Maman Muhseen: *SAFAH DA MARWAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹*DAGA ALKALAMIN*✍🏻
👇🏻*Aisha Abubakar*
*(Mrs Bb)**_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
Wannan page din kyauta ne gareki mami hakika kinamun yadda nakeso inajin dadin comment dinki akoda yaushe.
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
🅿 8⃣
Wani wajen shakatawa ne yatafi dasu
Sai Dan wane dawane yake zuwa wajen yayi kyau sosai wajen shan coffee ne,
Duk sunzauna saman plastic chairs"yace MARWAH kozakusha coffee ne""Ah nidai nakoshi saidai idan ko su SEENAH DA SAFAH",
KOWA yace bayada bukata don oganniya SAFAH batama cekomiba dama kuma baisa ran zata cewani abuba.
Gyara zama yayi yamaido attention dinsa wajen marwah, ai jitai kamar zata ruga don yatsareta da idonsa masu matukar rikita mutun koda baiyi komiba."Muna sauraronki marwah"
Tadan muskuta sannan tafara dacewa,
"Yah sameer hakika dawowarmu daga makaranta munshiga damuwa mai yawa tarashin mommy, tabbas dole akwai ayar Tanbaya cikin wannan Al,amarin,domin ko mommy baza tayi tafiya batare data gayamana ba kuma dole indai wani waje taje to Abba zaisani, Amma abun mamaki yace baima santaba
Saidai muyi hakuri to wane irin Al,amarine wannan yah Sameer, nidai Allah yasani wallahi banyarda da wannan matar ba yamatake dasuna sham.kowa oho Mata".Ajiyar zuciya yasauke sannan yace"wannan wani babban abune da yakamata ayi bincike kansa,kuma dole kuzaku yisa saboda matsalar daga cikin gidan take duk yanda akai takarfin tsiya akafitar da mommy daga cikin gidannan,
Babu kyau zargi Amma dolene azargeta saboda alokacin damuna nan babu wata kyakkyawar alaka mai kyau tsakaninta da mommy,
Sannan Rana tsaka mutadda mommy bata nan kunga dole akwai yadda akai"."Duba da yadda mommy da Abba suke sonjunan su bana tunanin akwai wani Abu da zatai masa har yakoreta, kokuma tabar gidan batare da yasaketa ba
Akwai saka hannun wani kuma babu tantama asiri akaimasu sudukan,
Sannan wani abun tanbayar Kai muhsin kaceman komi akan idonka yafaru Amma
Kace kamanta kanason fada Amma bazaka iyatunawaba"."SEENAH TACE Yah Sameer wallahi tabbas maganarka haka take gabanmu komi yafaru Amma wallahi duk sadda mukai yunkurin sanar dawani sai munemi Abun murasa, saida idan a bun yafadoman inshige daki iyita kuka banida yadda zanyi",
"Amma meyasa zaku zargi mami,bazata aikata hakaba
Mutuniyar kirkice kiduba fah Anty marwah yadda take tasonmu tana kula damu, tayaya Wanda yai wannan Abun zai mana Abunda takemana yanzu, inaga mubar zarginta bazatai hakaba".fada marwah take cewa
"Taya bazamu zargeta akan korar mana mahaifiyaba Seenah meyasa kuka dauki yarda ta lokaci guda kukabata, to inason sanar daku muddin zaku cigaba da yarda da ita wallahi saikunyi danasani bafata nakemakuba Amma satakaiku tabaro kudawo cikin hayyacinku, kunmance sadda take zagin mommy cingidannan take hadasu fada da inna kokunmance ne inyunamaku".SAMEER yadakatar da ita yadaga Mata hannun yace,
"Abun baikai nafadaba Marwah kibari abar abi abun ahankali, insha Allahu komi zaizama normal kukuma karku sakankance da ita sosai domin ance mugu baida Kama kukiyaye zanyi iyakar bincikena, kuma yazama wajibi kuyi""SAFAH tace shiyasa kiketa fushi Dani tunda kikatashi yau saboda wannan abun,
Danme bazamu sakijiki da itaba babu Wanda yasan gaibu sai Allah Amma bana tunanin zatai abun da zaicutar damu kima bar zarginta babu kyau.""Aidama haka kike kekowama abun yardarkine
