*TA'UMMU KA*🥳❔
(aure saida kaka)*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlight our reader's)_**wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357**LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*1-NUNA SO GABAN KISHIYA*
*2-AYSHAT*
*3-ZATOH*
*4-ANYA KUWA...?*
*5-NIGERIA KO NIGER(wacece bora)*
*AND NOW*
*6-TA UMMU KA(aure sai da kaka)**Alhmdlh ina godiya ga allah daya bani damar fara rubuta sabon littafi na mai suna ta ummu ka kuma ina rokonsa daya bani damar kammala littafin cikin ikonsa ameen summa ameen...*
page 1
Wata yarinya na hango yar shekaru 9 taci damara da dankwali irin na sofaffin nan fuskarta duk a zane yake dige~digen kwalli abinta wacce kallon farko zaka mata ka tabbatar da cewa yar kauye ce futuk gaba da baya...
kafafunta duk babu takalmi gashi kasa yariga da yagama lullube kafar wadda sai mutum ya lura da kyau zai fahimci babu takalmi a kafartata
tafiya take cike da kwarkwasa ga wata bakar laida a hannunta wacce bansan mainene a ciki ba... sai firirita takeyi sak yadda yemmatan kauye keyi ... duk inda tawuce saidai kaga mutane na binta da kallo wanda kai tsaye zakace ganin hauka sabon kamu suke mata amma sam abin ba haka yake ba
domin ko kallon ta sukeyi cike da burgewa sbd kaf cikin sa'anninta na cikin kauyen babu mai tsaftarta wai inji su da fada hakan yasa samarin cikin kauyen ke mutuwa akanta!
cikin tafiyar tata ne wata yarinya wacce zasuyi kusan sa'an da ita ta hango ta itama duk kanwar jace domin kou har gwanda ma dayar...
kwala mata kira tayi cikin budaddiyar murya yadda ta tabbata zata jita da kyau tace TA UMMU KA !!!
juyowa tayi cike da tsiwa dake cinta tunda take tafiyarta dama naiman mai sauke masa takeyi dan haka tasamu a bagas...
murkuda dan karamin bakinta tayi tace AURE SAI DA KAKA idan kinsan bazaki na karasar man da sunana ba tom ki daina fadaman ehe!
takare maganar tana murguda bakicike da takaici kawar tace danma kin samu na kula shine zakimin rashin kunya ko ta ummu ka?
takare maganar tana huci gata dama tabarakalla akoi jiki itakam-
harara wacce aka kira da ta ummu ka ta watsa mata cikin tsatsar tsageranci tace ke asuwaye dama bazan maki rashin kunya ba...?
ni asu zainabu abu mai tagwayen suna mata a gidan yusufa dan mai gari!
itama takare maganar cikin fusata ay kuwa ganin haka yasa cikin ta ummu ka kadawa amma ko a fuska bata nuna ba saidai ma kara tsuke fuska da tayi ganin har attention na mutane yafara dawowa kansu kar a raina ta sanin cewa datayi kaf cikin kauyen babu mai kawo mata wargi sai kawayen wasanta wayanda suka san cewa
ita din tsantsar tsiwa ce fal ciki! amma akoi dan banxan tsoro kamar farar kura gashi dama itadin bawani auki gare ta ba...
hakan yasa ko fada za'ayi itakam tana gefe koda kuwa da ita ake kawayenta ne masu shiga mata ita saidai tace tafi karfin hada jiki da yarinya amma akoi yaranta dazasu mata maganin marasa kunya manya da yara...
ganin yadda tayi da fuska yasa zainabu waskewa yana washe mata baki sanin datayi cewa yanxu mutane zasu fara terere dasu a cikin kauyen ace ay sunyi fada sukuma hakan sam bai masu dadi!
dan haka tasaki fuska suka kashewa juna ido aykuwa nan suka barke da dariya kamar wasu mahaukata...
cike da shekiyanci suke dariyar suna nuna wayan suke tsaye a wajen wanda hakan yasa mutane suka fara zamewa a wajen daya bayan daya kar wayannan yaran su kunya ta su a wajen!
