part 3

104 6 0
                                    

     *TA'UMMU KA*🥳❔
         (aure saida kaka)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

    *LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*1-NUNA SO GABAN KISHIYA*
*2-AYSHAT*
*3-ZATOH*
*4-ANYA KUWA...?*
*5-NIGERIA KO NIGER(wacece bora)*
     *AND NOW*
*6-TA UMMU KA(aure sai da kaka)*

*Alhmdlh ina godiya ga allah daya bani damar fara rubuta sabon littafi na mai suna ta ummu ka kuma ina rokonsa daya bani damar kammala littafin cikin ikonsa ameen summa ameen...*

                page 3

abin tausayi dakuma ban dariya wallahy saida suka jibgesa tas iya son ransu kuma duk ihun dayake yi babu wanda zaiji sa... sabida wannan lungun ihunka banza ne...

gashi babu halin guduwa mai likaf ta danne sa ta yadda bazai iya fecewa ba...gashi bulalar yadiya akoi dan banxan zafi wlhy (sabida nima na taba shanta)

aykuwa suna gama laftarsa iya lafta kan yadawo hayyacinsa har ya ganesu suka ce kafa mai naci ban baki ba...?

mai likaf dinnan ma a dari ta mara masu baya inda basu zarce ko ina ba sai bakin rafi dukda yamma tayi amma basa tsoro sukam...

numfarfashi  suke ta zaukewa sbd ba karamin gudu sukayi ba aykuwa nan suka faracin dariyar kansu suma yau sunsan sunyi babban kamu sbd basu taba dukan babba ba sai akan wannan...kuma acewarsu shi ya jazawa kansa tunda ya taba ta'ummu ka har hannunta ya fashe kasancewarta fatar ta irin masu laushinnan ne dukda baya samu gyara kamar yadda yakamata...

ta'ummu ka ce ta kara tuntsura dariyarta a lokaci daya kuma tana nuna mai nikap da hannunta alamun shekiyanci ...

aykuwa mamaki ne yacika ni a lokacin danaga namiji tsaye da wannan hijabin a hannu shima yana dariyar hadda rike ciki wanda bazai wuce 15yrs ba...wanda hakan ya tabbatar man ba mace bace tayi wannan ayka aykar...

yaro dai danye shakaf dashi  wanda kallon farko zaka masa ka tabbatar da cewa jinin fulani ne...

saida suka gaji dan kansu kana suka tsagaita da dariyar tasu...cike da keta ta'ummu ka tace"gaskiya yusufa kaima ka iya mugunta...kaga yadda ka danne wannan dan matalikin kuwa...?"

"ay kedai bari kawai ta'ummu ka kinsan zogalen zuciyata da rashin yafiya yanxu saita je tace ma goggo fatsun ta fasa aurena kinga ko akayi haka ay an tona man asiri a kauyennan"

"wannan haka yake angon zainabu abu"fadar daci kulu daya daga cikiin yan zugar tasu kenan kaasancewar susu bakwai ne...

Ta'ummu ka
zainabu
deeje-khadija
ma'u-asma'u
mimiko-hassana
daci kulu-hauwa
da fure-furera

wannan ne sunayensu kuma kaf cikinsu bakwai dinnan ta'ummu ka ce masoraciya,akoi ta da dan banxan rashin kunya kamar me? gata da shegen tsokala kamar na inna naha...

saidae kuma fah empty ce idan tayi tsokalar akazo fannin dambe wannan kam sai a hankali...kawanyenta ne masu shiga mata

kuma mutane da dama basu gane hakan ba,a ganinsu ma ta'ummu karce ta koya masu fadan har suma suka koya sbd bata taba dambe ba itakam...

wannan kadan kenan daga cikin halayensu...a gaba za'aji wai shin wacece ta'ummu ka...? mai yasa kuma ake kiranta da wannan sunar...? sannan wayannan kawayen nata sukuma yayan waye...? wacece dada...? idan kuna bibiye da alkalamin ummien2018 duk zaku samu amsan tambayoyinku...

saida sukaji ana kiran sallah magari ba kana suka dunguma cikin kauyen nasu wanda duk magidanta sun wuce kofar mai gari inda anan ne ake sallah...yusufa ma buta ya dauko yayi alwala yabi jam'i...

dama suna la6e a  gefe suna ganin an tada kabbbarar sallah babu wanda yake zuwa suka sadada ta yadda baxa'aji takun kafafunsu ba sukabi takalman gurin daya bayan daya suka dauke warin takalman amma bin mmki sai suka ki daukar na yusufa hatta dana iyayensu kuma basu bari ba...

dama gashi mutanen basu dayawa kasancewar kauyen GAYABUNA karamar kauye ce kuma itama kauyen tana karkashin kauyen MAMUDO ne...

basuyi gudu ba cikin tafiyar sanda-sanda suka koma inda suka labe domin ganin mai zai faru kuma next idan an idar da sallar...

ana idar da salllah bayan anyi gayshe gayshe a wajen tsakanin magidanta sunyi sallama kan zasu tafi gida amma kuma mai zasu gani...??

kowa sai duba takalmansa yakeyi amma wari daya hatta da mai gari...

yusufa na mikewa shikuma yaga takalmansa a duka biyu suna nan aykuwa tunda yaga haka yasan aykinsu ta'ummu ka ne...

dan haka yaja bakinsa yatsuke kamar na allah sbd shikam shirmen yarannan yafara isarsa fa kar azo asan cewa shima yana daure masu gindi suke shuka iya shegensu ?

aykuwa wajen ya barke da hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinsa a wajen sai masifa sukeyi wayanda suke da gajen hakuri...mai gari kam yama rasa abin cewa sai ido daya zuba masu ransa idan fah yayi dubu shima ya baci kuma shikam yana da yakinin cewa wannan aykinsu ta'ummu ka ne ...

kuma hadda yarsa acikinsu wato dafure...! dan haka yaukam yayi alkawarin saiya ci kaniyarsu tayanda basa tunani

baima kowa magana ba haka magidantannan suka watse kowa yakagama hanyar gidansa babu takalmi a kafafunsa duk sun riko wari daya a hannu

mai yara zasuyi yau idan ba dariya ba? sunso ma da rana ne da ko abin zaifi bada sugar sbd anan kowa zai lura da hakan amma ko babu komai yanxunma gashi yara sun fara masu ihu suna yawo babu takalmi kamar su ta'ummu ka

sukuma dama burinsu kenan ayi yara su masu a tile yadda zasuji kunya sbd ramako suka masu...
muddin suka hadu da daya daga cikin mutanennan saisun masu magana kan yawo ba takalmi wataran ma sai su ska yara su masu ihu dukwai ko zasuji kunya suna yawo da takalmin amma kuma sam abin yaki ayki...

shine fa yau suma sukayi damarar ramawa sbd kawai suji dadi...

kowa takaici ne yacika sa amna kuma hankalinsu bai kai kan ga wayanda suka shuka masu iskancinnan ba...

haka suka tafi gida da wannan bacin ran ko sallar isha'i basu fito ba sbida takaici gashi dama wasun takalminnasu rai da rai ne...

mai gari ne da wasu tsirarrun mutane kawae sukayi sallah kowa ya mule gidansa

nan ko sukabi kofar gidan wayannan magidantan daya bayan daya suka ajiye masu warin takalminsu kana sukayi sallama kowacce ta wuce gidansu cike da farin ciki...

bagaren mallam dan gayu kuwa...??

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*

TA'UMMU KA!Where stories live. Discover now