page 5

68 7 2
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
______________________________
*We are here to educate motivate entertain our readers*
_____________________________

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

           *RUMANATU DILLALIYA*

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱


©
*Zainab Abdullah*
      *(Real_shaxee)🍒*


*Email*
rzainababdullah@gmail.com


*Page 5*
"Gaskiya alhaji Abdullahi naji matukar dadi da wannan shawarar taka kuma na amunce,amma a ina zamu samu wannan yarinyar kuma karka manta hajiya Sakina itace duk mai hadda sa komai wallahi burinta kawai Marwan ya lalace shikuma yakasa ganewa gani yake duk duniya bashida masoyi sai ita". "Duk kabar mun wannan a hannuna zansaka P.A dina yasamo mun yarinyar sai muyi bincike tukun kafun ayi komai, ita kuma Sakina kabar ta da Allah batafi karfin addu'a ba, yanzu tashi mu koma office".

*Wanene alhaji Munzali*
Alhaji Munzali wani attajiri ne wanda yake da matukar tsoron Allah ga son mutane da kyautata musu,kowa yana matukar jin dadin zama tare dashi, su biyu rai iya yensu suka haifa suka mutu ta hanyar hatsarin jirgin sama,sun barshi da kanwar sa mai suna Mariya yana matukar sonta, ya cigaba da kular musu da dukiyar su, inna ya auri matarsa Sakina, Sakina ta kasacce macece wadda Allah yayiwa shegiyar kissa komai zatayi tasan yadda zatayi batare da anzar getaba bata da hali mai kyau kwata-kwata.

Alhaji Munzali bayajin dadin zama da ita hakama Mariya, bata taba haihuwa ba, alhaji Munzali kuma yana matukar son yara,hakan yasa alhaji Munzali yafara naiman aure, hankalin Sakina yayi matukar tashi babu yacce bata yiba amma ina saida akayi wannan auran inda ya auri Fadima, mace mai hankali da dadin zama.

Tasha wahala agun Sakina amma bata taba korafiba, ita da Mariya tasu tayi matukar zuwa daya, sauda dama tasha yimusu sharri amma ko mariya zatayi magana sai Fadima ta hanata, tun alhaji bai ganoba haryazo ya gano.

Lokacin da ciki ya bayyana ajikin Fadima Sakina haukane kawai bata yiba, tasha zuba mata maganin zubewar ciki a wani abincin amma sai Allah ya tsareta, ganin yadda alhaji duk yamaida hankalinsa akanta nanma takara rikicewa ana haka harta haifi danta namiji aka saka masa Marwan, Sakina sanda aka gaya mata haihuwar har suma tayi dan furgita, yaro yanata girma inda alhaji ya dau son duniya ya dora masa,alokacin akayi bikin Mariya, alhaji Munzali yanada wani babban amininsa mai suna alhaji Abdullahi wanda komai nasu tare sukeyi.

Marwan yanada shekara bakwai babarsa takuma samun ciki, Sakina takasa sakat, bokaye kuwa tabi sunfi kala nawa amma ba nasara, aranar da Fadima ta haihu tarasa ranta inda ta haifi namiji, alhaji Munzali bakaramun girgiza yayiba da mutuwar haka akayi mata suddaja aka kaita makwancin ta, Mariya kuwa tayi rantsuwa ita zata rike jariri dama bata haihuwa saboda tasan zaman sa acan kamar angama salwantar dashine,haka alhaji Munzali yabata shi inda yarada masa suna Abas.
Tun daga sannan Sakina ta kudiri gurbata Marwan, kullun cikin cusa masa munanan halayya take harya girma.

Ita takoya masa shan kayan maye taha dashi da wani dan uwanta maisuna Saif, shiyake kara ingizashi da alhaji ya gano yaita yimasa fada yahanashi kudi amma Hajiya Sakina ita zata zauna ta warware nasiyar takuma bashi kudi, bin matan banza ne kawai takasa nasarar sashi yayi, alhaji Munzali ya naima masa aure duk dan ya gyaru, sanda aka kawo matar sai Hajiya Sakina ta zuga Marwan akan karya kwanta da matar aikwa ya dauka suka fara zaman kishi da matar kullun matar cikin kuka take, duk hakan bai ishe taba saida tasa ya saketa saki uku kuma tasa ya gudu, duk dan kar ayi masa fada, ahaka har aure hudu akayi masa amma duk hakance take faruwa.

*Wannan kenan*


*Adadin comments adadin type🤷🏻‍♀*

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now