1

14 0 0
                                    

S*°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°* 
             *1441H/2020M.*
          *SHAWWAL/JUNE.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼*

*SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*Alhamdullah, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya kawomu wannan lokaci lafiya, ina godiya ga masoya na masu ƙarfafamin gwiwa domin sake kawo muku wannan labari mai ciki da ban alajabi, musamman my Aunty wato Miss xaks, bani da bakin godiya gare ki sai dai fatan alhairi😍 .*_

        

*SHAFI NA 1📑*

*__________📖* Yau rana ce ta visiting ga ƴan makaran ta, wato boarding school, kowacce ka duba taci ado jira kawai take taji ance anzo mata visiting.

Can na hango wasu ƴan mata su huɗu waɗan da suka yi ado mai ɗaukar hankali, waje ɗaya suka keɓe suka zauna suna firar su cike da kwanciyar hankali da nishaɗi, busu damu da kowa ba, amma duk wanda zai wuce sai ya ɗago ya kalle su musamman wata ƴar farar yarinya wanda ta ƙara haskaka su, suna cikin haka sai ga wasu motoci sun danno kai cikin harabar wannan makaranta, lokaci ɗaya waɗannan ƴan matan suka ɗago ido suka kalle waɗannan motocin masu shigowa cikin wannan makaranta, kuma lokaci ɗaya suka dube wannan ƴar farar yarinya wadda ke tsakansu kana suka buɗa baki a tare suka ce,

"Jamila ga shi ya ƙaraso". Suna faɗin haka farin ciki ɗauke a fuskokin su.

Duban su tayi tace, "to yaza'ayi yanzu?".

Batare da ɓata lokaci ba suka ce, "ki ta shi muje wajan sa".

Kai ta girgiza musu tace, "a'a kubari sugama gaisawa da Malamai nasan zasu sa anemo mu".
Tafaɗi haka ɗauke da murmushi a fuskar ta.

Waɗannan motocin basu tsaya ko ina ba sai gab da office ɗin principal , parking ɗin motocin suka yi da sauri ɗayar motar suka buɗe suka fito kana suka zo wajan ɗayar motar suka buɗe marfin , sai da akayi wasu ƴan seconds sannan ma mallakin motar yafito, shiba dajjijo ba, kuma shi ba yaro ba, a hankali ya fara taka ƙafarsa har ya ƙarasa cikin office ɗin principal, da sallama ya shiga, aikuwa principal ɗin yana ganin sa ya miƙe tsaye haɗi da miƙa masa hannu domin suyi musabaha cikin rawar jiki yace,

"ƴalleɓai kaine ke tafe yanzu da yamman nan?".
Ya faɗi haka fuskarsa ɗauke da murmushi.

Kujera ya nuna masa yace, "ƴalleɓai kazauna".

Ba musu ya zauna kan kujerar da ya nuna masa sannan ya sa hannu cikin aljihun sa ya ɗauko bundle ɗin ƴan dubu-dubu sababbi ya ɗaura saman  table ɗin da yake zaune, sannan ya buɗe baki yace,

"idan tana kusa a kiramin ita sabida sauri nake akwai musu jira na".

Tunkan wannan Alhaji ya rufe bakinsa sai principal yayi saurin faɗin, "bari-bari a kirata mai girma senator".

Yay maganar cike da rawar jiki.

Kai ya jinjina masa alamar to.

Jikin na karkarwa ya tashi yasa wani Malami  ya nemo mishi ita, bayan yasa a nemo ta sannan ya umurci wannan Alhaji ko ince senator ya shiga wani ɗaki na musamman wanda aka tana da sabida manyan baƙi.

ƘAWAYE NE SANADIWhere stories live. Discover now