page 4

82 5 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
______________________________
*We are here to educate motivate entertain our readers*
_____________________________

👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻

        *RUMANATU DILLALIYA*

👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻


©
*Zainab Abdullah*
     *(Real-shaxeee)🍒*

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*WhatsApp bomber*
08085898952

*Page 4*
Jamila ta rufa masa baya suka shige dakin, Lubabatu ganin batada wata mafuta illa tayi yadda yace, dan haka ta aiki daya dan nata Sile yasiyo mata panadol da munsileta ita kuma ta dora ruwan dimi dan ta duma ma masa jikin sa.

*Washe gari*
Rumanatu tana tashi tayi sallah tayi wanka tazo bakin murhun dan daukar abun karinta, Jamila tana bakin murhun ta dama koko tana kokarin yayyan ka tuwon dumame ta duma mashi, "Ga kofin nawa azuban kokon banda dumame". Wani kallon banza ta watsa mata, "Watakan ga baiwar kiko? tagama bautar dafawa ke kina zaune abanza kizo kawai kidiba kici ko?to wallahi baki isaba".

"Aikwa wallahi baki isaba koki zuba mun  kokuma kowama yarasa shi wallahi,nikuma infuta inci mairai da lafiya". Ummi yar gidan Jamila tayi huf ta futo daga dakin su, "Wallahi baki isaba Rumanatu kinyi kadan kizaki uwata kizauna lafiya, kedin banza mai akai akayi ki?". "Ke baki isa in yi dakeba dan nafi karfinki wallahi za'ayi biyu babu acikin gidannan inkuma an isa kar azubamun agani". Malam Musa jin haya niya yasa shi futowa da sauri, "Ke Jamila maza kizuba mata dan kinsan inta bata wannan kokon banda abunda zan wani kudin dazan bayar ayi wani kokon," ko magana Rumanatu bata kuma yiba ta dire kofun tayi fucewar ta daga cikin gidan.

Jamila ta kalli malam Musa tace, "Wallahi malam kaikake kara daurewa yarinyar nan gindi, shiyasa take duk abunda takeso". "Ke dalla rufe mun baki kinsan halinta dai, yanzu zata iya zubar da kokon kinga mu muzauna da yunwa ita kuma ta fuce taci ta koshi, kubarni da ita kwanan nan zanbada sadakar ta ga wani musakin ko fakiri muhuta". "Yauwa malam daka gama burge ni wallahi, ke ummi maza kizo ki dau naku kitawo da kwano inzuba muku tuwon".

Gurine mai dauke da shukoki ga kujeru da tebura wanda hakan yake nuna cewa gun hutawa ne na masu kudi.

Wasu dattawa ne azaune akan kujera daga gani tattau nawa suke yi, alhaji Abdullahi da alhaji Munzali ne.

Alhaji Abdullahi ya kalli alhaji Munzali yace, "abokina kadinga kwantar da hankalin ka,mudai mucigaba da addu'a insha Allah watarana zamuyi nasara". "Abdullahi kenan  kamar ka manta halin Marwan ne? Kullun cikin tashin hankali nake, shine shan giya kai duk wani abun maye yana sha, inda Allah ya taimake ni baya naiman mata,gashi kuma yaki zaman aure yau aure dai-dai har guda hudu ina daura masa amma kowacce bata huce kwana biyar yake sakinta kuma yagudu sai tsawan lokaci za'a ganshi, gashi kuma banason aibata shi kokuma mugun baki". Alhaji Abdullahi ya furzar da iska mai huci ya kalli abokinsa yace, "Ga mafutar mu guda uku rak, na farko zamu naima masa yarinya futunanniya mara tsoro amma wadda take da tarbiya mu aura masa ita, nabiyu kuma kace masa muddin yasake ta to baka yafe masa ba, sannan na uku kuma addu'a da sada ka, ya kake ganin shawara ta?".

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now