HAEEDARR PAGE 1↔5

34 0 0
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂
            HAEEDARR
             (live story)
                        🍂🍂🍂🍂🍂

Writing by
ALIYU ISHAQ
(fast class)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Wannan labarin wanda nasama suna (HAEEDARR) gajeren labari  labari nehh daya faru a gaske dan haka ban yarda wani koh wata ya chanza lbr daga wata ciga zuwa wata ciga ba

SHINFIƊA*_

_Bismillahir Rahmanir raheem,na fara da sunan Allah me rahma me jin kai,yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanallilahi wata ala.Tsara da aminci su tabbata ga annabi MUHAMMADU cika maki annabawa shugaban manzanni da ahalin gidansa baki ɗaya_

🅿  1↔5



Da sunan ALLAH mai rahma mai jin kai





"Haeedar " haeedar "haeedar  muryan wata yar tsohuwa nakei wadda baza wuce shekara hamsin da biyar ba a duniyar sai kalawa dan saurayin da bazai wuce shekara takwas a duniya ba kira shiko saurayin yana jinta ya lafe a soron gidan yayi shuru inda yake ta fada a zuciyarsa yana fadin ita wannan tsohuwar bazata bar mutum ya wataya ba kenan yanxun idan suka fara buga boll din fahh cikin zafin rai ya dawo gidan yana fadin




"Kai kaka dan Allah saura fa kadan su fara wasan boll din kuma ni kadai ake jira fahh dan Allah ki bari idan na dawo bayan sallar magariba sai nama dibo ruwan ba sai an samo wani ya dibo ba





Kaka tace" to kai inbanda haukar ka to da wani ruwa zamuyi alwala bayan kasan yanxun haka ma malam na hanya bai dawo kazo koh kai daya nehh ka dibo mana sai muyi sallah idan yaso sai a samo wani ya karasa




Badan raina yaso ba na dauki bokitin diban ruwan nayi waje ina mai kallon kanwata dake cinyar kakar tamu a zuciyata nace to ita wannan mene amfanin ta a gidan da ba zata dibo ruwan ba haka dai na wuce ina yan magan ganu na koh kulani kakarmu batayi ba dan tasan tanayin magana wani sabon darun nehh dan da wuya na dibo ruwan ma




Haka naje bakin rijiyar nan sai kunkuni nakeyi duk ga yara nan sa'anni na amma duk sunki min mgn sabida sun San zan Iya chasasu kuma su kai kara gidan mu
Kuma KAKATA ta tsaya min haka dai na samu na dibo ruwan na taho a hanya na hadu da YA malam ya dawo gida nace ya malam



Yace a haidar kai ne nace nine wai ruwa kaka tace na dibo kuma zamu fara boll aka ce sai na dibo nan yace




"To in banda abinka haidar ae yaune kurun watrana sai labari ka daina damuwa nan nace to malam kabani biyar na sai alawa nan ya dauko goma ma yace gashi duka na baka sabida ka debo ruwan nan na karba ina ta murna na kai ruwan gida na fito boll dina a ka fara buga ta dani dan jurana suka yi abokan nawa sukayi dan idan bani sunce boll din Bata dadi




            ASALIN LABARIN


Malam ishaq da kaka hafsatu malam ishaq haifaffen garin bauchi ne inda hafsatu take a katsina sune kakannin mu kuma tushen family din mu malam Ishaq yana da shekara  65 inda kakarmu ke da shekara 55 suna da yaya guda takwas a duniya inda hudu suka koma ga mahaliccin mu yanxun saura maza biyu da mata biyu Aisha itace babba daga Ita sai Bilkisu sai shamsudden wanda mukecewa baba Shamsi sai Yusuf wanda shine karamin su shikuma muna kiransa da baba dan gida



Aisha tayi auren ta na farko kuma na karshe a kano inda ta hadu da wani dan yobe mai suna Musa sukayi auren soyayya a yanxun haka su na da yaya goma a duniya ishaq shine Babba wanda muke kira da Abba sabida yana da sunan malam sai Maryam sai mika'il sai Muhammad sai hawwa'u sai Ibrahim sai Hafsat sai abdallahi sai Fatima sai saudat wadda sunan kamar kakarmu taci muke ce mata Hajiya




Sai Bilkisu da tayi aurenta itama a kano inda ta auri wani dan Fulani anan rugar tudun Fulani tana da yaya takwas inda biyu suka rasu a yanxun dai babbar yarta itace Zainab sai nusaiba sai ni haeedar sai kanwata sunan ta hafsat amma muna kiranta walida sai Hassan sai ikram






Baba shamsu ma yayi aure inda yake da yara hudu hauwa'u itace Babba sai mai bi mata yusufa sai sa'adatu wadda muke kira da suhailat sai HAFSAT dai again ita kuma muna ce mata amatullah sabida tana da sunan kakarmu


Sai baba dan gida da har yanxun baiyi aure ba yana kan nema dai



Ni da kanwata Hafsat tun muna kanana muke hannun kakarmu dan ni tun ina jariri na dawo hannunta yanxun inada shekara 8 kanwata kuwa walida a tsakar dakin kakarmu aka haifeta kuma anan ta zauna yanxun tana da shekara 6

                      Cigaban labari


Bayan mun gama boll din ne sai MUKA tafi masallaci dan kullum haka mukeyi da mun gama ball din mu sai masallaci dan gabatar da sallar magariba bayan munyi sallah ba mai komawa gida sai kuma a hau tsokana idan mukaga samari suna hutawa saimu tsokane ka mu hudu idan ka buyomu mu gudu muna ma Dariya idan baka biyomu ba to fahh bazamu bar gurin nan ba har sai mun bata ma dani da wani aboki na umar wanda shekarunmu daya dashi shine babban amini na dan haka bama fada dashi mune oganni a gun tsokana haka xamu dawo gida duk mun gaji bayan anci abinci sai a fito hirar tsakar layi duk Wanda zai wuce sai mun tsokanesa ya kai kara KAKATA bazata yarda ba ita kuma Babar su umar bata da rugima sai dai ta bada hkr kawai.............



Wannan kenan



WhatsApp number 08143314152



By fast class

HAEEDARR (live story)Where stories live. Discover now