kwana biyu, hakan ya faru sakamakon wannan annoba data addabi duniya, sai dai fatan Allah ya nuna mana karshen ta, badan rai na yaso ba na dawo da typing sai dan fans da suka takura mun, ga azumi yana sawo kai shi ne dalili, Allah ya bamu ikon kammalawa kafin azumin.*
         


                *40-45*

Minti goma ba tai ba ya dawo da wata nurse nan da nan ya ce da Umma zasu je da ita lab ta jira akwai gwajin da za'ai  mata, bata kawo komai a ranta ba ta amince saboda hankalinta ya gama tashi da aman da ta ke shekawa.

Nurse ta kamata suka je lab gwajin farko ya fito positive, abun da yai masifar daga hankalin Doctor Mahmud besan san da jiri ya dinga diban sa ba ji kake tim ya fadi.

Abun da ya daga hankalin nurses din da suke cikin lab din suka yo kansa, ya daga musu hannu ya mike a hankali ya jingina da bango, numfashi yake fitarwa a hankali me tsananin zafi da zugi a ransa.

A hankali ya kalleta "why Maryam? why? me ya sa ki kai haka? me ya sa ki kai wa rayuwarki karan tsaye? meye ya rude ki a duniya har haka?"

Wani kuka ta fashe da shi me tsuma rai "tabbas Arfan kai shedanine, ka gama dani ka gama da rayuwata bani da wani sauran farin ciki a rayuwata bazan iya ba."

Ta mike da gudu zata fice cikin wani zafin nama wanda besan yana da shi ba ya damkota, duk da radadin da zuciyarsa ta ke masa amma yana tausayawa yarinyar sosai musamman daya fuskanci tarin nadama a fuskarta.

Gaba daya Nurse din abun ya basu mamaki ji suke kamar a tv to me Doctor Mahmud ya ke haka ne? wacece wannan din ita kuma?  ba su da wannan amsar mamaki kawai suke ashe yana magana haka.

Kama hannunta yai suka fita office din sa ya kaita ya ajiye ya kulle kofar ya zauna ya zuba mata runannun idanuwansa wanda yake hukuntata dasu gaba daya ta gama fita hayyacinta.

Dan ya gama kashe mata jikinta kunya take ji mai cike da tarin nadama, kuka take kamar ranta ze fita sai da ya gama hukuntata da idanuwansa sannan ya bude baki da kyar kamar me koyon magana.

"To meye kuma abun kuka? meye na kuka wa kikewa kuka? kin bata wayonki Maryam, da girman ki kika aikata wannan mummunan abun, da wane ido zaki kalli mijinki me zaki ce masa? me zaki kai masa ranar daren ku na farko? kin san girman zunubin da ke cikin zina kuwa?"

Ta kuma rushewa da kuka "wallahi ba lefina bane Arfan ne yai mun fyade! wallahi bansani ba ban taba sanin wani da Namiji ba a duniya sai shi, na tsani zina Doctor da wane ido zan kalli iyayena a yanzu, na dade da gayawa Abba aure nakeso amma yaki yi mun ya ce karatu zan tun san da na fuskanci na fara shiga wani hali."

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now