Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹*DAGA ALKALAMIN*✍🏻
👇🏻*Aisha Abubakar*
*(Mrs Bb)**_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Bismillahir Rahmanir Rahim.
🅿 9⃣
Karfe takwas nadare Abbansu yadawo daga tafiyar dayai zuwa wani meeting dasukayi Lego's da manyan yan kasuwa masu irin kasuwancin Sa.
Sham.ce cikin bedroom dinsa tagama hadamasa ruwan wanka tasaka maganin da boka yabata
Tayi dariyar keta tace,
" duk Wanda yaci tuwo Dani miya yasha Nasiru hakika da bakashiga rayuwataba babu ruwan biri da kada, Amma bazan taba yafe irin dukan wulakancin dakamun ba bana barin bashi kona na kwana dayane,
Zakagaya masu wallahi duk saina raba kan yayanka sannan indawo inrabaka dasu, wannan shine Burina""Wai sweety har yanzu bakigama bane"
"Nagama honey shigo kawai zantayaka ne kobakaso"
Yayi murmushi"ni na isa ince haka Ganinan zuwa bari in cire kayan"
Saida taga yayi wanka da ruwan sannan tasamu natsuwa don kallamu yace duk sadda akasamu wani kuskure guda taufah tatace zata kare,
Shiyasa takeyin taka tsan tsan daduk wani magani dazatai anfani dashi,Tatayashi shiryawa sukafito falonsa inda zaici abinci
Nanma cikin abincin wani bala,in ne tasaka, don maganin cikin shekara hudu akeson yayita cinsa yana wanka dashi,
Yanzu anyi guda saura uku
Idan akasamu fashin kwana daya cikin shekarar nan tofah abunda akesoba zaitaba yiwuwaba.Saida yaci yakoshi sannan tace honey"baka tanbayi yarankaba yakamata Kugaisa ko,"
"Nama manta dasu saidakika tunaman bari Nakirasu dakaina"
Yadauki waya yasoma kiran
Seenah tanaganin kiran tayi zunbur tatashi yaukuma Abba kekirana tadauka,
"Abba Kaine kuwa kana lapia yaushe rabonka dakirana kofa ganinka nabaryi""Kitattaroman kanku kuzo falona ina jiranku kibiya kikiraman Sameer"
"To Abba gamunan zuwa yanzu kuwa"
"Anty marwah kinsame wallahi Abba nanan Ashe,
Sai muyi kwana da kwanakin bamuhadu dashiba sai yanzu yace inkiraku muduka muje""Zunbur ta mike tace dagaske kike seenah"
"Wallahiko bari naje nakira
Anty SAFAH kekuma Anty kikira yaya sameer"Duk suka fito marwah tanufi
Bangarensa cike da damuwar halin dayake ciki,
Hakika SAFAH tacuceta datasaka Mata ruhinta Rabin ranta cikin damuwa dolene ma nadauki mataki kanki.Suduka sun hallara gabansa
Bayan kowa yagaidashi,
Yaita kallonsu yanajin wata mahaukaciyar soyayyarsu acikin jikinsa,
Amma yadanne yace
"FATAN KARATU YAYI KYAU KO SAFAH""EHY Abba karatu Alhamdulillahi ansamu abunda akeso insha Allahu"
"DAKYAU HAKA NAKESONJI
KEFA MARWAH""NIma haka Abba sai godiyar Allah"
Duk yatanbayi sauran suma suka amsa masa yadda sauran suka amsa,
"SAMEER YAKAMATA KAFARA AIKI ZUWA YANZU DON ZAMA BAI KAMAKA BA
KANA MATASHI MEKAKESON YI""Abba duk abunda kazabaman zanyi murna da farinciki dashi"
"Nafison kazabi abunda kakeso kokafison kasuwanci irin nawa koko aikin gwamnati kakeso kayi"
Yasunkuyar dakai yace
"Abba inso samune nafison aikin gwamnatin saboda halin rayuwa""Hakane karkadamu Zan San yadda akai,kefah SAFAH aure zanmaki ko zakiyi aiki"
"Sham ce ta zaraf tace wane irin aure yanzu Alh aitasamu ta anfana da karatunko kafin Allah yafiddo Mata mijin"
"Eh Abba nidai zanfara aikin idan dahalima kaginaman asibiti na nakaina wallahi yadda zanzamo Babu mai iko Dani kasan banson ace wani ne ke mulkani wallahi"
Dariya yayi yasaci kallon sham.
