Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹STORY&WRITING
BYAISHA ABUBAKAR
(MRS BB)*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
🅿 4⃣
Tsawon wata guda kenan da yin barinta tafi fresh tayi lukui lukui da ita bata dauki damuwa tadorama kantaba
Don har yola taje tagaido iyayenta Sukai tasamata albarka tareda yimata adduoi masu yawa kwanan ta biyar tadawo,
Cike da kayan arziki don babanta har dinki yasa akaimata Kala biyu mamanta kuma tahadamata kayan yaji da turarukan
Hada su taliya akaba nasiru shadda yadi biyar,
Inna kuma akabata atanfa
Amma wannan baisa taragama falmata ba itace wankinta itace yin surfe idan za ai sanwar dare komai na wahalar cikin gida falmata itace keyi baiwar Allah bata taba gajiyawa donma jarumace,Yau juma,a gidan babu kowa inna taje gidan wata qawarta
Nan bayan layinsu sham.dama bakodayaushe take gidaba nasiru kuma yaje sallar juma,a
Falmata tagama duk aikin ta narana tashiga wanka kenan tacire kaya tafara watsa ruwa,
Kamar daga sama taga nazifi yafado Mata kewayen,Zabura tayi tajawo zanenta tadaura,
"Miye haka nazifi bakasan dakowa baneba kafita don Allah wanka fah nakeyi"
"Cikin muryansa tamaye yace dallah ware malama kebaki wayeba kibani in yi ingama kawai babu Wanda yaganmu"
"Zaro ido tayi tana anbatar sunan Allah cikin ranta,
Don girman Allah nazifi karufaman asiri wai Kai baka da hankali nacemaka wanka zanyi kafice kabani waje"Takowa yake zuwa inda take
Gabanta yashiga dukan Tara tara don tasan bakaramin Dan akuyabane yana iya keta Mata haddi acikin gidannan,
Gashi ba karfinsu dayaba
Tsoro take wani yyashigo yagansu kashinta yabushe wajen inna don bazata taba saurara mataba,Damkota yayi yana kokowar cire zanen,
Takibari yafara zabga Mata Mari ya na cewa."Tunda har miyauna yaguda to baki isaba agidannan ko gaban wannan banzan mijin naki saina ketaki nibaruwana gara kitsaya inbahakaba wallahi Zan sumar dake awajen nan,
Kuka falmata keyi ganin yanason yin nasara yakwance Mata Zane rokonsa take yakyaleta Amma yakiya don hankalinsa yagushe burinsa yasamu yabiya bukatarsa da ita,
Ganin datai idan ba ihu takurmaba naxifi tsaf zai keta Mata haddi inko haka tafaru tashiga uku tayaya nasiru zai yadda da ita idan yasan wannan a bun ko yayarda batada laipi inna bazata Bari yacigaba da zama da itaba wasu hawayen masu zafi suka shiga zarya ga fuskarta,
Cicin karfinta tatureshi yabugu da bango tajawo abayarta zata saka yasake damketa yawanketa da Mari yafara kokowa da ita,
Wani uban ihu takurma tana aceceta zai kasheta,
Tadunga kurma wannan ihu
Shikuma yasamu yakwance zanen takucce tafito dagudu,
Daidai nasiru yashigo dagudu shima ga mutanen unguwa duk sunshigo
Donjin irin ihun datakeyi yasakasu shigowa ganin meyafaru,Durkushewa tayi kasa tana kuka ga nazifi yafito kewaye rike da zanenta ga hannu,
yana raba idanu nanfa matasan dasuka shigo sukahau dukansa suna tsinemasa waje sukajashi
Suna shelar ga kwarto ankamashi zaima matar yayansa fyade,
Nanfa kamar sunga nama suka dunga bugunsa saida sukabarshi kwance,
Yakasa tashi sunmai jina jina,Karsawa yayi wajenta yadagota yarungume,
Shikansa kukan yakeyi yarsa mezai Cemata,
Don wannan bala,in ya isheshi cikin gidannan har ankai lokacin da kanensa zai nemi matarsa ta sunna wace masifa ce wannan tare suke kukan har inna tashigo tasamesu,Icce tasamo mazgege tanufosu dashi tana kuka tana cewa,
