[8/19, 10:12 AM] Ummu Jaafar😍: *°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *7GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 17📑*
*__________📖* Koda ya ƙarasa wajan katifar ta, wayam yagani, fitowa yayi ya same Mama yace,
"Mama ina tunanin ta tashi, wataƙila ma tana maƙewayi".
Mama tace, "eh tunda baka ganta ba tana cikin".
Ɗakinsa ya koma, yabar mama tana ida saurin aikin da yarage mata, har Mama ta kammala aiki ita da Na'imat, amma Jamila bata bito ba, kuma Mama so take tafito tashiga wanka kafin mutane su fara zuwa, amma Jamila tayi zamanta makewayi, jira Mama tagaji dashi, kuma tayi magana amma bataji ankarɓa ba, dan haka kaitsaye ta tashiga toilet ɗin taga me ya tsada Jamila? Koda tashiga wayam ba kowa aciki, sai tace,
"Kenan tajima da fita, amma kuma tayimin shuru ba magana, kuma tana cikin ɗakinta?".
Ran Mama ne ya ɓace, dan haka da sauri tazo ɗakin Jamila daniyar tayi mata faɗa, koda ta ƙarasa ɗakin, shima wayam ba kowa aciki, duban ɗakin Mama ta farayi har wajan kayan Jamila, shima wayam ba komai sai wasu ƴan tsumma da basuda anfani a wanta, gaban Mamane yayi mummunar faɗuwa cikin sauri tafito ɗakin Jamila ta ƙarasa ɗakin Yaya Aliyu hankalinta amatuƙar tashe, ko sallama batayi masa ba, tashiga, zaune yake yana duba wasu takardu, sai ganintayayi tashigo ɗakin ciki da tashin hankali, irin yadda yaga Mama tashiga ɗakinsa yasan akwai matsala, ahankali yataso yazo gare ta haɗi da riƙa hannuta yace,
"Mama lafiya kowa?".
Kanta da yasara mata ta riƙe, sannan tace,
"Aliyu banga Jamila ba".
Yace, "bata ban ɗaki?".
"Bata gidannan gabaki ɗaya, ko kayanta babu, kila Jamila ta gudu Aliyu".
Ta faɗi haka lokacin da wani kuka baƙin ciki yazo mata."A'a Mama bata gudu ba, ta gudu taje ina? Ƙila tana gidansu Antonia, bari naje nadubuta".
Yana faɗar haka yafito daga cikin ɗakin jikinsa asanyaye.Na'ima yaƙira yace tazo sutafi takiramasa Jamila gidansu Sakina.
Koda sukatafi Na'imat taje ɗakin Antonia amma rufe yake da kwaɗo, dan haka ta je dakin Mamarsu, shima haka rufe yake, dan haka tazo ta shaidama Yayanta Aliyu cewa basa nan.
Tunani ya fara, to ina sukaje da sassafinnan?.
maidata yayi gidan yace,
"Jeki tambayarmin ina suka je?".
Koda taje ta tambaye mutanin gidan, sai akace sun je garinsu wajan bikin mutuwa, haka tazo tagayawa Yaya Aliyu, sosai jikinsa yayi sanyi da jin wannan maganar, jiki ba kwari yaje hannun Na'imat suka dawo gida.
Koda suka shiga Mama da Baba suka gani tsaye sunyi shuru kamar masu tunanin wani abu, suna ganin Aliyu suka ce,
"Tana can ko?".
Jikinsa a sanyaye yace, "wallahi muje akace bata can, su Antonia ma sunje garinsu wajan bikin mutuwa".
Mama dake tsaye zama tayi sannan tace,