🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comDAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)🅿 15↔20
.........bayan wadansu dakiku nehh gimbiya Numaira ta dauke kanta daga kan na sadauki razmir sannan ta kalli boka salsalul num tana mai yi masa murmushi batare da tace wani Abu ba ta tafi da sauri ta dauki wannan jaririya dake kan gado ta fara mata wasa
Hakan ba karamin dadi yayi wa Razmir ba nan take yaji sanyi a ransa
Kamar daga sama yaji maganar boka salsalul num yana fadin "ya kai Razmir shin zaka iya fadamin abinda kayi wa wadannan dakaru na sarki Darraju har suke binka
Koh da jin wannan tambaya sai idanun Razmir suka cika da kwallah kana ya kalli wannan tsoho yace " ni dai tunda na taso acikin Daji naga iyayena anan na girma babana mafarauci nehh amma koh kadan bayaso na gajeshi duk SANDA nayi masa batu akan ya koya min yaki da yadda ake farauta sai ya dafah kaina yace
Ya kai Dana kayi sani cewa nayi bincike akan alkaluman taurarin ka nagano cewa har abada bazaka taba gada ba idan zan shekara dubu ina koyama farauta bazaka Iya ba balle har ka gajene
Kasani cewa ina hango mutuwa ta nan kusa tare da mahaifiyarka dan inaji a jiki na mun kusa rabuwa dakai dan akwai wani babban al'amari dayake tun karo rayuwarka Kuma wannan al'amarin shine zai yi silar mutuwa ta nida mahaifiyar ka sannan ina mai tabbatar maka ni farauta ba gadar ta nayi ba a bisa dole nakeyin ta dan mu rayu da ni da Ku yana kaiwa nan naga ya fashe da kuka
Nan na shiga rarrashin sa amma saida yayi mai Isar sa sannan yayi shuru ya kalleni yace"ya kai Razmir kasani cewa na boye ma abubuwa da yawa acikin wannan DUNIYAR amma da sannu zaka sani bayan bana raye yana kaiwa nan ya tashi ya shiga yar bukkar mu sakamakon nishin da yaji ammina tanayi dan dama tana dauke da cikin wannan jaririya
Bayan wani dan lokaci nehh nafara jin kukan jariri na tashi daga cikin bukkar nan ba karamin farin ciki nayi ba dan banda burin da ya wuce naga kani na koh kanwata ba a Jima ba saida abbana ya tare da wannan kanwa tawa a hannu yana zuwa ya damkamin ita a hannu yana hawaye sannan yace"ya kai dana wannan itace kaddarar ka a wannan duniya sabida haka inason ka tafi da wannan yarinya wani wajen kuje ku rayu kasani cewa a yanxun hakan nan dakaru sun xagaye wannan guri da miyagun makamai dan su kashe mu kayi amfani da baiwarka gurin tsira da rayuwarka nasan zaka iya yana fadin haka ya karbeta ya daureta a bayana sannan ya miko min guziri yace na tafi
Kasa motsawa nayi na tsaya agu daya ina hawaye ina kallon sa ban Ankara ba naji wani Motsi mai yawa ya cika da jin wata Uwar tsawa Abbana ya buga min yana mai bani umarnin na tafi
Ban yi wata wata ba na yanki hanya na run tuma da azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya ban jima ina gudu ba nafara jiyo kururuwar iyayen mu suna ihu bayan wani dan lokaci kuma naji shuru nan take kwallah ta fara zubo min dan nasan na rabu dasu har abada baki daya
Ban gushe ina gudu ba har saida na iso birnin Hindu anan na ci gaba da rayuwa har tsahon wata uku ina shayar da wannan kansa tawa da har yanxun ban sa mata suna wata Rana ma saina sha duka kafin na samu abinda zan bata taci nasha wahala sosae kafin zuwan wannan rana da na kwaci gurasa a hannun badakaren sarki darraju suka biyoni nasha dakyar a hannun su,
