3.

8 0 0
                                    

Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
               🌹
          🌹🌹🌹
   🌹🌹🌹🌹🌹🌹
           🌹🌹🌹
                🌹

STORY&WRITING
         BY

AISHA ABUBAKAR
(MRS BB)

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻


'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

🅿 3⃣

Ko da daddare nasiru shiyafita yasiyo masu abunda zasuci don babu Wanda yadora tukunya
Waina yasiyo masu hada manshanu,
Sukaci sai tarai raiyar matarsa yake har Sukai bacci.

Washe gari yataimaka Mata tagasa jikinta,
Yadiramasu ruwan shayi ga risho saiyomasu kosai hada inna don yasan yanzu zata fara zaginsa meyamaida ta yafifita Matarsa akan ta.

Bai samu fitaba sai da yamma tayi sannan shima saida yaga bacci take saiyafita.
Inna tabishi dakallo tana harararsa,

"Zakazo kasameni Dan jakar uba kainan anwanke anbaka kasha har wani babare kakeyi zakaci kwal ubanka"

Dadaddare bayan sallar isha,I
Inna na zaune tsakar gida dayake babu NEPA kuma ga zafi anayi shiyasa take zaune tsakar gida,
Tanajiran dawowar nasiru don yau ko ita kosu shida sham.

Falmata nadaki duk da wannan zafin don indai inna natsakar gida bata fita don kiyaye abunda zai saka tayita zaginta don bakomi takejiba tazageta tas,

Sallama yayi yashigo hannunsa rike da Leda baka
Tunda yashigo takebinsa da kallo taga ina zai shige da ledar saikuma taga yaja burki gabanta,

"Inna sannu da hutawa"

"Yawwa kaikuma sannu da bita zaizai shanyayye anriga angama dakai andauraye anbaka kashanye shiyasa kaketa babaren takashi kana Mata bauta ga lamuden sakarkaru ta Haifama falmata da ko"

Shiru yayi don bashida bakin dazai cemata wani abu,
Baicebama tana rufesa da masifa balle yace,

Sham.ce Tafito taci uwar kwalliya tasaka wasu riga da siket tayi matsu matsu sai zuba kamshi take, ga ciwgom tana taunawa sai das das takeyi wayace faskekiya Take dannawa taraba inna zata wuce,


Duk binta dakallo Sukai
Don a bun nata yawuce misali yayin da nasiru yake Allah wadai da halayyarta,
Muryan inna taji takwala Mata Kira,

"Zonan shamsiyya yau saikin Gayaman gidan ubanda kikezuwa idan angama isha,I
Nagaji da ganin wannan salon karuwan cin naki"

Juyiwatayi batai musuba
Tadawo tatsaya bisa kan nasiru  tayimasa kerere,

"Cikin tsawa yace matsa daga saman kaina kafin inyi kwallo dake shashasha kawai"

Taja tsaki tana gunguni
Inna tabita da kallon mamaki don sham.tsoran nasiru takeyi matuka Amma yanzu kwata kwata bata shayin kowa ma agidan.

"Zauna magana zanyi daku
Mai muhimmanci"
"Inna kiyi hakuri gaskiya yanzu banida lokaci don anajirana yanzu haka"

"Au Dan ubanki nikeke gayawa bakida lokaci to lokacin wa gareki gayaman kafin nalakada maki shegen duka"

"Wai inna meyasa kike takura rayuwata ne wai eh
To saurayina ne Wanda Zan Aura yana wajefah"

"To to yanzu naji Bayani to Dan jira kadan muyi wata Magana saikitai yi hakuri kinji Shamsiyyar inna"

SAFAH DA MARWAHWhere stories live. Discover now