"Gara Inkasheku daku kusheman yara wallahi Dana rasasu gara Ku narasaku yan iska,"Tashi yayi yarike hannunta Wanda tadauko iccen,
Zata bugamasu ya anshe iccen yawurga gefe,"Wai wace irin uwace ke ehy
Kina nufin wannan abunda nazifi yayi kenan ba laipi bane yayi niyyar keta ma matata haddi shine kike goyon bayanshi har kina yinkurin kashemu saboda bakison gaskiya wace irin tsanace kikayiwa wannan baiwar Allah,meta tsaremaki miye laipinta don kawai tana aurena koko don ina nuna kulawa ga reta wanene ciki laipi kigaman inna""Taushikenan zamu tattara mubar maku gidan saiku zuba ruwa kasa kusha Amma bazan yi shiru kuna bakantamana ba babu laipin tsaye babu nazaune"
Yakama falmata daketa kuka suka wuce daki yaita lallashinta yanabata hakuri tareda Gayamata zasubar gidan dole don farincikinmu musamu natsuwa"
"Aa maigida karkayi haka idan mukatashi nan ina zamuje kuma wazai ringa yiwa inna sanwa wazai kula da ita kayi hakuri muzauna babu abunda zaisake faruwa insha Allahu allah zaicigaba da tsaremu daduk masu nufinmu da shairri"
Rungumeta yayi yana jin kaunarta nasake shiga zuciyarsa hawaye yakeyi Dan tausayinta duk wannan a bun da akaimata baisa taji zatabar inna ba wace irin ce falmata da bata yin fushi,
Nazifi ko saida sukaima karaya uku bacin raunikan daduk sukajimai ga jiki,
Yansanda sukazo sukatai dashi saida suka tsaya dashi asibiti don yasamu sauki na kwana ki kafin suwuce dashi caji office,Haka nazifi yasha bakar azaba kafin yace ga garinku nan,
Wannan mutuwa ta nazifi takara jefa tsantsar tsana tsakaninta da falmata,
Inna tayi kuka kamar babu gobe kudayaushe tana cewa falmata akashe Mata danta,Itadai batada abuncewa don yanzu duk sadda tafito indai tana tsakar gidan tofah falmata batada zaman lapia zagine zatai ta sha saidai tayi ta hakuri da ita,
Har akai arba,in dayin rasuwar Amma iinna kullum tsinema falmata take,
Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji,
Saidai falmata tawayi gari taga cikinta yayi tauri kuma yayi girma gabanta yafadi badai cikine da ita ba tsawon wannan lokacin bata saniba,
Aiko bazata bari inna taganshiba har sai ya girma,Tunda dama ba girman ciki garetaba bazaka gane cikinba da nasiru yadawo tacemasa yabata kudi zataje asibiti masassara take fama da ita"
Baiyi musuba yabata washe gari tagarzaya asibiti awon farko yanuna tanada ciki wata hudu,
Saboda farin ciki kuka takamayi haka tattaro tadawo gida tacigaba da hidimarta don wannan Karon babu wani laukayi datake fama dashi,Haka taita boy on cikin ko nasirun batagayama waba tabari yagani da idonsa,
Duk sadda tayi sallah tana adduar Allah yatsaremata cikinta yakuma rabasu lapia,
Ranar ko da nasiru yagane
Kuzo kuga murna da farinciki jiyake kamar ansakashi aljanna yadinga godema Mata yana sakamata albarka,Cikin yana wata shidda Amma yayi wani irin girma naban mamaki,
Inna nagani tahau fada wai anrenata ba,a gayamata ansamu ciki ba saida yafito hakadai takaraci korafinta gama,Don yanzu sham.saita kwana biyu bata gidan
Hakan baidamu inna ba tunda kullum tanabata kudi shiyasa takashe bakin maganar,KUYI HAKURI BABU YAWAH
MUHADU NEXT PAGE
TAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSIN
YOU ARE READING
SAFAH DA MARWAH
FanfictionJan biyune su suna tsananin kama da juna amman kowace halinta yasha banban da na yar uwarta,kaddarar su ce soyayyar SAMEER