SADAUKI RAZMIR PAGE 10↔15

32 2 0
                                    

🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵

Writing by

ALIYU H ISHAQ
   (fast class)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
     And now
          ↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

🅿 10↔15



Dedicated to A T K PALACE GROUP





..............Al'amarin wannan saurayi dashi da yar jaririyar kanwarsa kuwa lokacin da ya shiga cikin wannan kogo mai zurfin bala'i har ya samu damar kaiwa karshen sa ya fadi kasa sumamme bashi ya farka ba sai bayan sa'a daya da rabi yana farkawa ya shiga laluben bayan sa jin da yayi wayam Alamar ba kanwarsa nehh ya matukar daga masa hankali biye da ko yaushe




Kawai sai ya Mike zumbur ya kama waige² yana Neman inda take



Chan ya hangota kan wani dan karamin gadon karfe na alfarma tana kwance ga madara nan a kusa da ita da alama an bata madarar


Zuciyarsa ce nan tayi masifar bugawa hankalin sa ya kai koluluwar tashi tsoro ya darsu a ransa

A hankali yake matsawa kusa da gadon yana mai waige²  gani yake yi ako da yaushe wani abun zai iya bayyana ya illatashi a hakan ya kusa kaiwa bakin gadon kenan kwatsam ba zato ba tsammani sai jin wata murya yayi ta cika kogon baki daya tana fadin




Lalle marhabun da sadauki uban sadaukai jarumi uban jarumai fasa taro SADAUKI RAZMIR IBN HAWWASHA


Ya kai Razmir ina son ka saki jikin ka tamkar kana dakin baccin ka dan idan kana nan ba wani mahaluki daya isa ya ganka balle ya kamaka ya kai Razmir kasani cewa yau shekara 20 kenan ina cikin wannan kogon dutse ina jiran zuwanka




A matukar tsorace Razmir yake fadin  "shin waye kai kuma mene nufin ka na jirana acikin wannan kogon har na tsahon kimanin shekaru 20 wanda a lokacin nan ma banzo duniya koh da Razmir yazo nan a zancen sa sai ya dan saurara yana jiran amsar tambayoyin sa




Ji yayi an kece da wata mahaukaciyar Dariya wadda take barazanar kashe masa dodon kunne daga bisani kuma sai yaji dariyar ta koma kuka sai da suka kusa rabin sa'a acikin wannan yanayi nehh sannan wannan mutumin da nima bansan ko waye ba ya ya tsagaita da kukan da yake yi



Zuwa wani dan lokaci dan Razmir yaga wani tsohon mutum ya bayyana a sama fuskarsa cike da hawaye tsohon yana ruke da wata farar SANDA a hannun sa sandar tana fitar da farin haske Wanda ya gauraye kogon  baki daya



Fuskar tsohon cike take da gashi tako ta ina kallon Razmir yayi sannan yace" da farko dai sunana BOKA SALSALUL NUM ni haifaffen birnin rum nehh



A shekaru 20 baya lokacin sarki darraju yana kan ganiya zaluncin sa yarda ya keso to shine ya kawo wa birnin mu ziyara ta bazata saida ya kashe kowa da kowa na birnin sannan ya tunkari gidan sarautar birnin a wannan lokacin sarauniyar dake mulkar mu tana dauke d tsohon ciki bazata iya yaki ba shine ta samu aka kirawo ni bayan mun kadaita nehh take cewa




Ya kai abin dogaro kasani cewa tun kafin wannan masifah ta afko mana nariga nagani a mafarki ni a yanxun burina daya nehh nasan bazan rayu ba a wannan rana amma ina matukar San abinda zan  haifah ya rayu dan ya gaji karaga kuma nayi bincike na gano cewa kaf cikin birnin nan kai kai nehh zaka iya bashi kariya yarda ya kamata har ya rayu ya kai munzalin da ake so a rayuwa




Daga yau daga yanxun na dam ka maka amanar abinda zan haifah



Tana kaiwa karshen wannan furuci NATA nehh nakuda ta kamata amma abin mamaki mai makon tayi kuka sai murmushi ya bayyana akan fuskar ta




Da sauri na fita na samo wasu kuyangi suka taimaka mata nikuma na fita chan filin fadar inda dakarun mu ke fafata kazamin yaki da sarki darraju shi kadai ya zame musu tamkar shaidani duk inda yasa gaba saidai kaga kawunan bil'adama na shawagi a sama