Saidaga baya kizo kina nadama nahanaki wannan halin Amma saboda taurin kaidakike dashi bakijin shawarata sai abunda Kika tsarama kanki, Allah yabaki Sa,a gaki gatanan zakiyi danasani""Cikin tsawa itama tace kece zakiyi danasanin biyewa wannan abun tanuna sameer, bakida hurumin hanani alaka da matar ubana
Dama haka kike dashegen zargi kan Abunda bakiso to baki isa kihanani abunda nai niyyaba"."Danasan kan wannan abun zaku kara zaku tattauna dabanzoba"
"Yanzuma zaki iya tafiya bakida wani anfani awajen,
Gara kitafi din marar tunani Kawai.....................karar Mari kakeji SAFAH tadauke marwah da Mari"Gabadaya suduka saida abun yasakasu mikewa,
Yau SAFAH ce kemarin Yar uwarta marwah wannan wace irin ranace mai matukar muni SAFAH din da kowani tagani yana nunama marwah hannu saitakusa cinyesa da bala,I
Amma yau itace ke daga hannunta tadauketa da Mari mai matukar zafi irin wannan,Idonta cike da kwallah badan zafin marinba aa bakinciki ne yasakata subar dasu,
"Nizaki Mara akan wata banzar bazara akan maha inciyar cen shamsiyya saboda ita kike dagaman murya har kina marina,
Lallai kinkaraman haske akanta kuma bincike akan abunda ta aikata yanzu nakara samun kwarin guiwar yinsa, sai yanzu nakara tabbatar dacewa ke sakarar banzace kuma marar tunani
Nafada"........Sake daga hannu tayi zata mareta,
Sameer yarike hannun gam
Yawurga gefe yana kallonta,
"Yace tashi muje marwah kikyaleta zatayi danasani nan gaba"Cikin daga murya tace masa,
Bakada matsayin dazanyi magana dakai baka kai wannan matsayinba,
Kamar yadda nake Daukar su yawale mai gadi damasu wankin mota, damasu shara da morping haka nadukeka
Sameer kabar dauka Kai wanine bakowa bane face almajirin mahaifinmu,
Donhaka kabar hakikancewa bakada wani power acikin gidan nan wawa kawai"Baki bude suke kallonta cike da tsananin mamaki,
Seenah tace"Anty mekike fada kinkosan wakika gayama wannan maganar,
........."rufeman baki kafin nabata maki fuska nafiki sanin kowaye shi bakowabane face tsintacce Wanda bashida wani anfani awajena"Marwah tuni hawaye sunwanke Mata fuska saboda wannan cin fuskar datayimasa cikin mutane,
Kowa sai kallonsu yake
Ta isa wajenta tace"Saikinyi danasanin wadannan kalaman naki SAFAH wallahi saikin duka watarana kinbashi hakuri wannan alkawarina ne kuma saiyafaru ina sha Allahu,
Indai nice usaina zanmaki wannan matsayin gift din birthday dinmu"Tanagama fadamata wannan tabar wajen
Tasamesu mota sukabar wajen,
Babu mai iyacewa komi cikinsu daka kalli idonsa kasan ransa amatukar bace yake don sunyi matukar yin jawur kamar gauta,
Har suka koma gida babu Wanda kecikin walwala,Wannan Rana tsakanin SAFAH DA MARWAH
DA SAMEER babu Wanda yakasance cikin farinciki,
Kuka marwah keyi akan irin abunda SAFAH tayimasu,
Wai SAFAH ce zata daga hannunta mai albarka tamareta dashi tagaigaya Mata maganganu kamar batasantaba, gaban mutane
Lallai tadauko kano babu gammo,
Nayi maki alkawarin kasancewa cikin bakin ciki mai dorewa har sai sadda kika gane cewa shamsiyya ba masoyiyarki bace,
Ina nan zaki gane kurenki
Bantaba anfani da kwafina akan kowaba to zaifara akanki, bakuma Dan bansonkiba saidan kigane darasin rayuwa,TASHIN HANKALI ABUBUWA SUNTAHO KARA LALACEWA KUTAYASU ADDUA
TAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSIN
YOU ARE READING
SAFAH DA MARWAH
FanfictionJan biyune su suna tsananin kama da juna amman kowace halinta yasha banban da na yar uwarta,kaddarar su ce soyayyar SAMEER