UKU

333 49 13
                                    

💔ALHUBBU DAYYI'AN 👎

®NWA

©Oum-Nass

   _Assalama alaikm. Barkanmu da sallah 'yan uwa, fatan anyi sallah lafiya? Allah ya mai-maita mana yasa mai lada mukayi. Ina fatan dai ba ku ci nama ya muku yawa ba. lolx_

___________________________

Saboda gudun da yake a mota yasa bai ɓata lokaci mai tsayi ba ya shigo garin Faskari.
  Dai-dai wajen da suka samu saɓani da yarinyar ya tsaya, yana nazartar wajen, zafin da zuciyarsa take da kuma abin da ta masa ya sa shi rintse idanuwansa, dan gani yake kamar a lokacin ta mare shi.

   A hankali ya fara bin wani ɗan lungun da suka shige bayan yarinyar da yake tunanin ƙawarta ce ta jata.
  Motarsa ya buɗe yana ƙara nazartar yanayin unguwar da bata da yawaitar mutane, haka kuma babu yawan masu shige da fice a wajen.
  Asalima unguwar ta kasance a ƙarshen garin ne irin sabbin shugowa garine a wajen, musamman idan yayi la'akari da gonakin da suke tsallaken wajen.

  Ya ɓata kusan awa ɗaya kafin wani matashin saurayi ya futo a lungun da yake da tabbacin na su yarinyar ne.
  Kallo ya bi saurayin da bai gaza shekara 18 ba, sai dai yanayin shigarsa da kuma silifas ɗin da ke ƙafarsa ya bashi tabbacin yana cikin halin rashi.
 
  Har yazo kusa da shi zai gifta yayi saurin yi masa sallama, da sauri matashin ya juyo yana amsawa, kana ya risina cikin girmamawa ya gaida shi.
   "Dan Allah abokina in ba damuwa zan tambayeka."
  "Allah yasa na sani." Matashin saurayin ya faɗa yana risinawa cikin girmamawa.

   "Yauwa  akwai wasu 'yan mata da naga ga ni sati ɗaya da ya wuce sun shiga wanan layin naka, ɗayar na sanye da hijab yayin da ɗayar kuma take rataye da mayafi.
   Shine nake son sanin bayani akan su idan ba damuwa."
  Shuru matashin saurayin yayi, yana nazartar Aryan Sultan, daga ƙarshe ya girgiza kai.
   "Gaskiya ba'a nan unguwar ka gansu ba." Ya faɗa yana yamutsa fuskarsa.

  Murmushi Aryan sultan yayi, sanan ya zura hannunsa aljihunsa ya zaro rafar 'yan ɗari biyar, ya fara fifita a da su "Naso ƙwarai ace ka gane 'yan matan da nake magana akansu, da babu abun da zai hana wanan kuɗin ya zama mallakinka.
  Amma kuma tunda baka sansu ba, ga wanan." Ya ƙarasa maganar yana zaro sabbin ɗari biyu a aljihunsa guda biyar ya miƙa masa.
  Hannunsa na rawa ya karɓi kuɗi, "Ka min kwatancen kamanninsu yallaɓai, wata ƙila zan gane su."
  Murmushi Aryan sultan yayi, a hankali ya shiga siffantama saurayin kamanninsu, daga ƙarshe ya ƙarasa da "Amma ni nafi son sani wacece mai hijabin nan, domin hankalina yafi karkata akanta."

   "NIMRAH ABDALLAH KANAWI zaka ce yallaɓai."
   'Nimrah!' Aryan Sultan ya faɗa a zuciyarsa, yana jin zafin da ke zuciyarsa na raguwa.
"Haka sunanta?" Ya tambaya cikin tattausar muryarsa.
   "Eh yallaɓai, bama iya sunanta ba, zan faɗa maka komi da ya danganci rayuwarta, saboda maƙotan gidanmu ne. Ɗayar kuna da ka gansu tare ƙawarsu ce tare suka taso sunanta Aziza Abdul-aziz kaigama."

