Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹STORY&WRITING
BYAISHA ABUBAKAR
MRS BBBISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
YAH ALLAH INAMAI GODIYA AGAREKA DA KA ARAMAN RANA IRIN WANNAN NASAKE DAWOMA MASOYANA CIKIN WANNAN LABARIN MAI CIKE DA ABUN MAMAKI YA ALLAH KABANI IKON GAMASHI LAPIA TAREDA ISAR DA WANNAN SAKO DA LABARIN YAKE DAUKEDASHI.JINJINA GAREKI SHUGABA KUMA MAIFADA AJI GA WANNAN KUNGIYA TA KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION WATAU ANTY FAUZA YAR AMANA UBANGIJI YAKARA DAUKAKAKI YAKARAMAKI LAPIA TAREDA ARZIKI MAI ALBARKA.
JINJINA GAREKI NANA AISHA AKULLUM BAZAN IYA MANTAWA DAKEBA KINMAN HALLACI INA ROKON ALLAH YABIYAMAKI BUKATUNKI NA ALKAIRI ALLAH YABAR KAUNA MARAR IYAKA.
INASONKU YAN UWANA IRINSU....
MAMAN IMAN
MARYAM ABUBAKAR
ASMA,U ABUBAKAR
NABILA NASEER
NURATU NASSER
NAJA,ATU NASEER
NAFISA NASEER
HADIZA SHEHU
HAUWAH DA
SAINA,U
BILKISU DAN OGA
UMMI DAN OGA.
DASAURAN YAN UWANA ALLAH YABAR ZUMUNCI AMEEN.MASOYANA HAKIKA KUNA MATUKAR BURGENI INA ALFAHARI DAKU AKODAYAUSHE DA WADANDA NASANI DAWADANDA BANSANIBA ALLAH YABIYAKU YASAKAMAKU DA MAFIFICIN ALKAIRINSA.
INA KIKE BESTY HAJARA IBRAHIM DALHAT ALLAH YABARMUNKE INASHA SHA,ANINA HAKIKA INA JIDAKE IRIN DAYAWAN NAN.
🌈 *KAINUWA WRITERS ✍🏻 ASSOCIATION*🤝🏻
{'''United we stand and succed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers'''}
http://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
🅿1⃣
Wani garine dakecikin birnin kaduna maisuna hunkuy
Allah yayiwa wannan gari albarkar noma da yalwar ni,ima do min babu abunda basa nomawa kamadaga noman rani zuwa na damuna,
danyun kayan miya fruit dadai sauransu gasunan kamar banza kodayaushe garin alinke yake cikin iska mai dadin Shaka,Wanigidane mai rangwamen gata don yafita daban dagacikin unguwar Amma duk dahaka Allah yahorema mai gidan wadatar zuci,
Abunda Allah yabashi dashi yake anfani domin baisama zuciyarsa sai yayi abunda yafi karfinsaba,
Don yanaganin cewa Allahn dayaba sauran mutane shima yana sane dashi bamantawa yayi dashiba,
akullum abunda yake gayama mahaifiyarsa kenan
Amma bata ganewa don tasakama kanta son kudi sosai batada wani buri arayuwarta illa ace danta yayi kudi yaginamata katon gida yasamata yan aiki tana azabtar dasu da aiki,Amma har yanzu bataga wata alama ba dazata nunamata zaiyyi kudi haryanzu,
Gashi subiyu kadai Allah yabata kuma duk maza sai diyar wanta datake riko tunda yarasu shekara goma kenan,
Nasiru da nazifi sune kadai ta haifa nasirun ne kadai ttakedanjin dadinsa shiko nazifi ai bama acewa komi don yazama dangiya fitik,
Daneman Mata abudai sai duai.Nasiru yayi aure kusan shekara bakwai kenan ya auri wata bafulatanar yola
Kunsan fulanin yola akwai tsananin kyau abun bama sai nafadaba,
Ya auro tane lokacin babansa nadarai sunje wajen kakansa suka hadu basu baro garinba saida akadaura masa aure da ita.Yakawota nan gidansu don bashida wajen ajeta dayawuce nan din don lokacin bashida wata Sana,a
Sai bayan rasuwar babansu daya samu gadon gonarsa,
Yake noman rani idan damuna tazo itama yayi,
Cikin ikon Allah yakesamun rufin asirin Allah suci susha sukuma yi sitra,Duk wannan zaman dasuke inna batason matar nasiru
Falmata kokadan tadoramata karan tsana babu gaira babu dalili shiyasa falmata keshan wuyar zaman gidan,
Ga gorin haihuwa dasukemata itada diyar datake riko shamsiyya Amma sham akecemata,Yanzu haka shekaransu shidda Amma ko batan wata bata Tabayiba,
Itakanta tana cikin damuwar hakan Amma yata iya tunda bazata iyaba kantaba sai Allah yabata,Sham.yarinyace marar jin magana kokadan inna
