*°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*SHAFI NA 28-29📑*
*__________📖* ba ɓata lokaci likitoci suka karɓeta aka fara bata taimakon gaugawa, sosai suka sha wahala wajan shawo kan matsalar ta, kwanan su biyu asibita suka dawo gida, amma tunda suka dawo gida bata wani samu bacci ba sai yau da safe bayan antasheta taci abinci kuma tasha magani sai ta kwanta, aikuwa tunda ta kwanta bata sake farkowa ba, har akayi kiran sallah azahar, matar Babace dataga bacci yayi yawa dan haka tazo dan ta tasheta, sosai hankalinta ya tashi daganin halin da take ciki, dan haka cikin hanzari taje ɗakin Baba ta sanar dashi ahalin da ake ciki, bai tsaya ɓata lokaci ba ya ƙarasu ɗakin da take ciki, da sauri yaje gareta yana dubata, amma ina, dan ko alamun numfashi babu ajikinta, idon ta baba yarufe tare da karnta addu'a bayan ya kammala ya juya ya dube matarsa dake tsaye yace,
"Kinga Allah yayiwa Jamila rasuwa, duk sun tafi sun barni, Allah ya gafar tamusu kuma yasa haka shine yafimin alhairi, Allah ya yafemusu kuskurensu". ya kai ƙarshin zancin yana fitar da kwalla.
Da Ameen Mama ta ƙarɓa haɗi da shafe ƴar kwallar da tazubu mata.
Fita yayi waje kana yakira ɗansa Adam da su Awal da Jamil ya gayamusu halin da ake ciki, sosai hankalinsu ya tashi dajin wannan mutur ƴar uwarsu kuma mafi soyuwa agaresu, bayan sun shafe hawayensu da suka zuba a fuskarsu sannan suka fara kiran mutane da ƴan uwa suna gaya musu halin da ake ciki, cikin ƙanƙanin lokaci mutane suka haɗu, wasu sukace bazasu zoba, saboda arniyace, daƙar dai akasamu akayi mata wanka kana aka ɗauketa zuwa gidanta na gaskiya, sosai su Awal ke kuka har da shasheka, bayan adawo mutane sai ta'aziya sukewa Baba da su Adam, bayan angama kowa ya watse dan Baba yace basa zaman karɓar ta'aziya, sai dai kowa yayi ta'aziya ya tafiyarsa batare da ya zauna ba.
Bayan sati ɗaya da wannan rasuwar su Jamil aka kuma ruwa, dan cigaba da harka gabansa, kamar bashine ke kuka lokaci mutuwar ƴar uwarsa ba, sosai Baba yaji zafin haka, dan haka ya fara shirin zuwa garinsu gani gida ko zai samu sassaucin abinda ke damunsa, haka kuwa ta kasance dan har Adam da iyalanshi za'aje.
Bayan kwana biyu suka shirya suka tafi garinsu Baba wato nijar, sosai ƴan uwa da abuka arziki sukayi murnar ganinshi, bayan sun huta suka fara zuwa wajan dangi dan agaisa, wani koda suke zuwa su tambaya ace sun rasu, ita dai Mama mafiyawanci ƴan uwanta sun rasu sai da ƴaƴansu, dan haka Baba ya haɗa yaƴansa da dangin mahaifiyar su haɗi da shaidamusu mutuwar Mama, sosai sukaji zafi mutuwar tata, duk da dayawa daga cikinsu basu santa ba, saboda wasu koda tabar gari suna yara, wasu ko ba'a haifesu, haka da Baba da iyalinsa sukayi tashiga ƴan uwa suna sada zumunci har sukayi sati biyu sannan sukayi sallama da ƴan uwa akan bajimawa zasu sake dawowa, haka da suka koma gida ciki da alhinin ƴan uwansu.
Bayan kwana biyu da dawowar Baba daga garinsu, sosai abin su Jamil yayi sanyi, dan gabaki ɗaya sun aje duk wani abu wannda suke ganin zai ɓatawa mahaifinsu rai, ko abukan shashancinsu sun daina biya, yanzu har kasuwa wajan nema suke zuwa kuma idan dare yayi zasu shiga masallaci ayi karatu dasu, abin dai sai wanda yagani, dan yanzu Jamil da Awal sai godiyar Allah komai yana tafiya yadda akesu, kuma sosai baba yayi farincikin sauyawar da sukayi.
Bayan wani lokaci, abubuwa sun sauya komai ya sauya Baba na gani zaune cikin wani fantamemin falo shida wasu yara sai wasa suke yana kallonsu yana murmushi haɗi da shafe kwallar da tazubuma sa, yana cikin haka sai akayi sallama, amsawa yayi haɗi da saurin goge kwallar da tazubumasa sannan ya tada kansa dan yaga kowasuye, idonshine suka sauka kan yaransa, wato Adam da Jamil da Awal, kallo ɗaya zakayi musu kasan nera ta zauna kuma kowane yakoma cikakin namiji.
Murmushi yayi wanda ke bayanar da kyawonsa, kallon yaransa yayi wanɗa da suka saka kaya kala ɗaya ciki da annuri yace,
"Har kun dawo?".
Ya faɗi haka dauke da murmushi afuskarsa.
"Mun dawo Baba, sunci mu gaisheka, ga sako can sun ci akawomaka".
Adam na kai ƙarshi zanci yasake cewa haɗi da kai dubansa wajan da yara ke wasa yace,"Jamila jeki ki daukowa Baba sako wajan Inna kaka".
Wadda akakira da Jamila na kalla, sai naga wata matashiyar buduewa wadda bazata wuce shekar tareba, gabana ne ya faɗi lokaci dana kai idona akanta, dan gabaki ɗaya sak take da Jamila ta farko, tana fita yaran dake wasa tare suma suka bi bayanta, da kallo Baba yabi bayansu haɗi da murmushi.
Saida suka fita gabaki ɗaya, sannan Baba ya ɗago da kansa ya dubesu kana yace,
"Inaso na ƙara shaidamuku ko bayan bana raye kada kuyi wasa da zumunci, dan kunga rashin sada zumunci abinda yajimin ni daku, dan haka nake muku fatar alhairi, kuma da fatar zaku kasance masu sada zumunci".
"Insha Baba zamucigaba dayi".
Haka rauyuwarsu taciga da kasancewa cikin kwanciyar hankali, cikin ƙanƙanin lokaci arziki ya mamayesu kuma suna zaune da matansu lafiya shima baba yana zaune da matarsa lafiya......
_Anan nakawo ƙarshin wannan lattafe mai suna ƙawaye ne sanadi, ina bawa masoyan wannan littafin haƙuri abisa rashin jina dasukayi na ɗan lokaci, abinda nafaɗa dai-dai, Allah ya bamu lada, kuskure Allah yayafe muna, sai mun sake haɗuwa acikin ƙayataccin littafena nagaba mai suna *BARRISTER JA'AFAR*_
Ina muku fatan alhairi.
*©UMMU JA'AFAR•*