22- 23

6 1 0
                                    

*°🔘°BARRISTER JAFAR°🔘°*   
             *1441H/2020M.*
      
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼*

*SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 22-23📑*

*__________📖*  Duk yadda sukayi da Awal yaƙi karɓa, dan haka suka kyaleshi suka cigaba da abinda sukeyi nashan kayansu na maye.

Suna cikin haka suka ji sallama waje, kafin su buɗa baki su karɓa sai ganin wasu mata guda biyu sun shigo gidan sai famar murmushi suke suna dubin wajan da Jamila take zaune, dubansu tayi tace,

"Kuzauna mana".
Tafaɗi haka tare da nuna musu wajan da take zaune itada ƙannenta.

Zama sukayi sannan ɗayar ta ɗau ƙwalba ɗaya ta kai bakinta, ɗayar naganin haka itama ta ɗau ɗaya ta kaibaki, sai da suka shanye kaf, sannan suka aje kwalabin hannunsu, murmushi Jamila tayi musu kana tace,

"Na ɗauka bazaku gane gidannan ba".

Sai ɗaya tace, "tunda kikeyimuna kwatance nagane, saboda bamu da  gidan iyayena bashi da nisa da naku".

"Kema nan unguwar gidan iyayenkisu ke?".
Cewar Jamila.

"Eh banisa danan".

Ɗayar tace "Jamila wannan fah?".
Tafaɗi haka tare da nuna Jamil.

Ƙanenane, miye hala Sadiya?".

"Bakomai Jamila naga yayi min kyau ne".

Tafaɗi haka tare da kashe ido ɗaya.

Dariya Jamila tayi kana tace,

"Gashi akulamin dashi".

Sai da Sadiya tayi murmushi tace,

"Bakida matsala tawajena".

tana gama faɗar haka ta ƙarasa jikin Jamil ta rungumeshi haɗi da kaimasa sunba abaki, janye ta yayi daga jikinsa kana yace tazo sushiga ɗaki, ba musu ta tashi suka shiga ɗaki.

Itama ɗaya taje wajan Awal suna fira, ita ko Jamila tacigaba da kwankwaɗar kayan mayen ta, itako Mama na gyafe sai wasa take da gashin kanta, suna cikin haka sai wayar Jamila tayi ƙara, ɗauka tayi haɗi da faɗi,

" kushigo ba matsala".

Ba a ɗau lokaci ba, sai ga wasu maza da mata sunshigo gidan sunfi su goma, saman tabarmar da take zaune suka zauna, wani wanda daka gani shine babbansu yazo ya zaune wajan da Jamila take haɗi da jawota jikinsa haɗi da kai bakinsa da nata, wani daga cikinsu ne da yalura da Mama dake zaune yayi sauri yace,

"Oga fah ga Mama nan zaune".
Tun oga baiyi magana ba, Jamila tace,

"Karkudamu da ita, kocigaba da harkar gabanku, batada hankali".

Ihu suka buga sannan suka cigaba da sharhuliyarsu.

Wanda ake kira oga ya ɗago da gansa cikin yanayin maye yace,

"Jamila inason zansha atayi".

Cikin magana irinta ƴan maye ta dube wajan da Mama ke Zaune tace,

"Mama ga kayan atayi ki shiga kicin keyimunashi yanzu".
ta kai ƙarshin zanci tare da bawa Mama ledar da kayan ke ciki.

Ita ko Mama ba musu ta ƙarɓa tashiga ta fara haɗamusu atayi.......


~Kuyi maneji da wannan rashin comment ɗinku ne yasa banajin ƙarfin typing.~



*VOTE, COMMENT, SHERE*






*©UMMU JA'AFAR•*

ƘAWAYE NE SANADIWhere stories live. Discover now