page 2

109 6 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

          *RUMANATU DILLALIYA*

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
      *(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp  nomber*
08085898952


*Duk wanda ya siyarmun da book ɗina to wallahi ban yafeba Allah ya isa book ɗina free ne bana siyar wa bane duk wanda yayimun amfani da book ɗina batare da izininaba to ban yafeba.*



*Page 2*
Hanyar gida ta nufa harta zo ƙofar gida saikuma ta tsaya tayi shiru, saikuma ta gyaɗa kai ta miƙe kawai tafasa shiga gidan.

Wani gida ta shiga, inda ta tarar da matar gidan tana girki akicin kujerar dake tsakar gidan ta ɗauka ta zauna akai ta kalli matar tace, "Maman Safiya yau babu abun siya ne?". Wacce aka kira da maman Safiya ta kalleta tace,"Wallahi babu gashi yaune ranar zubin adashina tunɗazu mai adashinnan takemun aike nikuma bani dako ficika agidannan".

Gyara zama Rumanatu tayi sannan tace,"Maman Safiya tunda kuɗi kikeso maizai hana acikin indomei ɗinku kiɗebo mun guda uku insiya kinga har ɗan ragowar canjima kyasamu bayan nazubin adashin". Da sauri maman Safiya tamiƙe,"Wallahi kinkawo shawara shiyasa nake son inga kinzo gidannan bara inyi maza inɗebo". Ɗakinta ta shige saigata ta ɗebo su guda uku ta kawo mata, ɗari biyu ta bata dama ita babu ruwanta kodan kadinga siyar mata da kata to zata siyi abunka da daraja shiyasa mata suke son kawo mata kayan siya.

Abaƙar laida tasaka ta futo daga gidan, kanti ta huce kai tsaye. "Isah mai kanti bani ƙwai biyu maggi na goma saika bani cingom na ishirin." ɗakkowa yayi ya bata saita huce gun mai kananzir. "Tanimu bani kananzir na ɗari biyu gobe zan kawo maka shaddar saimuyi zamiya aciki". "Kai dillaliya harna gaji da jiranki kuma wallahi gun bazawata nakeson zuwa shiyasa nakeson sabon kaya". "Karka damu goben nan zan kawo maka sha kuruminka". Jarka ya ɗakko ya zuba mata ta amsa ta huce gida.

Duk suna tsakar gida azaune sun zuzzuba tuwo miyar kuka suna ci babu wanda ta cewa ko ƙala ta buɗe ɗakinta ta shiga ta futo da rishonta ta zauna aƙofar ɗakinta ta gyarashi tas ta zuba masa kananzir takunna ta shiga ɗaki saigata da tukunya ta ɗora indomei ta, nan danan ƙamshi yafara tashi mutanan gida suka fara haɗiyar yahu, dama tana sane.

Indomein ta tana gama dahuwa ta fasa ƙwanta ta yanka albasa ta ɗakko kasko ta soya ƙwanta, nan da nan gida ya gaure da ƙamshin ƙwai, kowa binta yakeyi da kallo, abba yace"Ke ƴar rainin hankali kullun bakida aiki saitayarwa da mutane kwaɗayi to wallahi koki zubomun tawa kokuma inɓallaki acikin gidannan inga uban da zai hanani". Wainar ƙwanta ta ɗora akan indomei ta sannan ta kashe rishon ta kalleshi tace,"Wallahi inkaga kaci wannan indomei to kaci hantar uwarka, banza mara aikinyi nima sana'a nakeyi kaima kaje kayi kaci babu wanda zai hanaka, kuma zancan ɓallawa dakakeyi inka isa kazo kamun mugun kalloma kagani inba akwasheka agidannan ba". Azabure ya miƙe yayo inda take juke tasss! Ya kwasheta da mari. "Ni ka mara ko? Wallahi saikayi babbar nadama acikin gidannan". Lubabatu tayi carabb tace,"Saidai kekiyi nadama banza dangin mayu". Kallonsu tayi kawai saikuma tayi murmushi ɗakinta ta koma taɗakko laimonta da cokali tazo ta zauna tafara cin abincinta shikuma Abba ya koma gunsa ya zauna yana zazzare ido irin manya anyi hukunci.

Tana cinyewa ta ɗebo ruwa aɗan durom ɗin ɗakinta tayi wanke-wanke ta maida kayan ɗaki tayi alwalar magariba tayi sallah tana idarwa ta rufe ɗakinta tafuto daga gidan.

Kai tsaye wani ƙaton gida ta nufa wanda ba a gama ginashiba amma anfara ginin anan duk wasu ƴandaban unguwar dama na wata unguwar suke haɗuwa suna sharholiyarsu nan ta shiga.

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now