SADAUKI RAZMIR PAGE 20↔25

24 3 0
                                    

🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵

Writing by

ALIYU H ISHAQ
   (fast class)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
     And now
          ↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

🅿 20↔25







..........Kamar yarda boka salsalul num ya fada haka al'amarin ya kasance wato shi da kansa ya fara bawa Razmir horon yaki mai tsanani a kullum idan suna horon nan sai ya suma sau bakwai amma daya farfado ya tuna da mahaifan sa sai yaji zuciyarsa ta keka she ga barin jin tsoro nan take zai zage kwanji





Ta guri daya Razmir ya ke samun saukin wannan horo shine ta gurin gudu indai anzo fagen gudu to shi gwani nehh dan yana iya shafe kwana arba'in yana gudu ba tare da ya nemi abunchi ba shi kansa boka salsalul num yayi mamakin wannan baiwa tasa sabida a lokacin da yazo bashi wannan horo suna kasa tsere kan kace wani abu Razmir ya bashi rata mai yawa ta yarda bazai iya kamo shi ba





Haka al'amura suka ci gaba da tafiya inda Razmir yake karban horon a gefe daya kuma ga yarima mangul da zaluncin sa ya Kuma shahara a kasashen duniya dan yanxun ma kasa kasa yake turawa indai aka ga yarinya mai kyau sai a dauko masa ita a kawo masa shikuma da yagama amfaninsa da ita zai kasheta dan shi bayason magaji a rayuwarsa


Idan ko aka Nuna masa yarinya ya nemi ta taki to fahh har birnin su xai dauki runduna suje ta jawa yan birnin koh sun kai su million sai ya kashe su zai dauko ta a gurin zai keta haddin ta ya kashe ta ya debo bayi da ganima ya taho gida





Ta kai ta kawo shi kansa Darraju abin yana matukar damunsa yana son ya hanashi abinda yake yi amma baya son bacin ran dan nasa dan haka ya kyaleshi yayi duk abinda yake so sabida yana kawo makudan kudade cikin kasar sannan yana kawo bayi kosassu wadanda idan aka sai da su za a sami riba mai yawan gaske






Yarima mangul nehh zaune acikin turakar sa yana wa yar kanwarsa wasa wato gimbiya lamrita dan yana son ta sosae wani badakaren sa nehh ya shigo mai suna dufan yana shigowa ya zube ya kwashi gaisuwa




Dagowa yayi ya kalleshi sannan yace"an gaisheka dufal jarumin jarumai kuma amin tacce na shin akwai wani kamun nehh

Cikin biyayya dufal yace"kwarai da gsk ya shugaba sunan ta shamril anan yamma da wannan birni namu mai albarka take cikin birnin damjul ranka ya dade sai dai itace sarauniyar birnin shugabana




Cikin izzah yarima mangul ya dago ya kalleshi yace to dan itace sarauniya sai me kawai kaje mata da bukata ta idan taki nayi aikina



Cikin biyayya dufal yace an gama ya shugabana yana kaiwa nan ya Mike ya fita



Bayan kwana daya ya dawo wa yarima mangul da mgnr sarauniya shamril akan taki amincewa da bukatar su



Cikin matukar fushi ya dauki takobin sa ya five daga turakar tasa dufal ya rufah masa baya kai tsaye burgar dawakai ya nufah tun kafin ya karaso aka daurawa doki siddi yana zuwa ya haye ya sakar masa linzami


SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORYWhere stories live. Discover now