Yadauke Kai yace"indai Dan wannan anyi angama SAFAH""Marwah fah mekikeso kiyi Aure ko aiki zakifara"
"Abba bani da zabi kayi duk yadda kaso Dani kaike da iko Dani Banida zabin dayawuce naka duk Wanda kazabaman zankarba hannu biyu"
Hakika yaji dadin kalaminta
Yarinyar tanada BIYAYYA duk abunda kasakata babu makawa zatayi,
Yace"shikenan marwah zanyi tunanin Abunda yadace da rayuwarki karkidamu"Akwai mai bukatar kudi ko wani abu,SAFAH tai saurin cewa"eh Abba inason shiga super market zansiyo kayan shafah da riguna da takalma"
"Ai nasan kezaki riga kowa
Magana sarkin kwalliya
Kuma duk da kwalliyar har yanzu banga kowa yazuba"Duk Sukai Mata dariya banda sameer da marwah,
Yakallesu batare dasun saniba yakauda Kai yacigaba da tsokanar SAFAH,
Sannan yafiddo rafar yan dubu dubu guda uku,"Yace anshi nan SAMEER TUNDA KAI BABBANE KAYI HIDIMAR GABANKA"
YA ansa yana godiya maitarin yawa tareda yin addua mai dadi,
"Babu komi Kai Dana ne har abada duk abunda namaka banfadiba, karkajikomi kajiko Allah yaimaka Albarka""Yace Amen Abba"
Sham.abubuwan sunfara dauremata Kai,
To mehakan kenufi anyako maganin nan yana aiki uwani bata yaudareta ba wajen saka maganin kuwa,"Anshi nan SAFAH keda Yar uwarki kuraba asai kayan kwalliya ayitayi tayi dariya batareda godiyaba"
"Marwah tace Angode Abba
Ubangiji yakara budi na alkairi, yatsareka daduk sharrin masu sharri yakiyayeka daduk mai nufinka da shairri,
Sannan makiyanka aniyarsu takoma masu"Dabiyu duk tafadi haka tana satar kallon sham
Duk tadimauce tana zaro idanu, murmushi Abban yayi yana kallon sham.
Kafin yadauke idonsa yajawo su suduka ya rungume yana sakamasu albarka,Ai sham.jitai kamar ta kurma ihu mehakan kenufi yazama wajibi wannan kaunar tarabata dolene tashiga tsakanin su hakan bazai yuwuba,
Abba sai dariyar Sa yake dasu, yana satar kallonta,
Sameer dake gefe yamike zaifita yacemai"tsayamana kokai bakason albarkar"Yadawo kusada shi shima yarungumesa yana sakamasa albarka,
Sunjima suna hira dashi Wanda hakan yadade bai faruba,Mamaki tsoro fargaba da rudani sundabaibaye sham.
Duk tayi zufah daka kalleta kasan tana cikin rudani sai zufa take duk da uban sanyin da falon keyi,Sukaimasa bankwana saida safe sannan suka fito kowa da tanbaya cike da cikinsa
Amma bashida Wanda zaima ita.TIRKASHI WASA FARIN GIRKI YANZUMA AKAFARA
YAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSIN
ILOBE U FAN'S 🥰🥰🥰
YOU ARE READING
SAFAH DA MARWAH
FanfictionJan biyune su suna tsananin kama da juna amman kowace halinta yasha banban da na yar uwarta,kaddarar su ce soyayyar SAMEER