page 6

79 4 4
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

_________________________________
*We are here to educate motivate entertain our readers*
________________________________

       
👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱
             *NIDA  MARWAN*
👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱


©
*Zainab Abdullah*
        *(Real_shaxee)🍒*

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

🔻
*Na jamza wa book din nan suna daga RUMANATU DILLALIYA zuwa NI DA MARWAN saboda wani dogo tunani dakuma shawar warin da aka bani, ina fatan zaku amshi wannan gyaran nawa.*



*PAGE 6*
Rumanatu tashigo cikin gidan da bakar laidar ta ahannu, kujera ta ajiye a kofar dakinta sannan taje bakin murhu ta dakko kokon ta ta dawo ta zauna, sugar da kosai da fanke ta siyo, nanda nan tahau karin kumallon ta cikin kwanciyar hankali.

Malam Musa yana futowa daga daki ya kalleta yace, "A haka dai zaki kare kullun cikin cin kudaden mutane nakusa dai maganin ki, Sadiku mai shayi zan bawa auranki kowa ya huta agidannan." "Ayiriri nanaye! Wallahi dana fi kowa farin ciki acikin gidannan, sai muga karshe mara kunya." Lubabatu ce take fadar haka tare da gutsuro katuwar lomar tuwo takai bakinta.

Wani malalacin murmushi Rumanatu tayi sanna ta kallesu tace, "Inma dan insammaka kosai kayi abba to Wallahi ko guda daya bazan bakaba, dan narantse duk abunda kayiwa uwata saina ramashi acikin gidannan, kuma sanin kankane babana tun yana da lafiyarsa yake mun addu'a akan in auri muji nagari wanda zan huta kuma nasan addu'arsa bazata fadi abanza ba, kekuma da wani wawwaran bakinki kike wani magana zanyi maganin kine." "Kan uban can! yanzu Rumanatu nikike gayawa hakan? To wallahi zan baki mamaki asatin sama zan aurar wa Sadiku ke inhuta da mugun halinki,sakarar banza kawai." Yana gama magana yasa kai ya fuce daga cikin gidan yana Mita.

Jamila ta kwashe da dariya ta kalli Lubabatu tace, "Ai wallahi Lubabatu ranar bikin harkida zamu sha dan dadi, wayaga matar mai shayi, ni Safiya maza ma kifuto daga dakinnan kizo kimun wanke-wanke."

Saida Rumanatu ta gama  shan kokonta tas tacinye kosanta sannan ta tashi tsaye ta kallesu tace, "Tabbas lokacin dazan kara koyawa yan gidannan darasi yaza gayo, sanyin danayi kwana biyune yasa akemun haka tabbb za'a yita kuwa." Dakin ta tashige.

Sukuma suka kwashe da dariya,Safiya da ummi da Amina yayan Jamila kenan, "Umma wai yaushe ne zakiban kudin siyayyar ne? yaufa saura kwana shida akawo kayan laifan amma kinyi shiru." Amina ce take magana. "Karki damu ai bikin ki sai kowa yafade shi kibari anjima za'a kawo mun kudin adashin sai ku tafi kasuwar nima inkarasa siyayyar abunda zanyi."

Malam Musa yana futa baizar ce ko inaba sai gun Saduku mai shayi, da mutane agun dan haka saida ya tsaya yadan sallame su sannan suka ja gefe, "Yauwa Saduku mai shayi dama nazo maka ne da wata muhimmiyar magana, dama Rumanatu nabaka auranta in kanaso." Washe baki Saduku yayi hadda sosa kai irin kunyarnan, "Mai zai hana malam Musa wazai ki auran kyakykyawar yarinya irin wannan, wallahi ni na amunce dama zama da mata daya ya isheni kuma ashirye nake." "Yauwa Saduku yanzu abunda za'ayi zuwa dare ka kawo kudin sadakinka dubu talatin kawai sati nasama sai a hada bikin da na yar uwarta Amina." "Aikwa ana kidar da sallar magariba zan kawo maka kudin sai inje inyiwa daya dakin indan shafa masa farar kasa, amma kuma batun laifefa?" "Ahabb karka damu da wannan in andaura auran Allah ya hore saika dinka mata kayan, yanzu dai ina jiranka dan sauri nake namakara akasuwa." Sallama sukayi ya tafi, yayinda Saduku yaketa fara'a yana sanarwa da mutane abun alkairin da akayi masa.

*Adadin comments adadin type🤷🏻‍♀*

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now