SADAUKI RAZMIR 5↔10

42 4 0
                                    

🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵


Writing by

ALIYU H ISHAQ
   (fast class)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
     And now
          ↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)


🅿 5↔10




Dedicated to All my fans



DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI



..............Gudu wannan saurayin yake iya karfin sa iya kar iyawarsa dan ya tsere wa wadannan miyagun dakaru amma daya juyo bayan sa sai ya gansu daf dashi tamkar su mika hannu su damko shi amma ba damar hakan dan zullewa yakeyi tako ta ina





Koh da yaga wannan gudun bazai kai masa ba sai ya fara tunanin mafita sabida a koh da yaushe zai iya sarewa kuma ga wata yunwa dake nukurkusar cikin sa dan rabon sa da abinchi tun na jiya da safe da ya kwaci wata gurasa a hannun wani badakare ya gudu to shine wadannan dakaru suke ta binsa dan ganin sun kamashi su kai shi gurin sarkin su dan ya yanke masa hukunchi abisa laifin satar daya aikata da kuma dukan badakare





Yana cikin wannan gudun nehh ya tuna da jaririyar kanwarsa dake bayan sa ya Shafa yaji bata wani Motsi Alamar tana da rai nan take hankalin sa yayi masifar tashi ya juya yaga wadannan dakaru na Neman cim masa kawai sai ya dage ya kwala ihu dai dai karfin sa ya fita da wani mahaukacin gudu wanda bai taba yin kamarsa ba a rayuwarsa





Aiko kan kace wani Abu ya basu mahaukaciyar rata sai da ya zamana cewa basa Iya hango koh da kurar sa a cikin wannan Daji a wannan lokacin nehh ya hango wani kogon dutse mai matukar duhu duk yana ta rufe bakin sa





Ba tare da tsoron komai ba ya kuna kai cikin kogon sai da yayi tafiya Rabin sa a sannan ya isa karshen kogon




Yana isa ya zube sharaf a kasa sumamme ,





Suke wadannan dakaru koh da suka ga sun daina hango shi sai suka juya suka kada dawakan su suka koma da baya cikin matukar takaici dan wannan shine lokaci na farko da wani mahaluki ya taba sira daga sharrin su





Bayan wasu yan sa'o'i nehh wadannan dakaru suka isa cikin birnin Hindu fuskarsu ba Alamar annuri duk wanda yaga wadannan dakaru a wannan lokacin sai dai kaga ya dare ya basu hanya dan kowa tsoron su yake ji sakamakon dan ban zan zalincin su a cikin wannan birnin sarkin garin ya basu damar yin duk abinda suka ga dama acikin birnin sa sabida a kaf cikin dakarun birnin yafiji dasu har yana  musu lakabi da DAWAKAN AZABA,




Wadannan dakaru basu tsaya ako ina ba sai a gidan sarautar birnin tsayawa fadin yarda gidan sarautar ya tsaru ma bata lokacine fans ta tsaru matukar tsaruwa





Kai tsaye suka wuce cikin fadar SARKI DARRAJU IBN KULMAN dan dama basuda wani shamaki acikin wadannan gidan sarautar


Wata tamgamemiyar kofahh ta zallar zinare ita kanta kofar abar kallo ce kai tsaye suka kunna kai cikin fadar




Lokacin da nayi ido hudu da fadar sarki darraju saida hankalina ya kusa Barin jikina bansan sanda yawu ya rika diga daga bakina ba ba abinda ya bani mamaki sai yarda naga tsarin fadar yake gabaki daya ginin fadar anyi shi nehh da zallar zinare da yakuta da jauhari da sauransu girman fadar ya kai girman gari guda




Tako ina jama'a nehh makil an cika ana ta fadan ci daga chan nesa kadan na hango wasu tsala tsalan yan mata sun zage sai tikar rawa sukeyi gefe daya makada nehh da maroka suke ta aikin su na koda sarkin






Daga Chan sama na hango wata rangadediyar kujera ta zallar zinare a bisa wannan kujera SARKI DARRAJU nehh zaune ya hakin ce akan kujerar nan fuskarsa tamkar bai taba Dariya ba a duniya




Wai rigiji gabja din fah kenan shi kansa sarki Darraju abin kallo nehh sabida ya kasance tafkeke mai kirar mutanen farko yana kira irin ta manyan sadauki  kuma ya kasance jarumi mai tarwatsa maza a filin daga wata zabgegiyar takobi ce daure a kugun sa tana mai fitar da jan haske gabaya kaf jikin sa gurayen tsafin sa nehh,





Daga gefen daman wani dan saurayi nehh wanda shekarun sa bazasu Haura na wannan saurayin na Daji ba saurayin yana sanye da kaya na alfarma shima ya kasan ce ya tamke fuska nehh tamkar bai taba Dariya ba a duniya lalle kam kyan da ya gani uban sa YARIMA MANGUL kenan daga sarki Darraju sarki Darraju yana matukar ji da yarima mangul sakamakon bishin da yayi aduk wani bakin hali nasa kuma shima ya gani uban sa a sadaukan taka da karfin zalunchi




Daga bangaren hagun sa kuwa kyakykyawar yarinya ce yar kimanin shekara uku a duniya tana sanye da kaya irin na sarauta da alfarma ta kasance kyakykyawa ta gaban kwatance haka ba abinda ya rabasu da yarima mangul sakamakon tsananin kamar da suke da juna GIMBIYA LAMRITA kenan ibn DARRAJU




Wadannan sune yayan sarki Darraju wadannan yafi jii dasu aduk duniya amma yafi ji da yarima mangul sakamakon yana taimaka masa abisa harkallar da suke yi tare da dan nasa






Ba wata harkallah bace bace bataucin bayi da Kuma farautar bayin a kaf fadin duniya ba wanda baisan sarki Darraju ba haka kuma duk birnin da yaga dama zai shiga yaje ya yaki garin ya kashe kowa ya kwaso dukiya mai dunbin yawa






Hakan nehh yasa kowanne birni ke tsoron Kuma suke yi masa biyayya dan dole badan sunso haka duk shekara sai sun biya haraji idan ba haka ba kuwa yanxun nan zai yi hawa shi kadai ya zo ya rushed birnin gaba daya a duniya ba abinda sarki Darraju ya rasa amma duk da haka sai yayi wannan barnar yake jin dadi





Bayan haihuwar yarima mangul nehh sarki Darraju yayi matukar farin cikin da ganin sa dan yasan ya samu magaji haka kuwa akayi din dan duk wani hali na sarki Darraju saida yarima mangul ya dauko shi sai dai shi har ma ya fishi zalinci da cin zarafi idan ya fita farauta shi bayan ya rushed gari da komai idan macece sarauniyar a gaban jama'ar ta zai yi mata fyade ya kashe t idan namiji nehh muddin yanada ya mace to akan idanun sa zai keta mata haddi sannan ya kashe ta a gaban Babban ta sannan ya kashe uban NATA ya kwaso ganima





Wannan dabi'a ta da da uba tana damun mutanen birnin Hindu amma ba yarda zasu yi dasu dole su hkr dan koh suma basu tsallake tarkon yarima mangul ba muddin ya kyalla ido ya hango yarka to fahh a ranar saita mutu bayan gama biyan bukatar sa da ita .............





Wannan kenan gsky naji dadin son da kuka nunawa wannan book din nawa sannan naji dadin comments dinku Yan uwa da abokan arziki ALLAH yabar zumunchi ameen thumma ameen


Vote
Comments and shared



WhatsApp number 08143314152




By fast class

SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORYWhere stories live. Discover now