🍂🍂🍂🍂🍂
HAEEDARR
(love story)
🍂🍂🍂🍂🍂Writing by
ALIYU ISHAQ
(fast class)________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com🅿 10↔15
Daga marubucin
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
SANDAR GIRMA
And now
↙
HAEEDARRR
(live story)BAYAN SHEKARA 5
A wannan shekarar MUKA zana jarabawar kammala primary nida kanwata cikin ikon ALLAH duk munci bayan an dawo Hutu nehh muka fara zuwa secondary a wannan lokacin na Iya Hausa sosae English ma INA iya karantawa amma bana jin sa makaranta daya muke zuwa da kanwata ita tana bangaren mata wato girls secondary nikuma ina bangaren maza haka muka ci gaba da zuwa makarantar mu
Cikin ikon ALLAH haudar ya dai na duk wani rashin jin da yakeyi ya dukafa akan karatun sa dan idan kaka HAFSAT ta zaunar dashi tana masa fada jikin sa sanyi yake yi dan haka duk ya rage Abu buwa da dama a rayuwarsa
Shima kawun mu Dan Gida yanxun ya zama direban babbar mota Abu daya ya rage masa a bashi mota a kamfanin A A RANO amma duk da haka yana bin ogan sa suna tafiya tare
Bayan shekara uku kawun mu ya sami mota a ranar da ya tafi dauko motar nan yaci buri akan kaka wato babarsa fadi yake yi ta huta duk wata wahalarmu tazo karshe kuma idan ALLAH yaso ya yarda sai ya kaita makka da wadannan burika ya tafi Lagos dan ya dauko motar
A wannan rana nehh abinda bazan taba manta wa dashi ba ya faru a kaina abinda ban taba tunanin zuwansa ba a rayuwa a ranar laraba da misalin karfe goma sha biyu da yan mintina muna kwance acikin dakin mu ni kadai nehh a gado dayake katifar su walida a kasa take ita da kaka nikuma ni da malam muna gado to a wannan rana nehh na hana malam kwana a dakin ma baki daya dan idan muka kwanta tare takurata yake yi idan ina kallo na dan haka na turashi dayan dakin dayake shima da gado da katifah
A ranar sai sha biyu saura na shigo gidan ina shigo wa na kalli bangon dake jikin dakin mu na makotanmu naga ya fara zazzagowa Alamar zai fadi sai na haska da fitilar wayana na gani tabbas hakan nehh banyi mgn ba na wuce ciki dakin na tadda kaka batai bacci ba dayake kullum saina shigo na tadda tayi bacci
Ina jin ta tana cewa kai haeedarr banace ka daina kaiwa dare a waje ba bakajin mgn wlh
Nidai banyi mgn ba dan nasan nayi laifi na huce na kwanta ina kwanciya kanwata tashi ta fita dan yin fitsari dan ya zama mata jiki ma Niko na toshe kunne na da airpice dan yin kallo a ka'idata saina kure volume nake kallo to yauma kamar kullum dai hakan take
Koh minti biyu banba da kwanciya naji Abu rigijib a kaina ba komai bane ba illah ginin makotan mu na kasa daya dako namu shima na kasa tun na da chan suka HADU suka fado cikin dakin mu bansan SANDA na kwallah ihu ba na fara giran sunan kaka ina ihu da Neman taimako
Itama ihun take tana fadin wayyo ALLAH haeedarr dina jama'a haeedarr dina wayyo Allah
Nima naki yin shiru har muryata ta dashe ta daina fita kasa ta rufeni ruf n suma
Chan zuwa jima wa na farfado Abu daya na fara ji mutane ne suke fadin ali ma fahh yana ciki eh yana ciki nan suka fara laluben inda nake koh da naji haka sai na yi mgn da dashashiyar muryata nace gani anan dan Allah Ku taimaka min
Nan aka fito dani ina tashi naga kaka ta acikin kasa ta rufeta tun daga kafafun ta har kirjin ta sun rasa ta yadda zasu fara cirota nan dai wani mutumi ya ja ni muka fito waje naga mutane d dama duk da dare nehh
Achan gefe na hango walida sai kuka take yi naje na zauna a kusa da ita ba afi yan mintina ba saiga shi sun fito da kaka a kusa da malam din mu aka aje ta sai salati takeyi tana ganin malam tasa kuka tana fadin
Malam bazan iya mikewa ba kafata nan yayan ta mata wato iyayen mu suka zo kusa da ita ana fadin ta mike kafar ta amma ina ta kasa da sauri aka samo abin hawa dan zuwa asibiti amma kememe taki zuwa tace sai an tafi dani an duba ni nan aka fara Mata dabara ana fadin ai ni ba abinda ya sameni amma taki yarda nan dai sukace mata nima ZAMU taho daga baya nan Babban jikan ta Ishaq mai sunan malam d mamarmu da yar babarmu suka dunguma asibitin a kake napep dan ganin likita
Suna tafiya naje kurin malam na zauna abinda na fara ji daga bakin sanehh ya matukar razanani ba komai bane illah mutuwa zatayi
To wace zata mutu kakar tawa na fada a zuciyata nan take na kalli malam nace malam wace zata mutu
Ganin da yayi na shiga tashin hankali neh yasa shi fadin ba kowa bafa haka nace ba haeedarr kwantar da hankalin ka ba abinda zai faru insha allahu
Kai kawai na kyada masa amma badan na yarda ba dan ni tunda naji ya fadi wannan kalma nasan naji kamar nayi wa KAKATA kallon karshe a duniya kenan..........
Wannan kenan muje zuwa
WhatsApp number 08143314152
By fast class
YOU ARE READING
HAEEDARR (live story)
Romancewannan labari mai suna (HAEEDARR) labari nehh daya faru a gaske lbrn yana dauke da darussan rayuwa da ban tausayi kai sadai ka karanta