ta dauremata gindi tanayin duk abunda tagadama,
Samari layi layi kuma babu mai zuwa da kafarsa saidai mota,
Club take zuwa har cikin garin Kaduna duk ranar asabar da lahadi,
Inna nagani tana wandaka da kudi Amma takasa tanbayarta ina take samu kuma tahana nasiru yadauki mataki akanhaka don acewarta zai takura rayuwarta ne yabarta taci kuruciyarta,
Dole yasakamata ido yadaina kallon duk abunda takeyi,Yauma kamar kullum inna nazaune bisa tabarma bakin dakinta tanajin radio,
Sai zagin yan siyasa take na kwashe masu karama,
Falmata tafito tanata shirin yin tuwan dare don biyar taiyi, daker tasamu tafito daga dakin don baccin bayan sallar la,asar yakamata gashi kwanan nan kasala take fama da ita gashi taita tara yawu gabakinta gashi tanajin bakin babu dadi,
Wuta tahau hurawa tasamu takama tadora tukunya,
Tadauko tankade tafarayi
Batadaice ma inna komiba
Don kadan takejira tahauta da masifa dukdanginsu saita zagesu tas,Hakadai falmata tasamu tagama tuwo tanaji inna nacewa wani dantakarar gwamnah akaduna,
"Shege mai nasama yaci balle yaba nakasa,
Kaima bakaci kakoshiba balle ka kosardamu,tunda harkagama mulkin bazakabi mu da miliyoyiba,"tsotsai yasaka falmata yin Yar dariya kadan
Amma dayake inna jiranta take saitahau ta da balbalin masifa,
"Dan kundun ubanki mekikewa dariya ehy shegiya juya sai aukin kashi amasai babu abunda kikeyi,
To kisake kikara shiga shirgina kigani banza kawai,
Zaki daina tsayuwa anan kisaina tsinemaki albarka,"Taja jikinta tacigaba da aikinta yayinda zagin da inna ke danna Mata yaketa cin zuciyarta,
Don hakika tana bakincikin irin zagin wulakancin datakemata yana sakata bakinciki Amma bakomi watarana sai labari.Haka tagama wannan tuwo cikin rashin kwarin jiki don har wata juwa take gani tasamu tagama kwashewa takaiwa su inna kitchen takai nasu daki,
Tayi alwallar mangaruba tashige daki dondama idan tashige bata sake fitowa sai safe,
Nasiru bai dawoba sai kisan goma,
Yashiga suka gaisa da inna
Take cemai matarsa tarenata har tana gayamata magana to yajamata kunne don ba ayenta bane watarana yadawo yatadda tamata mugun bugu,murmushi yayi don jin abunda tace itada tsufa yakama ko ina ita ina iya dukan falmata,
"Kiyi hakuri inna zanja Mata kunne babu ruwanta da ke insha Allahu""Dadai yafi tashi kaban waje
Ni"Yamike yafito ya na bakincikin halin innartasu
Kokadan batada hakuri
Yanada tabbacin falmata bazatai abunda tace tamataba,Sadda yashiga kwance yaganta talullube dabargo agado,
Abunda baisaba ganiba don kullum yadawo zaisamutana
Zaune tana jiransa suci abinci,
Zama yai kusada ita yadan bubbugi kafarta tatashi cikin hanzari,"Maigida kadawo wallahi daga gama salla naji bacciyaci karfina shine nadan kwanta sannu da zuwa ya kasuwar"
"Lapia lau alhamdulilah
Amma sainake ganin kamar bakijin dadi kwanan nan
Gayaman meke damunki"Kanta nakasa tagayamai duk yadda takeji
"Shikenan sauko muci abincin dasafe saikuje asibiti kila masassarace sai abaki magani"
Tare sukaci suka koshi
Anan yake tanbayarta meyahadasu da inna tayi yake tace wallahi tsotsai yasa nadan bigeta banganiba shine taketa fada"Murmushi yayi kawai don yasan tadorama kanta laipine kawai Amma badan tayidinba,
Hakika samun Mata mai hakurin falmata sai antona macece mai kawaici da dauke Kai ga abu tanada tsananin hakuri ko anzalinceta bata Iya ramawa zatai hakuri komi yawuce,MUHADU NEXT PAGE
INASONKU MASOYANA😘
TAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSIN.
YOU ARE READING
SAFAH DA MARWAH
FanfictionJan biyune su suna tsananin kama da juna amman kowace halinta yasha banban da na yar uwarta,kaddarar su ce soyayyar SAMEER