🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)DAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)🅿 1↔5
Wannan labarin wanda nasama suna (SADAUKI RAZMIR) gajeren labari labari nehh daya faru a gaske dan haka ban yarda wani koh wata ya chanza lbr daga wata ciga zuwa wata ciga ba
SHINFIƊA*_
_Bismillahir Rahmanir raheem,na fara da sunan Allah me rahma me jin kai,yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanallilahi wata ala.Tsara da aminci su tabbata ga annabi MUHAMMADU cika maki annabawa shugaban manzanni da ahalin gidansa baki ɗaya_
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI
...............Wani matashin saurayi nehh wanda bazai wuce shekara goma sha hudu ba saurayin yana rike da wata jaririya wadda bazata haura wata uku ba a duniya
Gudu yake yi na fitar hankali wanda da gani gudun ceton rai nehh yana gudu yana waigawa bayan sa a matukar tsorace sabida gani yakeyi a koh da yaushe dakarun birnin Hindu zasu iya cimmasa
Bai gushe ba yana wannan gudu ba tun safe har rana ta soma faduwa anan nehh gajiya ta riskeshi ya zube kasa yana mai fitar da numfashi sama sama a yayin da ya yar da yar jaririyar dake hannun sa chan gefe daya tana mai tsala kuka
Bayan wani dan lokaci nehh wannan ya jiyo sukuwar dawakai ta koh ina suna masu kusantoshi da alama sun zagayeshi ta koh ina
Da sauri ya dauki jaririyar nan yana mai rufe mata baki sabida ta daina kukan da takeyi
Amma ina aikin gama ya gama sabida wannan jaririyar ta Riga da ta fallasa shi sakamakon kukan da takeyi tun dazun
A hankali yaji takun sahun dawakan yana mai kara kusantoshi nan take hankalin sa yayi masifar tashi sabida baisan yarda zaiyi ba dabarar sa ta kare yana cikin wannan yanayin nehh ya hango wani kogo daga chan nesa dashi kadan
Da sauki ya tashi yana tafiyar sanda dan kada suji takun sahun tafiyar sa yana isa kusa da kogon bishiyar ya fara kokarin shiga ciki amma ina bakin kogon yayi kankanta da yawa bazai yuwu ya shiga ba
Sabida haka nehh hankalin sa ya Kuma tashi ya rasa dabarar da ya kamata yayi
Bayan wadansu yan dakiku nehh wata dabara ta fado masa kawai sai ya zagaya bayan wannan bishiya ya labe yana buya kuwa sai ga dakarun sun iso kimanin su ashirun da doriya
Dakarun kowa yana rike da zabga zabga takubba masu matukar kaifi da tsini
Dakarun sin kasance zabga zabga tamkar bishiyar kuka sannan suna da kira tamkar mutanen farko ni kaina da naga wadannan dakaru sai da na tsorata
Wannan Matashin yaro yana make a bayan wannan bishiyar ya xuba musu idanu a matukar tsorace saida ya tabbatar da da sun kusa iso wa inda yake nehh yayi sauri ya ya cire rigarsa ya Goya wannan jaririya a bayan sa saida ya tabbatar y daure da kyau sannan ya dauki wani itace mai tsini da ya gani a kusa dashi ya gyara tsayuwarsa
Sai da ya tabbatar sun iso daf dashi sannan yayi fitar burgu daga bayan bishiyar yana mai kwala ihu kai tsaye yayi kan wani badakare yana mai tsala ihu yana isa daf dashi kafin badakaren yayi wani yunkuri tuni wannan matashin saurayi ya da ka tsalle ya kirbawa dokin nan wannan icen a yuwa take icen ya fasa wuyan dokin ya bullo ta daya bangaren nan take dokin ya sulale kasa matacce
Shiko wannan saurayi koh da yaga ya samu hanya saiko ya dauki hsnyar nan ya fita da azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya
Duk da ba ganin hanya yake yi ba sosae sakamakon duhun da ya fara mamaye gurin baki daya
Suke wadannan dakaru koh da suka ga abinda ya faru da dan uwan su sai suka kuma tunzura suka rufah masa baya
Abu daya nehh yake basu mamaki a game da wannan saurayi wato tsananin karfin gudun sa gashi dai karamin yaro mai karamar halitta amma idan ya huce gaban Abu to har abada bazai kamu ba fahh saidai idan shi ya tsaya da kansa.............
Wannan kenan idan naga yawan comments zanci gaba da typing idan naga akasin hakan to zan tsaya anan fatan alkhairi fans
WhatsApp number 08143314152
Vote
Comment and sharedBy fast class
YOU ARE READING
SADAUKI RAZMIR ADVENTURE STORY
Adventurewannan lbrn kirkirarren lbr nehh banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba sannan ban yarda wani ko wata ya chanza min lbr ta ko wace siga ba