part 16

964 47 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



                   *75-80*

Awansa biyu cir akan ta sannan ya fadi ragwaf kamar matacce yana nishi, sai sannan ya lura ashe suma tai cikin firgici ya dagota yaraf ta koma cikin tashin hankali ya fice.

Parlour ya nufa yama rasa ina zai sa kansa saboda tsananin tashin hankali, da sauri ya nufi parlour ya bude fridge ruwa ya dakko mai sanyi sosai ya tuttula mata wata ajiyar zuciya ta saki tana kukan azaba.

"Wayyo Allah na na shi ga uku na" idonta a rufe tama kasa budewa saboda azaba ki ta ke kamar bayanta ba a jikin ta ya ke ba, haka ta din ga rusar kuka lallabata ya ke amma kamar kara tunzura ta ya ke.

Hankalinsa ya tashi ga lokacin dawowar Alhaji Ghali ya kusa dabara ce ta fado masa ya daka mata tsawa "ke! dallah ki rufan baki ban miki kashedi ba, wallahi ko kiyi shiru ko na maimaita abun da nayi bana san iskancin banza kin jini ko?"

Gaba daya ta gigice ta toshe bakin ta saboda tsoro gaba daya bayan ta ciwo ya ke mata dan bazata iya motsawa ba sam saboda azaba, yaja tsaki "mtsww! raguwar banza raguwar wofi, saura naji nishin ki ko kuka kuma wallahi kika fito ni da ke nai."

Ya fice ya barta cikin tashin hankali kuka tasa mai cin zuciya, "ya Allah na tuba astagfurullah Allah ka yafe mun, Allah ni baiwarka ce makaskanciya Allah karka bawa wannan bawa naka damar cigaba da cutar dani, Allah na rokeka ka kawomun karshen wannan lamari, Allah ka shiryi mijina Allah ka dawo da shi hanya madaidaiciya, Allah na tuba astagfurullah!.

Allah na rokeka ka saukaka kamun ka kawon silar da zan bar wannan gidan, saboda ba alkhairi sam a cikin sa Allah ka juyo da hankalin mahaifina kai na, Allah na rokeka ka yafemun ya Allah."

Haka ta din ga kuka tana addu'o'i tana rokon Allah amma sam ta kasa zama kuka ta ke ta mike kamar yar kaciya dan din kin da akai mata ma ga farke, ta nufi bandaki ta tara ruwan zafi ta shi ga ciki wani ihu ta saka ta fito haka ta daure ta kara ruwa ta dan gasa tai wanka ta dauro alwala.

A gicciye ta ke zama dan ta kasa zama sam haka tai sallar azahar ta kwanta tana lazimi cikin tana ta zil zil, ta shafa shi a hankali ta fashe da kuka, tabbas ciki nai da ita dan gashi yana ta zillo taci gaba da kukanta da addu'a.

Alhaji Ghali yau yai alkawarin kebewa da matarsa ko ta halin yaya saboda bacin ran da Baby Chakwai ya guma masa, hakan yasa yayo mata siyayya mai dumbin yawa ya kawo mata yayo mata shopping lodi guda ciye ciye da shaye-shaye sai magriba ya dawo gidan.

Hakan yasa bai fito da kayan ba ya shi ga Baby Chakwai yai masa banza har lokacin baccin su yai yai kwanciyarsa, Alhaji Ghali ya samu ya busa masa maganin nan bacci mai nauyi ya dauke shi sosai ya samu ya fice ya bude mota ya debo kayayyakin daya siyo mata ya nufi dakin cikin sa'a ya ji kofar a bude bai yi tunani ba.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now