*°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 20📑*
*__________📖* Ba ɓata lokaci Jambe tabiyewa Ana, duk yadda takeso haka tayi da ita, har gari ya waye kana ta koma ma saukinta, cikin ƙanƙanin lokaci Shugaba Ana da ƴan ƙungiyarsu suka koyawa Jambe duk wata harka wadda suka san tana kawo kuɗi cikin ƙanƙanin lokaci Jambe tayi suna, kano kaduna abuja ba wanda bai san Jambe ba, sosai ta kawowa ƙungiyarsu cigaba, tana cikin haka ne ta haɗu da wani ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wato Alhaji Sadik galadima, mai kuɗi ne sosai, ɗan garin sokoto ne, yana da ƴaƴa da yawa maza da mata, matansa huɗu kuma kowace nada ƴaƴa sama da biyar, sosai yake kula da ƴaƴansa har suka kai lokacin aure, ya aurar da yawa daga cikin ƴaƴansa maza da mata, suma har sun kai da ƴaƴansu, yanzu haka bashi zuwa ko ina, sai dai yaransa sukawo masa kuɗi yayi duk lalurar da yake su komai yawanta, ana cikin haka ne Allah ya haɗashi da Jameela, tunda ya ɗura ido a kanta yaji duk duniya babu mace da yake so kamar ta, ba ɓata lokaci ya gabatar masa da kansa, wani kallo ta aikamasa, lokaci ɗaya ya gane mitake nufi, ba ɓata lokaci yayi mata kyautar wani dan ƙarerin gida a garinshi na sokoto, sosai taji daɗin kyautar gidan da ya bata musamman a cikin garinsu, ba ɓata lokaci ta gabatar masa da kanta da abubuwan da take so, tundaga wannan lokacin Alhaji Sadik yake bata kuɗi kuɗi bana wasa ba, danshi duk lokacin da zasu haɗu to ba abinda yake bata sai dollars , lokaci ɗaya Jameela ta canja tayi kyau sai take gani kamar tafi ƴan kungiyarsu, dan haka ta farayi musu rashin mutumci yadda take so, saboda taga tafi kowa sa'a a cikinsu, gabaki ɗaya ta tare gidan Alhaji sadik bata ma waiwayin ƴan kungiyarsu, dataga ma zasu riƙayi mata rashin mutumci ta tatara nata da nata ta koma garinsu na sokoto, gidan da Alhaji ya sayamata nan ta zauna, shima alhaji ya dawo nan da zama, ko abinci gidansa baya ci sai na Jameela gabaki ɗaya ya birkice komai sai Jameela, ƴaƴansa sunshiga tashin hankali sosai akan zamansa da Jamila dan da ace sun san yadda za'ayi da sun aura masa ita sun huta, dan ba yadda basuyi yarabu da itaba yace wallahi Allah kaɗai ya isa ya rabashi da Jameela, duk da shi yasan ya haife ta, ko yayi jika da ita, da suka ga haka suka shirya sukaje wajan Jamila suka faɗamata abinda ke tafi dasu, sai da ta gyara zama haɗi da turu ɗan kwalinta yayi gaba sannan tayi murmushi haɗi da kallonsu sama da ƙasa sannan tace,
"Koda narabu da maifinku shi bazai iya rabuwa dani ba, yanzu haka a takuri nake, ya hani zuwa ko ina sai inda yace naje dan haka karkuga laifina".
Ɗaya daga cikinsu ya dubeta kana yace,
"Kiyima Allah kirabu da maihifinmu, wallah duk abinda kikesu zanyi mikishi, zan sai miki gida wanda yafi wannan, zan baki kuɗi miliyan ɗari, muddin kika rabu da mahaifinmu".
Zama ta ƙayara gyarawa kana tace,
"Duk abinda zaku bani bazaku bani abinda nasamu ga mahaifinku ba, dan haka nake sun kuyi haƙuri ku bani lokaci kaɗan, wallah ko bayaso zan rabu dashi".
Bayan sun gama magana suka tafi haɗi da ajemata kuɗi masu yawan gaske.