  Kai Aryan Sultan ya jinjina yana nazartar matashin da ke rattaba masa bayani "Idan ba damuwa shigo mota sai muyi maganar saboda mutane."
  "Ok!" Ya faɗa yana buɗe masa gaban motar, shima Aryan Sultan shiga motar yayi yana fuskantar matashin saurayin. 
  "Bani labarin abun da ka sani akanta."

     Gyara zamansa yayi a jikin motar "Kamar yanda na faɗa maka sunanta Nimrah Abdallah kanawi, asalinsu mutanen kano ne, yanayin zama da kuma aiki ya dawo da mahaifinta Abdallah nan garin, wanda ba wani aiki ne mai girma yake yi ba asalima masinja ne a kamfanin sarrafa fata na Kainuwa investment, suna da reshe a kano, amma da yake ma'aikatan sunyi yawa yasa aka dawo da wasu daga ciki na reshen nan katsina.
  Shine ya samu gida ya fara haya anan garin yana tafiya katsina yana barinsu sai a mako yake zuwa, daga ƙarshe ya siyi gidan ya zama nasa.

   Nimrah itace babbar 'yarsa akwai ƙannenta uku biyu mata ɗaya namiji Sa'adiyya, Zahra sai kuma autansu Nauwass.
  Mahaifinsu ya tsufa saboda ƙarancin lafiyar da ke gareshi, hakan yasa kamfani ya sallame shi, daga nan madadin ya koma gida sai ya fara aikin sayar da kayan gwari a bakin kasuwa. mahaifyarsu kuma Umma Habiba ta ke sana'ar kayan miya a gidan.
  Nimrah ta ƙare karatun sikandire ɗinta da ƙyar, saboda gazawar mahaifinta, amma tana da buri sosai akan karatu, hakan yasa ta sha alwashin tsayama ƙannenta suyi karatu, daga lokacin da ta yanke wanan shawarar ta fara yin aiki kula da yara a makarantun kuɗi da suke garin.
  Bata sha wahala ba aka ɗauketa saboda tana da takardar kammala karatu, haka kuma tana da nutsuwa da kula da yaran yanda ya kamata.
  Nimrah tana son ƙannenta fiye da komi a rayuwarta, akansu ta ɗora duk wani burinta wanda bata samu cikarsa ba akanta.
  Koda iyayen da suka haifeta ne za su nuna cewar su suka haifesu amma ba wai suna sonsu fiye da itaa ba.
  Rauninta a rayuwa shine ahalinta, da kuma ƙaunar da take musu, haka kuma tana girmama duk wanda ke girmama ahalinta, zata maka dariya a lokacin da ta ga ka damu da ƙannenta.
   Wanan shine taƙaitaccen tarihin NIMRAH ABDALLAH KANAWI."

   Kuɗin hannunsa Aryan Sultan ya miƙa masa "Nagode da wanan labarin naka."
  Jujjuya kuɗin matashin saurayin yake yana lissafin adadin shekarunsa da ya ɗauka a duniya bai taɓa riƙe koda rabinsa ba.

  "Wanan duk nawa ne?"
Kai Aryan sultan ya gyaɗa masa yana murmushin da iyakarsa laɓɓansa.
  "Nagode sosai yallaɓai, Allah ya saka da alkhairi, lallai wanan ranar farar rana ce a gareni."
  Murmushi Aryan ya masa yana buɗe masa ƙofar motar, jiki na rawa matashin ya fice. Ƙofar motar ya janyo sanan ya kwantar da kansa a jikin kujerar ya saki wani tattausan murmushi gami da dariya.

   "NIMRAH kyawawan ranakunki sun fara daga yau." Ya faɗa yana kunna motar ya bar wajen zuciyarsa cike da farin ciki da nishaɗin da ya manta rabon da yayi shi..

🌷

HAPPY SALLAH

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now