hayaniya nake jiyowa na tashi inda wasu zugar ne wajen su biyar duk kafafunsu babu takalma ga kuma rana fatso fatso ake kwalawa a garin amma ga dukkana alamu ko a jikinsu hakan ne ya tabbatar man da cewa ba yau aka fara ba...!
wasu zuga zugan bulalai ne a hannunsu wanda yama fisu daza a auna suka tun karo wajen aykuwa kallon wayannan yara da akayi yakara hargitsa wajen hatta wasu manyan da sassarfarsu suke barin wajen...!
ganin yadda mutane ke fecewa yasa suka daka tsalle inda suka far masu da ruwan bulalai babu kakkautawa kuma babu ruwansu duk wanda bulakar yasamu babba da yaro aykuwa take aka fara gudu sukuwa yaran basu fasa ba saida sukaga an watse tas a wajen duk bulalar ta karye!
ta ummu ka da zainabu da suke tsaye sai dariya suke kyakyatawa abinsu ganin danyen aykin da abokannasu sukeyi wanda hakan ba karamin dadi yamasu ba?
cike da iyayi daya daga cikinsu wacce itama kamar ta ummu ka take babu kiba ko na sisin kwabo tace haba mata agidan yusufa wannan ay saiku saka a rainamu a cikin kauyennan mu muna can muna zaune aka zo aka fesa mana anganku kuna fada a bakin akurkin kasuwar nan...?
inaaaaaa gaskiya an fadi ba nauyi kuma anyi abin kunya! takare maganar tana yamutse fuska
zainabu tayi karaf tace aykinsanni bana naiman fadar daya daga cikinku kou deeje?
kawai dagayiwa ta ummu ka magana naga tanaso tamin bakin halinnata shine nikuwa naga bazan iya kyalewa ba amma kinsa ay yadda nake so furen dita bazan mata komai a gaban mutane ba!
takare maganar tana wani karkada ido ita ala dole tayi turanci(friend take nufi)
ta ummu ka tace ay nima ina sonki amma kinsan banso ana kwalaman kira acikin mutane kuma imma zaki kiranu daga nesa sai kina karasarwa bawai ta'ummu ka kadan basai kace bani ba...?
haka dai suka tsaya shiriritarsu ta ummu ka kuma tazuba masu ido saida suka gama shirmensu kana ta dauko laidar dake rike a hannunta kasancewar daga cikin kasuwa ta fito tace ma'u kuzonku muje mukaiwa dada wannan taliyar kamin ta ishe ni da mita nikam!
saike yar dada yemmata yau kuma dadan ake cewa mai mita ni ma'u??
fadar wacce aka kira da ma'u itama tana wani kwarkwasa ...
ki rabu da dada wai yau ita taliyar murji zata mana shiysa kiku ga ban zo kwanar mu ba ay...
cikin tsantsar tafiyar su ta kauyanci suke tafiya duk inda suka wuce saidai kaga ana dauke kai amma babu wanda ya'isa ta toshe hanci sbd wani karnin rana dasukeyi baki dayansu...!
gasu dukkansu babu wacce take a tsaftace sai wannan uban kwalliyar kwalli da aka zane fuska dasu gashi uban karnin datti dasukeyi...
haka suke tafiyarsu kamar bosawa kuma duk yaron daya gansu zakagansa yana ferere gudu idan ba haka ba kuma tsaf zasu mawa dan mutum mugunta koda kuwa bai shiga shirginsu ba...
muyi sauri mukai mata nikam mu tafi rafi muyi wanka yaukam sbd nima wari hammatata nakeji yau...
fadar ta'ummu ka kenan aykuwa kowa ma haka yake fada har suka dangana da gidansu ta'ummu ka
more comment more typing
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
YOU ARE READING
TA'UMMU KA!
Fantasyyarinya ce mara jin magana wacce kakaeta ta matukar daure mata gindi take shuka rashin ji a kauyensu,saidai kuma ta'ummu ka da zugar k'ayawayenta sun had'u da wani takadirin dan iska dayayi sanadiyyar rabuwarsu da ahalin kauyensu