page 1

393 13 2
                                    

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

       *RUMANATU DILLALIYA*

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

©
*Zainab Abdullah*
          *(Real_shaxeee)🍒*

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*WhatsApp bomber*
08085898952

*BISMILLAHIR RAHMANIRRAHEM*

(Da sunan Allah mai rahma mai jin kai yabo ya tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad s.a.w)

*DEDICATED to*
*Surukarmu ce pans*

*Tsokaci*
Gidane mai dauke da dakuma falle-falle guda biyar sai bandaki babba, sai gun girki ba kicinba gefan tsakar gida me aka samu akadan yimasa rumfar kwano, daga sama saboda ruwa, to duk anan suke girki,sai tsakar gida mai dan girma sai soro.

Kana ganin gidan kasan bana masu kudi bane, saidai rufin asiri,kuma kaf unguwar ma haka suke saidai dai-dai Ku acikinsu sune masu hali.

Malam musa shine mai gidan yana da mata biyu Aisha da Jamila, Allah yayiwa Aisha rasuwa bayan shekaraBiyar da suka huce,tabar yarta daya tilo wato Rumanatu bayan mutuwarta malam Musa ya karo aure, inda ya auri wata bazawara mai suna  Lababatu, inda tazo da yayanta biyu duka maza, Jamila kuma tanada yaya uku, zama ake agidan narashin dadi.

££££££££££££££££££££
Rumanatu ce azaune a tsakar gidan, tana ninke kayan ta data wanke dazu,Lubabatu ce tafuto daga dakinta ta kalleta tace, "To uwar kwashe-kwashe yaudai naji shiru ba'a debo wata rigimar ba, kodai an nutsune? au dama nasan keba yarinyar kirki have,saidai ubanki yaita wani yabonki yau ina yabon yake? Kuma maza kije ki doran tuwan dare".

Duk wannan surutun da Lubabatu take baisa Rumanatu ta daina abunda take ba,kuma bata dago kanta ta kalleta ba, saida tagama ninkin ta tas tukun ta kwashe su ta mike tsaye ta kalleta tace, "Iallaima wannan matar nizan yimiki tuwo? Ashe kuwa zaku kwana da yunwa a gidannan,kuma batun dakko rigima yanzu nafara, nidai bazan daina sana'a taba ta dillanci kema in najiki kwana biyu shiru ba labari". "Kedai bari wallahi ina bukatar kudi gashi kuma mijin nawa ba bani yake ba ".

Tabe baki Rumanatu tayi sannan tace, "Wallahi mata kuna bani mamaki kuyita zama maza suna wahalar daku,to bara kiji kidinga dibar kayan sa kina soyarwa kina samun yan kudinki".

"Kayan sa kuma!? Inya tamba yeni ince masa me?". Matsowa Rumanatu tayi ta dafa ta, "Kinga ki kwantar da hankalin ki ga yan dabaru n mu na mata, kice masa kema baki gansuba, kokice tunda aka kaiwa mai wanki da aka dawo da kayan baki gansu ba aciki, inkuma kayan abinci ne kidinga diba yadda bazai ganeba insiya in baki yan kudinki". "Kai amma kin kawo dabara, shekara jiya naga ya shigo da gajerun wanduna guda biyar daya siyo a gwanjo zaki siya kuwa?". "Ke ni nan dakika ganni babu abunda bana siya har gajeran wando dayake amfani da shi inbaisha jikiba siya zanyi,maza jeki dakko muyi ciniki".da sauri ta tashi tashige dakinta saigata da wanduna.

Dubu daya da dari bakwai ta bata ta futo daga gidan tabar matar tana murna dan rabonta da rike kudi masu yawan wannan harta manta.

Kai tsaye Rumanatu gun wani mai guga ta nufa a shagonsa yanata gugarsa". "Jafaru mai guga ga gajerun wandunan na samo maka, amma gaskiya dari hurhudu zaka bayar dan masu kyaune da karko".

"Karki damu dillaliya ainagansu wallahi,to ga kudinki nan saura singileti". Ta amsa ta kirga, "Karka damu suma zan kawo maka".

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now