Wannan abun shine yasa raina yayi mugun baci cikin bakin zafin nama na zare sandar tsafina nayi kansa da mugun gudu ina mai kwallah ihu ina isa na shammace shi na dankara masa naushi a kirji saida yayi juyi biyu a tsaye sannan ya durkushe yana tashi muka kachame da masifaffen yaki sai da MUKA kwashi sa'a hudu muna kwabzawa amma dayan mu bai sani wata nasara ba dan haka da naga wankin hula yana Neman ya kaini dare nehh yasa na shammace shi na make kafar sa ya durkushe kafin ya Ankara na bace








Ban bayyana ako ina ba sai a turakar sarauniya ina isa naga ta haifi ya mace amma ita ta mutu ba karamin bakin ciki nayi ba haka na dauko wannan yarinya MUKA bar birnin




Shiko sarki darraju koh da yaga sarauniya ta mutu sai ya nuna wa mutanen birnin suyi mubayi'a koya kashe su nan suka mika wuya ya Nada wani Babban hadimin sa mai irin halinsa akan karagar mulkin





Bayan wasu kwanaki nehh muna zaune nida wannan jaririya ina shayar da ita da madarar shanu itama hadimai na na aljanu nake sawa su kawo min kullum bayan tasha ta koshine naji Alamar tafiya a bayana



Nan take na dauki wannan jaririya na shige cikin bukkata na hada komai nawa nan take MUKA bace bat



Bamu bayyana a ko ina ba sai a karshen wannan Daji dake yamma da birnin rum anan nehh na yi bincike akan wadanda suka kawo mana nan naga dakarun sarki darraju nehh suka kawo min hari dan su kamani su kaini gunsa dan tun sanda MUKA fafata dashi ya kasa kashe ni yake kyankyamin kansa yace dole sai an kawoni ya kasheni





Koh da naga haka sai na shiga binciken mafita dan bazan iya tunkarar birnin Hindu da yaki ni kadai ba dan haka na shiga Neman mafita ban jima ina binceke ba a madubin tsafina na gano cewa banda wata mafaka inba cikin wannan kogon ba nan kawai xan shiga na tsira da rayuwa ta data wannan yarinya sannan idan ina cikin sa nan da shekara daya za a haifi wani yaro acikin birnin Hindu wannan yaron shine zai wanzar da adalci a wannan nahiya baki daya kuma shi kadai nehh zai iya Mayar da wannan jariri ya daya sawa suma NUMAIRA kasar ta ta haihuwa har ya cika burin mahaifiyar ta







Koh da naga haka sai na shiga binciken inda zan ganka acikin birnin Hindu bayan kazo duniya nan fahh Abu yaci tura sai a karshe nehh na gano cewa Indai ina Cikin wannan kogo kai da kanka zaka kawo kanka har inda nake kuma a sanda xakazo da Neman taimako zakaxo guna,,






Wannan shine lbrn na yanxun kasan koni waye sannan ina mai gabatar maka da gimbiya NUMAIRAH tsoho salsalul num ya fadi haka yana mai nuna wani bangare daban da hannun sa






Wata kyakykyawar budurwa ce ta fito ta gaban kwatance komai NATA yayi dai dai da tsarin jikin ta shi kansa Razmir sakin baki yayi yana kallon ta





Itako koh kallonsa batayi ba ta huce gurin boka salsalul num tana mai fadin gani ya kai abbana akwai abinda kakeso nayi maka nehh yanxun







Dafa kanta boka salsalul num yayi yana fadin babu komai yata bakin da muketa jira nehh sahon shekara 20 yau gasu sun bayyana kansu



Sai a wannan lokacin ta lura da Razmir da kuma wannan jaririya dake kan gadon ta sai wasan ta take




Kallon kallo suka tsaya yi itada Razmir acikin su an rasa Wanda zai dauke fuskarsa daga cikin su kowa da abinda yake sakawa a ransa..........







Wannan kenan ni kam nafi tunanin tafiya lbr ya kare yanxun ZAMU shiga cikin gundarin lbrn dan haka kubiyoni muje zuwa ni iya comments dinki kawai nake bukata




Vote
Comments and shared





WhatsApp number 08143314152




By fast class

SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORYWhere stories live. Discover now