2

13 0 0
                                    

[7/16, 7:43 AM] Ummu Jafar 😍😘: *°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
             *1441H/2020M.*
          *SHAWWAL/JUNE.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼*


*SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*


*SHAFI NA 3📑*

*__________📖*  Har Jamila tabuɗa baki zatayi magana sai wayar Antonia ta fara rura, ɗaukar wayar tayi dan taga mai kiran ta, aikuwa tana ganin sunan da ya bayana saman screen ɗinta, lokaci ɗaya ta sanya wani ƙayataccin murmushi sannan ta ɗauka haɗi da karawa a kunnnita tana faɗin, "raka shi dade babban senator".
Tafaɗi haka amma daji kasan hausa bata zauna abakinta ba, saɓanin ƴan uwata da idan sukayi hausa zakace su asalin hausawa ne.

Banji miya yace  ba, amma naji tace, "tau sai kazo muna jiranka".
Tana faɗar haka ta datse kiran haɗi da tashi tana taka rawa har da waƙar jin daɗi, suma ƴan uwanta tunda sukaji tayi waya da senator  sunsan yau jikarsu zatayi nauyi, dan haka suma suka tashi suna rauwa haɗi da ƴar waƙa.

Jamila dake zaune tana kallonsu abin har dariya yabata sosai.

Sai da sukayi rawarsu sosai, sannan sukace Jamila tashiga toilet tayi wanka, bayan tayi wanka suma suka shiga sukayi nasu wanka sannan suka ɗauko mata wasu English wears tasaka, sosai sukayi mata kyau, dan idan ka kaleta zaka ɗauka tafitone daga jinin india, musamman yanayi jikinta, Jamila mai kyauce tawuce duk yadda za'a bada labarinta.

Bayan sun kamla shirinsu ba jimawa aka fara yin horn, da sauri Antonia ta tashi ta ƙarasa bakin gate ɗin gida, dan taga ko waye.

Aikuwa tun bata ƙarasa  gate ɗinba taga wasu rantsatson mutuci masu ɗaukar hankali, aikuwa tana ganinsu ta sanya wani ƙayataccin murmushi haɗi da ƙara sauri dan ta isa garesu, dai-dai wata mota wadda tafi sauran kyau da tsada ta tsaya, dan tana tunani yana ciki sabida baƙin glass ne ba'a gani sai wanda keci, hannu ta ɗauka daniyar tayi masa knocking, amma kafin hannuta ya kai ga glass ɗin har anbuɗe motar, ummarni ya ba driver yace ace tashigo cikin motar, ba musu ko ya zartar da abinda yace musu, ya bata dama tashigo cikin motar,sai da ta zauna sannan ta dubeshi tace,

"Ranka shi daɗi, da fatar ka ƙaraso lafiya?".

"Lafiya ƙalau". yace da ita.

Kafin ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri tace, "raka shi daɗe muƙarasa daga ciki ".
Ta faɗi haka ɗauke da murmushi a fuskarta.

"A'a Antonia bazan shigaba, kawa kibani ita zuwa yamma zan maidomiki ita".

Tun kafin ya rufe baki tace, "ba komai rankashi dade".
Tana faɗar haka ta buɗe marfin motar tafi.

Bawani ɓata lokaci sai gashi sun zo ita da sauran ƴan uwata da kuma Jamila.

Dai-dai motar da yake suka tsaya sannan Antonia ta buɗe motar haɗi da cewa,

"Rankashi dade gata sai kun dawo".

Tana faɗar haka ta jawo hannu Jamila ta sanya ta cikin motar sannan ta rufe haɗi daga musu hannu sai sun dawo.

Jamila na shiga driver yaja motar suka tafi, basu tsa ko ina ba sai Guest house ɗinshi, dukkan motocin sukayi parking, da sauri driver ya fito yazo ya buɗe mishi marfin motar,  sai da aka ɗau lokaci sannan ya fito, hannushi ɗaya riƙi da ƙugu Jamila suna tafi har suka ƙarasa wani fantamemin falo,  ahankali suke tafi har suka shiga cikin ɗaki, wanda yake ɗauke da gado da wadorf mai matsanancin kyau da tsada, daganin waɗannan kayan kasan nira tayi kuka anan.

ƘAWAYE NE SANADIWhere stories live. Discover now