2

787 43 1
                                    


DG
Shafi na biyu (2)

******
Lokaci daya iska me karfin gaske ta taso, gaba daya bana ganin gaba na, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ni, na sani sarai idan har na bari ruwan nan ya taba lafiyar jiki na kashi na ya bushe, ganin da gaske bana ko ganin hanya yasa na makale gefen wani shago na kudundune kaina ina jin matukar tsoro. Ina nan makale yayyafi ya fara sauka a hankali, tsoro na ya dadu, zuciya ta tayi rauni sosai, kamar daga sama naji an dafa kafada ta, cikin tashin hankali na dago kaina,ban samu nasarar ganin fuskar kowaye ba, saboda tsananin hasken torch light din da aka sa aka haske ni. Cikin muryar tsoro na furta

"Waye!"

Be amsa ba, ba shi kuma da niyyar amsawar, illa sake dalle ni da yayi, take hasken yayi tasiri rage kaso tamanin cikin dari na gani na, baya da ƙurar da ta riga ta cika min idon nawa, da sauri na mike ina kokarin daidai ta zaman riga ta, na fara alamun barin wajen, hannu naji an saka an riko ni, cikin wata iriyar murya mara fasali ya furta

"Gidan uban wa zaki? Ai wallahi kinyi kadan tsuntsu daga sama gashashshe."

Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskata jin muryar Garbati, mutumin da ko a mafarki bana fatan hada hanya dashi, waye be san shi ba kaf kauyen nan namu, tantirin dan iska ne, lamba daya, gashi babu wanda ya isa dashi kaf kauyen. Da sauri na ja da baya ina kokarin sake shiga cikin ruwan sosai, damko ni ya sake yi nayi kara da karfi jin zafin rikon da yayi min, ja na ya shiga yi yana kokarin turani cikin shagon da tun zuwa na wajen na lura da yar kofar dake bude, amma banyi tunanin akwai mutum ciki ba, da karfin gaske na hau kokarin kwatar kaina, sai dai ko kusa da hakan ban kai ba , duba da yanayin karfin ba daya ba. Tuni na hau kuka ina magiyar bashi hakuri, tunda ayi ƙarancin shekaru na nasan hakan da yake me yake shirin aikata min. Be saurara ba, ko ma nuna alamun yaji abinda nace, haka ya tura ni ta karfi ya maida kofar ya tura yana sakin wani shu'umin murmushi.

Tuni na watsar da aiken Inno, na shiga ihu da dukkannin murya ta ko Allah zai sa a jiyo ni, dariya ya shiga yi ba kakkautawa.

"Yarinya da kin hakura babu shegen da zaiji ki, uban me ya fito dake a wannan lokacin shegiya."

"Aike na akayi wallahi." Nace ina sharbe hawaye da majina.

"Daidai kenan, idan na ci ubanki zaki gane shayi ruwa ne."

Ya fada yana kokarin matsowa kusa dani.

Sosai na kara karfin murya ta, cikin tsananin tashin hankali, magiya nake masa ina rokon sa, sai dai hakan ba sa ya fasa aiwatar da abinda ya kudurta a ransa. Tun daga nan bansan me ya kuma faruwa ba😭😭

***
***
Tafiya yayi sosai yana mai jin dadin yanayin garin, kafin zuwa lokacin da iskar ta taso, sauri ya kara don ganin ya isa gida, be yi tunanin ruwan zai zo da iska haka ba. Saukar ruwan ne ya rage karfin iskar sosai, hakan ya bashi damar cigaba da tafiyar sa cikin kwanciyar hankalin ruwan na dan taba fuskar sa kad'an-kad'an. Kamar daga sama yaji ihu, ihun ma na mace me karancin shekaru, sai dai karar saukar ruwan yayi tasiri kwarai wajen kasa tantance daga ina ihun yake, hankali ya tashi ya hau neman ta in da muryar ke fitowa, kamar mahaukaci haka ya shiga kai kawo a cikin ruwan, hankalin sa ne ya kai wajen, da wani irin mugun guda ya nufi dan karamin shagon daya gama tabbatarwa daga nan ɗin ne yake jin kukan, beyi wata wata ba yana zuwa ya daki kofar da dukkan karfin sa. Abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali, da gudu yayi kansa ya shiga dukan shi, duka me cike da tsantsar bacin rai. Yanayin rashin karfi da a tattare da Garbatin ya hana shi katabus, sai daya yi masa duka sosai sannan ne hankalin sa ya dawo kanta, tana kwance kamar mara rai, abinda ya dade yana jin labarin yana faruwa ga yara masu kananan shekaru ne ya faru da yarinyar nan, yarinyar da dududu ba zata wuce sa'ar Amal ɗin su ba, da sauri yayi kanta ya dago ta, tuni ta sume saboda tsabar firgicin data shiga, wani irin kuka ne ya taso masa, wannan wane irin rashin imani ne?. Da dukkan karfin sa ya daga ta ya sata jikin sa, be bi ta kan Garbati ba da yake kokarin tare shi, har ya kai kofa maganar shi ta dakatar dashi

DAURIN GOROOù les histoires vivent. Découvrez maintenant