Kwalla ce ta cika a idanun boka salsalul num saida ya zubar da kwallah kana daga bisani ya kalli Razmir yace"lalle kaga rayuwa Dana to kasani cewa wadannan dakarun da suka kashe iyayen ka ba kowa ya tura su ba illah sarki Darraju kasani cewa da chan baban ka shike mulkin birnin Hindu wato SARKI HAWWASHA sarki nehh mai adalci da kyautatawa talakawan sa Darraju ko bawansa nehh wanda ya amince dashi Dari bisa dari yaudarar sa yayi wata rana bayan an haifeka mahaifiyarka ta koma gida wanka tsakanin birnin Hindu da birnin su tafiya ce ta kwana daya da yini daya to a ranar da zata dawo nehh sarki hawwasha yace shi kadai zaije ya taho da ita shine ya bar Darraju a matsayin wakilinsa to dama Darraju yana da shirin sa nayin juyin mulki to ga dama ta samu kawai sai yayi amfani da wannan dama ya kashe duk wani babba a garin ya dare karaga a ranar da sarki hawwasha ya dawo ya sami lbr sai yaki shiga birnin kuma yayi Dana sanin yarda da Darraju da yayi Daji ya koma Ya kafa tantinsa daga ranar ya koma mafarauci yana badda kama ya kai birnin Hindu a siya ya sayo kayan abinchi wannan shine lbrn da abban ka yake boye ma Kuma dalilin sa nakin koyama farauta ba komai bane illah burinsa
Bokan sa ya tabbatar masa da cewa Kaine zaka kawo karshen mulkin zalunchin sarki Darraju lokacin da yaji haka sai yayi yunkurin sanar da kai komai amma sai bokan sa ya hanashi yace idan ya fada ma bazaka taba yin nasara akan sarki Darraju ba akwai lokacin da zaka sani da kanka Kuma gashi kasani yau dan haka sai ka shirya,
Cikin rashin fahimta ya kalli boka salsalul num yace"ya shugabana to taya zan iya tarar wannan azzalumim sarki alhalin ni ban kasance jarumi ba
Boka salsalul num ya kalleshi sannan yace"daga yau zam fara baka boron yaki iya kar iyawa ta bayan ka samu horo mai kyau kafin nan yar uwarka ta girma sai ka dauki gimbiya numaira ku tafi birnin sin domin ka sadu da BOKA MUTSULUL GAYUSH kasani cewa duk duniya ba wanda yake da karfin sihirin tsafi irin na boka mutsulul gayush zaka he ka zama yaron sa na mako daya a sannan neh zaka sami horo irin nasa kasamo cewa a hangar zuwa birnin sin akwai wani gwaggwan biri mai shekara dari uku a duniya kasani cewa a shekara arba'in baya ba a Kuma samin mahalukin daya ratsa wannan Daji ya shiga birnin sin ba a Raye kasani cewa dole saika kashe wannan gwaggwan biri sannan burin ka zai cika
Bayan nan kuma zaka tunkari birnin KUFA dan ka sadu da SADAUKI DARBUZA masana da masu bincike sun tabbatar da cewa ba wani mahalukin daya kai sadauki darbuza karfin dantse a dniya sai mutum daya ba kowa bane wannan mutumi ba face sarki Darraju nan ma acikin mako daya zaka gama komai ka huce gaba
Sannan a hanyarka ta zuwa birnin kufa acikin wani kungurmin daji akwai wata muguwar macijiya mai kawuna arba'in sama da shekara goma ba wani mahaluki daya taba ratsa dajin nan ya huce lpy saidai gawarsa
Bayan nan a gabas da birnin damaska akwai wani karamin kauye mai suna GURGUN acikin wannan Kauye akwai wata gawurtacciyar mayakiya mai suna MURHALU masana da masu bincike sun tabbatar da cewa a duk fadin duniya ba mayakin daya kaita iya sarrafa takobi
Haka a hanyar ka ta isa birnin damaska akwai wani rukakken zaki daya tare hanyar nan sama da shekara Biyar an daina shige da fice acikin wannan birni dole saika yaki wannan zaki ka kashe shi sannan zaka sadu da jaruma MULHALA
koh da jin wadannan batutuwa sai idanun Razmir suka zazzaro zuciyarsa ta buga amma daya tuna da mahaifan su sai yaji zuciyar sa ta keka she ga barin jin tsoro nan take yaje ya daga kan kanwarsa yana mai fadin
Na rantse da wannan kansa tawa koh zan rasa rayuwata saina cika burin mahaifina............
TOM YANXUN FAHH AKA FARA FADAN BA A SOMA KOMAI BA FANS GSKY INAJIN DADIN COMMENTS DINKU ALLAH YA BAR KAUNA
Vote
Comments and sharedWhatsApp number 08143314152
By fast class
YOU ARE READING
SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORY
Aventurawannan lbrn kirkirarren lbr nehh banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba sannan ban yarda wani ko wata ya chanza min lbr ta ko wace siga ba