SADAUKI RAZMIR PAGE 25↔30

23 2 0
                                    

🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵

Writing by

ALIYU H ISHAQ
   (fast class)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
     And now
          ↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

IG, haidar_Ishaq_576

Email,  haidarishaq@gmail.com

WATTPAD, @FASTCLASS

Facebook, haidar ishaq



🅿 25↔30






...........Al amarin yarima mangul kuwa lokacin daya fita daga cikin turakar sa bai zame koh ina ba sai turakar mahaifinsa yana zuwa ya zube bisa guyoyinsa yana mai sunkuyar da kansa



Koh da sarki Darraju yaga yanayin da dan nasa ta shiga sai ya taso cikin sauri yana mai dafa kafadar sa yana fadin

Ya kai dan shin me yake faruwa da kai nehh waye ya taba ka


Ko da jin wannan tambaya sai yarima mangul ya dago rinannun idanun sa da suka kada sukayi jajur ya kallo sarki Darraju lokaci guda ya fashe da kuka yana mai fada wa jikin sarki


Cikin tashin hankali sarki Darraju ya fara girgiza shi yana mai tambayarsa abinda ya sameshi


Sai da ya yayi kukan sa mai Isar sa sannan ya dago jajayen idanun sa ya fuskan ci sarki Darraju ya zayyane masa duk abinda ya faru tsakanin sa shamril bai boye masa komai ba


Wata kururuwa sarki Darraju yayi lokaci guda kuma ya fashe da kuka chan kuma sai ya tsagaita kukan yana mai kallon dan nasa yana cewa"kaico da kai yarima kayi Babban kuskure kuskuren kuwa ba komai bane illah saduwar da kayi da wannan budurwa da ka kyaleta da zan iya dawo make da dukkan karfinka da karfin sihirin ka da karfin sihiri na amma yanxun aikin gama ya gama kasani cewa daga rana irin ta yau ka daina jin sha'awar kowacce mace a duniya inba shamril ba sannan ina mai sanar da kai a yanxun hakan nan baka da wani sauran karfi ajikin ka da kai da macen data shekara Dari a duniya duk daya dan ba abinda zaka Iya tabukawa



Magana ta karshe shine tabbas shamril zata samu ciki da kai kuma zata haifama magaji kuma zai taso da tsananin tsantsar jarumtar da kai karasa kuma tabbas sai yayi ajalinka dan shine zai kashe ka idan kanaso ka hana faruwar wadannan abubuwa anya daya ce hanyar kuwa ni kaina bansan ta ba amma tabbas akwai mafita a yanxun hakan nan duk duniya boka daya nehh zai iya ma wannan aikin ba kowa bane face BOKA BURNUHUL MANSUR amintaccen da nakeji dashi acikin wannan birnin



Kasani a duk duniya ba wanda yake da maganin wannan matsala taka inba shi ba sabida haka yanxun zan kirashi sai ya fada maka maganin kafin sarki Darraju ya rife bakinsa kawai sai ganin wani koren haske sukayi ya ratso bangon dakin ya shogo take haske ya rikide ya koma boka barnuhul mansul yana mai kyalkyala Dariya saida ya jima yana wannan Dariya tukun daga bisani ya turbine fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya kalli sarki Darraju yace"





Gani ma na bayyana ya shugabana kuma naji duk abinda yaje faruwa da yarima mangul tabbas yayi ganganci ba kadan ba domin wannan yarinya shamril yar wani gahutaccen boka ce shi yarima mangul da kansa ya kashe mata mahaifin ta ya dauko ta daga birnin su shiyisa ta masa wannan shiri batun haihuwa kuwa wannan bakin alkalami ya ruga ya bushe tabbas sai ta haihu da kai kuma idan kayi wasa danka shine zai kashe ka





SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORYWhere stories live. Discover now