*TA'UMMU KA*🥳❔
(aure saida kaka)*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_**wattpad:UMMIEN2018*
*whatsapp number:09076427357**LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*1-NUNA SO GABAN KISHIYA*
*2-AYSHAT*
*3-ZATOH*
*4-ANYA KUWA...?*
*5-NIGERIA KO NIGER(wacece bora)*
*AND NOW*
*6-TA UMMU KA(aure sai da kaka)**na sadaukar ga littafinnan ga daukacin makarancin littfaina baki daya *
page 18
A haka suke rayuwarsu da dadi,babu dadi...su hikimat nada shekaru shida allah yayima adamu rasuwa,wanda hakan ba karamin dagama madam hikimat hankali yayi ba,
sunyi kukan rashin mahaifinsu kwarai da gaske,wanda hindatu ma taje ta ta'aziyan mijin yar uwartata tare da yarta wacce itama tana da aure mai suna UMMU FATIMA!
dama kuma tun shekarun baya k'addara ta rufta a family house nasu madam hiikimat,gofara takama gidan tsakar dare,wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ahalin nasu baki daya,su kadai suka rage daga hindatu sai hikimat basu da dangi!
ganin yadda hankalin madam ya tashi takasa natsar da kanta,yasa hindatu tabama haruna shawarar kan yanaimi transper daga gurin aikinsa idan yaso saiya tarkata hikimat ta daina rayuwa a lagos ko zata dangana idan ta daina ganin abubuwan dazasu na tunda mata da marigayi mijinta!
babu musu,haka akayi ba'a dauki tsawon lokaci ba yasamu transper inda shima aka wurga sa garin kano,duk cikin shekara daya akayi wannan hatsaniyar!
alokacinne ciki yakara bayyana jikin fiddausi tare da yar gidan hindatu,ummu fatima wacce suke kira da ummu!
sunan mijin ummu fatima abdulhadi ne,suna zaune a kauyen dake mashigar garin kano!!
fiddausi ta haifi yarta mace,inda aka saka ma yarinya sunan mahaifiyar fiddausi amina data riga mu gidan gaskiya wajen shekaru 5 dasuka gabata!
suna ana kiran yarinyar da minal,ita kuma ummu ta haifi ya mace,inda taci suna fatima,mai sunar surukarta kenan maman abdulhadi,dada(hindatu) sbd haka ake kiranta,ta tafi garin azare domin halartar bikin kanin mijinta ummu ta haihu!
a ranar da ummu ta haihu dada ta dawo da kaddarar rabuwarta da yar uwarta kwallin kwal data rage mata a duniya!yarinyar da ummu ta haifa ta rasu a ranar batare da kowa yasani ba,dada da abdulhadi ne kawai suka sani!sai kuma ita kanta uwar yar,inda aka shaida ma mutane yan biyu ummu ta haifa amma dayar ta koma,sai dayar!
ummu na matukar ji da fatima karama,dan haka take kiranta da ta'ummu ka! ma'ana dai tata ce yarinyar (kunji yadda asalin suna ta'ummu ka yasamu kafuwa,dafatan an fahimceni)...
mijin hindatu yatafi yabarta da kewa,sannan mijin yarta abdulhadi ya shaida masu kan ta'ummu ka ba yarsa bace yar tsuntuwa ce,wanda hakan ba karamin matsala ya haifar ba suka ce sam baxasu karbi yarinyar a matsayin tasa ba!inda mahaifiyarsa tace an yaudareta an boye mata gaskiyar lamari tun farko,dan haka acanza ma yarinya suna yabar sunanta!
wanda hakan ba karamin fusata dada hindatu yayi ba tabiya kudi aka kawo rago inda aka yanka a cikin gidan aka maida sunan yarinyar tazama ummu fatima a maimakon fatima!
tsugune bata kare ba saida mahaifiyar abdulhadi tasaka yasaki ummu fatima duk akan sunyi taimako! dama kuma auren nasu na hadi gida ne sbd dangin mahaifin ummu fatima ne su abdul hadin!
yayi kuka sosai rabuwarsa da matarsa wanda hawan jini ya kamasa har abin yazo da ajali yabar masu duniyar baki dayanta,labari yakaima ummu fatima mutuwar tsohon mijinta,wanda hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba itama,a tsaye take zabgewa na ban mamaki!
YOU ARE READING
TA'UMMU KA!
Fantasyyarinya ce mara jin magana wacce kakaeta ta matukar daure mata gindi take shuka rashin ji a kauyensu,saidai kuma ta'ummu ka da zugar k'ayawayenta sun had'u da wani takadirin dan iska dayayi sanadiyyar rabuwarsu da ahalin kauyensu