Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹STORY&WRITING
BYAISHA ABUBAKAR
(MRS BB)*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
🅿 5⃣
Watan cikin falmata tara har yazarce goma babu haihuwa babu dalilinta
Duk sunshiga damuwa itada nasirun gashi cikin yayi wani irin girma naban mamaki,
Duk yakunburata yamunana Mata jiki,Haka yaitasamo Mata maganin gargajiya don kozata samu tahaihu Amma Shir u kakeji kamar anshuka dusa,
Saida cikin falmata yacika shekara guda gam,
Sannan tawayi gari cikin tsananin ciwo tun tana iya jurewa har ta kasa haka taita
Fama har nasiru yadawo,
Yasameta cikin tsananin ciwo
Yafirgice yafita natsuwarta
Yaje yanemo mota aka dauketa Sukai asibiti,
Tun nasiru naganin a bun dasauki har yazo yafi karfin tunaninsa,
Don saida falmata tayi kwana uku tana nakuda Amma bata haihuba a bun yabaci sosai shiyasa aka yanke shawarar yimata aiki
Haka nasiru yashiga yafita yasamo dubu ashirin din da za aimata aikin,Anshiga da ita dakin theater kenan tafara wani irin nishi
Tana kankame gadon datake
Kafin wani lokaci,
Saiga jaririya tafado nan danan nurses suka tareta,
Sukashiga gyarasu
Bayan wasu yan minty na kadan tafara wani irin nishin mai mugun karfi saida suka rirriketa sannan tasamu wata Yar tasake fadowa,
Nan suka shiga gyarasu suna Mata murnan haihuwa da kanta,
Likitan yashiga dubata yaga tasamu Kari akaimata dinki tareda yimata allurai nan danan tashiga yin baccin wahala,Sadda aka kaiwa nasiru yaran durkushewa kasa yayi yana kuka,
Yana kuma dariya don duk ya rude samun yara biyu lokaci guda bakaramun baiwa bace Allah yaimaka,
Haka yarungumesu yanajin duminsu yashiga dakin da aka Kai falmata,"Kinbiyani falmata kingama biyana Allah yayiwa rayuwarki albarka allah ya rayamana wadannan yara masu albarka, Allah ya albarkaci rayuwarsu Allah nagodema Allah kakarma annabinmu salati"
Haka nasiru yaita sabbatu, daker yaje yatahoda inna
Badan tasoba yajawota
Amma ganin yaran saita hau dariya tana farinciki yau ce rana guda da inna tayiwa falmata magana cikin dadin rai da fara,a"Sannu yarnan Allah yabiyaki Allah yabaku lapia keda yaranki gaskiya kinwake zuciyata tas Allah rayasu cikin sunna"
Kwanan su uku akasallamesu sukadawo gida inna sai nan nan take da wadannan yara inn kemasu wanka kuma take yima falmata kasancewar haihuwar fari,
Ranar suna yaran sukaci sunan *SAFAH DA MARWAH*
A bun mamaki da farinciki ranar sunan nasiru yasamu
Aiki aikinma bakaramiba wani company dake garin abuja suka daukeshi aiki,
Matsayin shugaban company nin,
Farinciki yasaka inna taka rawa don wannan abun farincikine,Falmata tatafi wanka yola
Shikuma nasiru yafara shirin komawa abuja da zama,
Don sunce basai yakwso wasu kayaba,
Sunbashi gida kato da mota harda masu aiki da driver damasu gadi,
Wannan a bun yasaka sham.
Cikin farinciki don dama tasamu awajenta yanzune zata amunce da aurensa,
Tayadda zata rama irin cin kashin da yamata,Falmata dagacen zaije yadawo da ita sadda inna taga wannan gidan da abubuwan dake ciki murna take kamar me don tamafi nasirun yin Murnar,
Ranar ne yaje yataho da falmata da yaransa sunyi bul bul gwanin sha,awa bazakace sunyi wata ukuba zaka dauka sunkai wata shidda,
Rayuwar da suka canza mai cike da farinciki ce komi awadace yake idan kaga inna da su Safah saika dauka komi bai taba faruwaba,
Sonsu take kamar kamar me
Batason su matsa ko can dacen,Watarana nasiru yadawo
Daga office sai yasamu wani yaro bakin get dinsa kwance
Kamar babu numfashi ajikinsa driver yacewa,"Kamalu maza daukoshi muje asibiti Inaga baida lpy
Don naga bayanumfashi"Sadda sukaje asibiti akadubashi likita yace ulcer ce tayi mugun kamashi
Amma za,abashi magani
Zaisamu sauki
Aka rubuto magungunan sukataho,
Nasiru yake tanbayarsa inane gidansu"Yace banida gida nima natashi naganni hannun wata Mata wadda kullum take sakani bara ina kawo Mata kudi,
Nibanida kowa sai ita kuma kullum saita dakeni indai bansamomata kudiba kuma idan nasamu bata bani abinci,"Hakika yaba nasiru tausayi
Don haka yayi alkawarin rikesa amana matsayin danshi don da nakowaneKoda yakawo ma falmata shi tana farinciki tana murna ta ansheta tashiga rikonsa kamar yadda take rikon su Safah,
Haka yaron nan *SAMEER*
Yacigaba dazama wajen falmata tana kula dashi sosai inna ma bata wani damuba da kawo shigidan,
Tunda yazo jininsa yahadu da na Safah shiyake renonta kodayaushe indai tabaro wajen inna to tana wajen sameer indai yana nan,
Don nasiru ya sakashi makaranta yana primary 2
Kuma akai Sa,a yana da kokari sosai don har mamakin falmata keyi idan taji yana karatu,Sham.ba,abar hhaliba saidai yanzu tabar binmaza sai Mata,
Haka zakaga Mata kodayaishe suna zarya abangarenta,manyan Mata da matasa harma da wadanda basu gama zama maturity ba,
Duk abunda takeyi nasiru yasani yayi banza da ita yasan akwai ranar da duniya zatai Mata hankali,ZANSO GANIN WANNAN RANA KUMA MASU KARATU KUMA NASAN ZAKUSO KUGA WANNAN RANA
KUCIGABA DABINA ZA,AZO WAJENTAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSIN
YOU ARE READING
SAFAH DA MARWAH
FanfictionJan biyune su suna tsananin kama da juna amman kowace halinta yasha banban da na yar uwarta,kaddarar su ce soyayyar SAMEER