PAGE 7

169 19 3
                                    

👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱
           *NI DA MARWAN*
👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱👩🏻‍🦱

©
*Zainab Abdullah*
       *(Real_shaxee)🍒*

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*A gaskiya nadaina post a WhatsApp saboda sai a wattpad saboda bazan dinga bata lokacina abanza ba inyi type amma comments saiya gagara tunda bakwaso sai inkai inda ake so, ina fatan kun gane maiso zai iya following dina duk sanda nadora zai ganshi*



*PAGE 7
Duhu yana yi, saiga Saduku mai shayi nan yazo dama malam Musa yana kofar gida yana dakwan sa a kofar gidan, babbar tabar ma ya shinfuda tare da makotan sa guda biyu daya kirawo dan su shaida,shima Saduku da mutun biyu waliyan sa suka tawo.

Rumanatu tana bayan kofa ta labe tanajin abunda suke tattaunawa ta kwashe da dariya, "Lallai ma wannan mutumin ko tsoron Allah bayaji,kamar ni za'a bashi kyauta, kaikuma abba wallahi saina jangwalo maka tsiya dani kake zancan ne." Kwafa tayi ta shige cikin gidan, su Amina suna ganinta suka kwashe da dariya, "Kunga amaryar mai shayi, harkin fara kwamshin citta da Lipton hhhhh." Ko kala bata ce musuba illah murmushi datayi musu ta shige dakinta.

A kofar gida kuma, an gama duk wasu zantuka tare da bada sadaki dubu talatin saikuma dubu ishirin daya bada dan abawa amarya tayi hidimar  biki.

Malam Musa yana shigowa cikin gidan duk ya tara kowa a tsakar gida hadda Rumanatu.

"Yauwa kamar yadda kuka sani waliyan su Saduku mai shayi sun zo yanzu sun kawo sadaki da kudin shagalin biki,dan haka antsaida ranar biki za'ayi shi rana daya dana Amina, dan haka Rumanatu ungo dubu hansin dinki saiki je kisiyi kayan gado da komai da komai, dan wallahi fucikata bazan kashe miki ba, aidama kina sana'a da kudinki ahannun ki." Hannu tasa ta amshe kudin cikin farin ciki.

Wata shewa mutanan gidan suka kwashe da ita,abba yace,"Allah shi kara! badai baki da aikiba sai jangwale-jangwalen fadaba da dillanci aiyanzu kinga karshen iskanci yanzu hhh."

Mikewa Rumanatu tayi ta kallesu tace, "Ayidai mugani indai nice." Gaba daya tama fuce daga cikin gidan.

"Kurabu da yar banza zandai aurar da ita inhuta da wannan shegan takar tata, Lubabatu ni maza ki dakko mun abincina kikawo mun daki." Tashi yayi yashige cikin dakin Lubabatu.

Rumanatu tana futa ta huce gun mai gasa kaza tasai guda daya mai zafi, sannan ta huce babban kanti tasai yogot babba daya da laimo, sannan ta huce gida, dakinta tashige ta cita koshi abunta.

Da safe Rumanatu tayi karinta mai rai da lafiya rana tanayi ta shirya ta dakko kudin da jiya aka bata da wasu kudaden ta tafuto tarufe dakinta ta kallesu tace, "To nidai na huce kasuwa zanyi siyayya kuma daga nan zan huce inkai dinki." Wata uwar dariya ummi tayi tace, "Ai gwara kifara siyayya amaryar mai shayi, ai gaskiya munada shagali agidannan dan har ranar party din shan shayi zamu ware musha mu koshi."

Fucewa tayi daga gidan bata ma kulasuba, kaisaye kasuwa ta huce, tasai kayanta masu kyau guda hudu hadda shadda aciki sai tasai mayafi da takalmi tadan kara kayan kwalliya, sannan ta huce gidan wacce take kaimata dinki.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 16, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NI DA MARWANWhere stories live. Discover now