1⃣0⃣🔚
Zee Na zaune a tsakar gida tana uban wanke-wanke Wanda yazame mata tilas, sai zum6ura baki takeyi da k'unk'uni, mamanta tana kallonta amma ta shareta.
Da gudu k'aninta Sageer yashigo yana hakki, daga mama har zee kallonsa kawai sukeyi, cikin hakki yace yaya Zainab 'yan sanda sunkama k'awarki yanzu.
Dafe k'irji zee tayi, tace sageer wace k'awar tawa?.
Yaya Taufeeqa, wai naji mutane nacewa sata tayima wata mata ana gobe sallah.
Sallallami Maman zee takeyi kawai.
Zee kam jikinta sai rawa yakeyi.
Basu gama tu'ajibin abinda yafaru da taufeeqa ba sukaji sallama.
Jiki a sanyaye suka amsa, amma ganin yayar jabeer da k'anwar babansa sai gabansu yafad'i, mama cikin sanyi take musu maraba, Dan tabbas taji ajikinta ba alkairi bane ganin iya yalwa agidansu, kuma awannan farar safiyar.
Bayan sunshiga d'aki sun zauna zee tashiga tana gaidasu, ganin Harar da iya yalwa kemata yasaka gabanta tsananta fad'uwa.
Tashi tayi tafita, saidai kuma kafin ta ida fita iya yalwa ta tsaidata dafad'in dawo Zainab, aii zuwan nakine.
Dawowa zee tayi ta zauna, mama dai batace komaiba, saida suka gaisa sannan iya yalwa tace baban Zainab fa? Dan tare muke da bak'i suna a waje.
Bak'aramin fad'uwa gaban mama yayiba, murya a sanyaye tace yana d'akinsa bara natadosa, batareda tajira amsarsuba tafita kiransa.
Zee dai tana zaune tsuru-tsuru, kareema sai banka mata harara takeyi dajan tsaki, itamadai iya yalwa kallonta tsana kawai take binta dashi.
Bayan mama tayima baban Zainab bayani yamik'e cikin hanzari, k'ofar gida yanufa, manyan attijaine maza hud'u, cikin gidan yaymusu iso, bayan gaishe-gaishe. Wan baban jabeer yace Malam Usman dama dai wani abune yakawomu, amma munaso kayimana k'yak'yk'yawar fahimta dan ALLAH.
jinjina kai kawai baban Zainab tayi danya kasa magana.
Yacigaba da fad'in, dama jiya damisalin 10pm akazo har gida aka kama jabeeru, ahannun 'yansanda yakwana, to yaudai dak'yar muka samu ganinsa.
Bayan munbi ba'asin kamashi da akayi police sukaimana bayani akan wai yad'ibarma ogansa kud'ine ashago.
Hankalinmu yatashi, danba'a ta6a kama jabeeru da makamancin wannan halinba, wannan yasa mukace abamu damar mutanbayesa, sunyimana wannan alfarmakuwa, akafiddomana jabeeru muka tambayesa, bai 6oye mana komaiba yafad'a mana Zainab Ce ta takurasa akan yamata kayan sallah, idan bahakaba tafasa aurensa, wannan dalilinne yatada masa hankali yad'iba kud'in ogansa har 35k.
Wlhy Malam Usman bakaga yanda suka canjama yaron kamanninsaba, sunmasa duka bana wasaba, to yanzudai ga kud'insu munhad'a musu dak'yar zamukai mu kar6osa.
Asha-asha Abu baiyi dad'iba Cewar Malam Usman cikin tsananin 6acinrai.
Yacigaba dafad'in, dalilin zuwanmu nankuwa shine gsky mun haramtama jabeeru auren Zainab, Dan kaitsayema mahaifiyarsa tace inhar ya yasake kallon Zainab batayafe masaba barema aurenta, kaga bikinsu sati uku kawai yarage, to gara tunda wuri kusan halin da'ake ciki.
Dan aganinmu Barin Auren shiyyafi alkairi, tunkan ya aureta yafara saka Kansa cikin Matsala da halinda banasaba, yana mayaraya, inaga tazo gidansa? Ai ba'asan mizata sakashi aikatawaba kenan?.Wasu kwallah masu zafi suka cika idon baban Zainab, yagogesu tareda yimasu godiya, hukuncin dasuka Yanke daidaine, kuma subar kud'insu zai biya afiddo jabeer.
A'a suka fad'a at are.
Baban Zainab yace inhar kun hanani kar6o jabeer da kaina to kunnunamin jabeer ba d'ana baneba kenan?.
Hak'uri suka basa sannan suka mik'e sukatafi harda baban Zainab.
Zee kam kuka takeyi rirus dakiran tabani ta lalace, su tausaya mata tanason jabeer wlhy, Dan ALLAH karsu rabasu, wlhy kuskurene bazata sakeba, tanasonsa sosai.
Wata maguza mamanta takai mata abaki saboda bak'incikin da zee ta haddasa mata, batasan kawai tafara jibgartaba, gashi babu kowa agidan, saida Tamata dukan tsiya sannan takoma gefe tana kuka dafad'in zee kin cuceni, ALLAH ya Isa ban yafe mikiba, kinzubar mana da kimarmu da tarbiyyar damuka baki zakijamana zagi agari, teer da halinki Zainab, tir dahali irinna k'awayenki, waccan tayi sata kekuma kinsaka mijin dazaki aura yayi, ALLAH yawadaran halinku.ALLAH saiya sakamana zagin da kukeja mana agari.....
Kuka sosai Maman zee keyi, itama zee d'in haka, bata ta6a tsanar kantaba irin yau, dalilin San zuciya tarasa abin sonta, anfasa aurenta ana saura kwana 21, *_Sanadin bikin sallah_* takafama kanta tarihin dabazai ta6a goguwaba, k'ilama yazama sanadin dazata rasa mijin aure anan gaba, wani irin kuma maiban tausayi tafashe dashi.😭

YOU ARE READING
SANADIN BIKIN SALLAH!!
Short StoryYanda ƴammata ke mancewa da kansu da martabarsu a yayin bikin sallah, burinsu su haska kawai wajen samari, ko ina suka zagaya a yabasu su da kwalliyarsu, ajiye al'ada da addini dan kawai ace kaine wane, bin kowacce hanya wajen neman kayan bikin sall...