Da dare bayan ta kammalawa Alhaji girki, wanka tayi haɗi da yin kwalliya mai ɗaukar hankali, riga da wando tasaka waɗan da suka matsemata jiki sosai, dan duk wani abu wanda ke jikinta ana gani, zaune take saman kujera mai zaman mutum ɗaya, shisha ta ɗauko ta fara zuƙa ahankali tana cikin haka sai taji parking ɗin motarsa, aji shishar tayi kana ta sanya ma jikinta wani turari mai ƙamshi, dai-dai lokacin da ya shigo cikin palon, jikinsa ta faɗa haɗi da kai bakinta ga nashi, da sauri ya kwaici sannan ya kalleta haɗi da ɗan ɓata rai yace,
"Bana hanaki shan wannan abu ba ?".
sai da tayi marmushi haɗi ƴar shagwaɓa kana tace,
"Kayi haƙuri zan daina, ai yanzu narage sha sosai".
"To Allah ya nunamin kin daina shan waɗannan kayan gabaki ɗaya".
"Ameen ya Allah".
Haka tace dashi a taƙaice.Bayan yayi wanka yaci abinci sunyi shiri bacci, suna kan gado kwance, ahankali ta ƙara shigewa jikknsa, bayan ta dai-dai ta muryarta kana tace,
"Alhaji na".
Na'am baby na".
Dan sosai yakeson ta kirasa da wannan sunan."Nasan bazaka jidaɗin abinda zance da kai ba, dan nasan yanzu ka daina sona".
Tafaɗi haka haɗi da sanya masa kukan shagwaɓa.jikinsa ya jawota yace,
"faɗamin mike damunki Baby na".
Cikinta ta shafa haɗi da yin murmushi kana tace,
"Ciki ne dani na tsawon wata uku".... tun bata kai ƙarshin zancin ba yace,
"What!!!
Yafaɗi haka tari da tashi zaune.
Haɗi fuska yayi kana yace,"Baby banason wasa, idan wasa kikemin ki gayamin".
wani kallo ta watsamasa wanda yasa lokaci ɗaya ya dai-dai ta na tsowarsa kana tace,
:Kodama nasan bani kakeso ba jikina kakiso kuma kasamu, amma wallahi wannan cikin da kake gani naka ne kai kaɗai, kuma wallahi inason abuna ba wanda zai zubarmin dashi".
Rarrashinta ya fara amma taƙi saurarinshi, daga baya ma ta sauka daga kan gadon ta bar ɗaki.
Bayan ta yabi amma tashiga wani ɗaki ta kulle, ba irin haƙurin da bai bataba amma taƙi saurarin sa har gari ya waye bai runtsaba, ƙarshi dai sukayi haƙuri ta reni cikin ta har ta haifo ɗanta namiji sak mahaifinsa, sosai ƴaƴansa da ƴan uwansa da danginsa suka shiga tashin hankali da jin wannan mummunan labari, inda ta raɗamasa sunan Alhaji Sadak, haka yaro yaci gaba da girma yaje wajan ƴan uwasa kuma yaje wajanta, a nacikin haka Alhaji ya kwanta ciyo, babu wani jimawa yace ga garinku, sosai Jameela tashiga tashin hankali lokaci da taji mutuwar Alhaji, bayan mutuwar Alhaji da wani lokaci kaɗan, sai ƴaƴan Alhaji suka ɗauke Sadak wanda suke kira Baffa, sosai Jamila tayi tashin hankali akan sai sun bata Baffa, amma ina... dan suna ɗaukarsa suka bar ƙasar dashi, dan lokacin da mahaifinsu zai rasuwa ya tabbatarmusu karsu bar Baffa hannun Jameela, dan haka yasa suka karɓeshi duk masifarta amma sukaƙi kulata, daga ƙarshe ta haƙura ta kyalesu tacigaba da harkar kasuwancin ta.
Bayan wani lokaci ranar da yamma tashirya taje wani fati tayi kyau abinta, tana cikin tafiya ta haɗu da ƙaninta Jamil, har ta wuceshi kuma tayi sauri ta juyo ta dawo gab dashi, sai da ta tabbatar dashine sannan tace,
"Jamil".
Da sauri yajuyu ciki da mamaki da alajabi yace,
'Aunty Jameela".
Ya faɗi haka da tsantsar farinciki.
Tambayar sa tayi gida da mutanin gida har ma da Yaya Aliyu, kuka ya sanya mata kana ya faɗa mata halin da ake ciki, sosai hankalinta ya tashi dan haka tace yazo sutafi can gida taga halin da ake ciki...
*#VOTE, COMMENT, SHERE*
*©UMMU JA'AFAR•*