part 6

72 6 0
                                    

     *TA'UMMU KA*🥳❔
         (aure saida kaka)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment and to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIEN2018*
*whatsapp number:09076427357*

    *LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*1-NUNA SO GABAN KISHIYA*
*2-AYSHAT*
*3-ZATOH*
*4-ANYA KUWA...?*
*5-NIGERIA KO NIGER(wacece bora)*
     *AND NOW*
*6-TA UMMU KA(aure sai da kaka)*

*Alhmdlh ina godiya ga allah daya bani damar fara rubuta sabon littafi na mai suna ta ummu ka kuma ina rokonsa daya bani damar kammala littafin cikin ikonsa ameen summa ameen...*

                page 6

Mutane na fitowa da zummar fita sallar asuba da tocilarsu kowa saiyaci karo da wari takalmansa a wajen wanda hakan yasa sukasan cewa dama dan gangan akayi masu iskancinnan...

ana idar da sallar mai gari yabawa kowa hakurin kana yashaida masu wayanda sukayi ayka aykar kuma insha allah zai dauki mataki akai...yusufa kam sai zare ido yake bawan alllah

aykuwa nan takaicinsu ya karu hatta ga iyayensu dan haka duk suka wuce gida da zummar tahowa da yayansu kofar mai gari...

shima mai gari ya kamo hannun yusufa suka shigo gida sbd ya fito da dafure...

yakuma tabbatar da kyar idan ta tashi yanxu sanin dayayi cewa akoita da son baccin safe wata rana ma da kyar ake tashinta domin zuwa makaranta...

Amma me...??  babu dafure babu dalilinta a cikin gidannan sama da kasa ... fitowa mai gari yayi cikin sanyin jiki da takaici yasamu waje yazauna inda yusufa ma ya rakube a wajen...

wayanda suka rage a wajen wato wayanda babu yayansu a ciki suma  dama a zaune suke basuyi magana ba saida sauran ma suka dawo cikin takaici shaidama mai gari ay basu ga yayannasu ba...

wanda hakaan ya kara harzuka shi sosai ba kadan ba dada ma zuwa wajen tayi tsille su kan duk wanda ya kuskura yataba mata jikarta hukuma ce zata rabasu (kujimin tsohuwa rikici fa?)

babu wanda ya kulata har ta gama babatunta tayi tafiyarta...

mota aka ciro a gidan mai gari irin akori kura dinnan, da wasu samarin kauyennasu hatta mai gari suka kama hanyar mamudo...sabida yaukam yayi alkawarin saisunji a jikinsu.........……

Bangarensu ta'ummu ka kam saida suka tabbatar dacewa sunyi nisa da baba mai gadi ta yadda baxai iya cimmasu ba kana suka tsagaita da gudun idan suka sayi koko da kosai a wajen wata mata kan kwalta suka ci sukayi nak suka shige makaranta,allah yasosu yau basuyi late ba

primary 3 suke kuma ta'ummu ka ce ass monitor a class din wanda namiji yakasance monitor...

malamin maths ne first period ya shigo inda yafara masu koyarwa wanda kaf cikinsu babu wacce ta iya maths sai ma'u...

gashi malamin maths dinnasu mugu ne na kin karawa shima baya tolerating na nonses,dama kuma ba dan kauyen bane shima tp yakeyi yazo daga potiskum...

hakan yasaka kowa natsuwa saida yaga saura time kadan period nasa yace kowa taciro peper zai masu ca...

duk suka ciro kuwa da biro nasu,kunsa makarantar kauyen sai hankali kujera kwaya 3 ne a class din...na mata 2 saina maza daya kasancewar mata sunfi maza yawa

ta'ummu ka,deeje,ma'u,zainabu da daci kulu suna seat daya zaune...sai dafure da mimiko suna zaune a seat na bayansu da wata yarinya gudu daya sbd jarabarsu na masifa kowa tsoron hada wajen zama yake dasu...

itadinma yarinyar kawai fitinanniya ce irinsu shiysa suka barta kan seat din amma kowa yana kasa akan tabarma...

haka dai akayi wannan test din duk ma'u ce tayi sukuma sai su kwafa saida yayi submitting saiga wani tsamurarren mlm yashigo da wani peper a hannunsa mai kama da mallam sas ...

inda yafara kiran suna kamar haka:

UMMU FATIMA ABDULHADI
zainab isyaku
asma'u talle
khadija amadu
furera musa gayabuna
hassana sa'idu
hauwa husseini

ku biyo ni yanxunnan!  yana gama fadar haka batare daya jirasu ba yafice...!

cikinsu kamar zasuyi fitsari da zawo a wando sun tabbata kiran mllm zalimu ba alkhairi bane ke kiransu dan haka suka wawuro jakakkunansu sukayi office na headmaster...

aykuwa tun daga waje suka fuskanci abinda ke shirin faruwa yau wato an biyosu daga kauyensu? sun gudu basu tsira ba yaukam sukam

har sun juya da niyyar fecewa sukayi arangama da barde yana masu muzurai...

wayyo allah zawo yaukam zai billo masu a wando domin ko kaf cikin kauyen nan sunfi tsoron barde sbd yanda yake cin ubansu idan ya cafkesu

gashi dama wani kafcece me zubin mutanen da ne ...

sumi sumi suka juya suka da tsantsar tsoro fal ciki suka shige office din,inda suka tarda mai gari fuskarshi kamar hadari

ha yusufa dake tsugune kamar wanda yayiwa sarki karya duk yazama abin tausayi sbd tsoro

shikam yau zainabu ta jaxa masa bala'i! idan haka akeyin soyayyar ya hakura kawai kowa ma ya huta domin ko ya lura bulala bata ayki a garesu

ananne mai gari sukayi sallama da headmaster nasu sbd sun riga da sun gama tattaunawa kamin suzo su...

bayan akori kurannan aka loda su baki dayan su aka wuce kauyen gaya buna dasu , kuka suke bilhakki yaukam

ta'ummu ka kam alllah alllah yake yau dada na da labari sbd tazo ta ceceta a wajen mai gari

         …………………………

wanene mallam mutari...?

mallam mutari dane ga wani abokin mai gari mai suna musale dasuke zaune cikin wani kauyen mamudo suma wanda yake makoftaka da garin gaya buna...

babansa natsatstsen mutum warai da gaske saidai kuma ya haifi fitinannen yaro wanda yakasance bayajin magana tun yana yaro karami...

wanda hakan yasaka shi taso cikin mummunar dabi'a ta mallamta,bawai malamin na allah bane pha!

mallamai masu hada allah da wani wayan suke bugun kasa wannan shine sana'ar mutari...

wanda hakan yadawa mahaifinsa hankali sosai har ya yanke shawarar turasa wajen mai garin gayabuna domin yayi karatun addinin allah kozai natsu

inda ananne ya hadu dasu ta'ummu ka wanda tun kallon farko daya masu yaji ya tsani ta'ummu ka har cikin zuciyarsa

gakuma rashin kunyar dasuke masa kuma duk ya lura yarinyar ke zugasu suka tafka wata tsiyar...

tom a lokacin daya bar kauyen gayabuna sanadiyyar abinda aka masa yasa a halin yanxu yana gaf da cinma matufarsa bayan yagano wayanda suka masa ayka aykar... bama kamar ta'ummu ka

wannan ne takaitaccen tarihin mallam mutari dan gayu...

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*

TA'UMMU KA!Where stories live. Discover now