SHA BAKWAI

173 20 1
                                    

💔ALHUBBU DAYYI'AN 👎

  ®NWA

©OUM-NASS

 page17

FASKARI.

  A hankali Umma ta tashi tana jin zuciyarta na zafi, irin zafin da bata taɓa jin irinsa ba, duk tsawon lokacin data ɓata tana addu'a akan samawa yaranta miji nagari wanda za su huta su ji daɗin zamansu tare, sai gashi addu'arta ta amsu, amma kuma Abban Nimrah na ƙoƙarin dawo mata da wanan mafarkin nata. Lokacin da ya sanar da fatan Aryan sultan ta tsinci kanta a wata duniya daban, kanta na yawo a tsakiyar gajimare, badan komi ba sai dan kyakkyawar goben da ta ke gani tana ɗago mata hannu.
  
   Amma kwatam ya dakatar da wanan burin nata tun kafin ta isa inda take so.  Hakan ba zai taɓa faruwa ba, dole ta nuna masa cewar itama tana da hakki akan yaranta kamar yanda yake tunanin yana da akwai shima.

  Ɗakin da ya shiga ta ganshi zaune a bakin gadonta, yana jujjuya sandar da ke hannunsa, alamun yana cikin damuwa, damuwa mai yawa kuwa.

     "A sanina dai Nimrah bata da wani mijin da ka ce ka mata, kasancewar baka taɓa ɓoye min abun da ya shafeka ba, balle kuma wanda ya shafi yaranmu ba ABDALLAH!" Ta faɗi sunansa tana ƙarfafa shi a bakinta.
  Da mamaki ya ɗago yake kallonta, domin zai iya cewa ya manta yaushe ne rabon da ta kira shi da sunansa.  "Abdallah!" Ya sake mai-maita sunan akan laɓɓansa.

  Kai ta jinjina masa tana wurga idanuwanta sama zuwa ƙasa "Eh ko ba haka ba ne sunan naka?"
  Murmushi yayi domin ya gano bakin zaren, tijararta ce ta ke so ta motsa, domin shi kansa ya kwan da sanin wacece Habiba akan zafin zuciyarta da kuma fushi.
   "Haka ne sunana Habiba." Daga haka bai sake yin magana ba, ya ci gaba da juya sandar da ke hannunta.

    "Me yasa kace ka mata miji bayan babu wani mijin da ka mata Abdallah? Yaron kirki ɗan arziƙi wanda yasan darajar mutane ya taimake mu, ya kawar mana da furgicin tsoron rasaka da muke shirin yi, amma shine ka iya runtse idanuwanka ka datse duk wata igiyar yakanah da ke tare da kai wajen hana shi Auren Nimrah! Me yasa ka zama mutum mai saurin manta alkhairi ne?"

    Dakatar da ita yayi da hannunsa, duk maganar da take faɗa ko kaɗan fuskarsa babu damuwa ko ɓacin rai.
  "Tabbas ni mutum ne mai Yakanah har gobe Habiba! Asalima ni mutum ne wanda baya taɓa manta alkhairi da kuma riƙe muhimmancin alƙawari.
  Ke sanin kanki ne kinsan waye ni tun ƙuruciyata. Bana yin abu babu dalili. Allah ya sani na so ƙwarai ace yaron nan Sa'adiyya yake so ko kuma Zahra, wallahi da zan bashi su babu ja."
   "Hmm ita kuma Nimrah har ka ƙulla mata aure ne ban sani ba ko kuwa me kake nufi?"

   "Ban ƙulla mata aure ba Amma kuma na karɓi sadakinta a gabanki. Da hannunki na baki kika ƙirga sadakin auren Nimrah tun muna kano."
  Ɗagowa ta yi da mamaki a fuskarta, tana nuna kanta da hannunta "Ni kA bawa sadakin Nimrah na ƙirga da hannuna Abban Nimrah?"

  Kansa ya gyaɗa cikin bata tabbacin maganarsa "Ƙwarai ke fa Habiba. Zaki iya tuno abokina Haitham?"
  A furgice Ummah ta ɗago kanta tana kallon Abban Nimrah "Wani Haitham ɗin kake magana? Haitham da na sani wanda rabona da shi tun bayan ya zo barkar Nimrah. Me kuma ya kawo maganarsa yanzu?"
  "Kin tuna lokacin da ya zo da matarsa da ɗansa, har yaron ya ƙi yarda su tafi yana ruƙe da Nimrah a hannunsa?"

  Shuru Ummah ta yi kamar mai hango abun da ya faru a lokacin "Na tuna, ni ka rabani da waɗan nan mutanen, wanda sai dai muji labarinsu a duniya sunyi kuɗi sun manta da mu da rayuwarmu.
  Ni yanzu maganar Nimrah nake maka da kuma son jin mijin da ka mata aure har ka hana yaron kirki kamar Sultan aurenta."

   "Nima ai kaiki nake kan labarin, a lokacin da Haitham za su tafi ƙin yarda yayi ya bi iyayensa, har suka tafi suka barshi yayi sati ɗaya.
  Inaga wananma ba zaki manta ba, domin ko yaushe yana maƙale da ke da Nimrah har Allah yayi tafiyar su Haitham ƙasar Sudan saboda nauyinsa da gobnati ta ɗauka na karatunsa shi da iyalinsa, anan ya zo ɗaukan ɗansa wanda sai da aka kai ruwa rana sanna ya yarda ya bisu, bai ma yarda ba a lokacin sai da ya dage akan sai idan zamu aura masa Nimrah ne. Kin tuna abun da kika ce a  lokacin?"
  
  Zama Ummah ta yi kusa da Abban Nimrah tana kallon idanuwansa "Nace zan bashi auren Nimrah idan har ya yarda ya bi iyayensa."
  "Me kuma ya faru bayan nan?" Abbah ta sake tambayarta.

   Kanta ta dafe tana jin zuciyarta na harbawa kamar zata yi tsalle ta faɗo wajen "Agogon hannunsa ya cire ya bani na zinare, da kuma kuɗin aƙallah jaka shida a wancan lokacin. Yace na ajiye kuɗin sadakin Nimrah ne idan ya dawo zai tafi da ita."
 
  "Kin zo dai-dai wajen da nake so ki kai."
  "Kana so ka ce min wanan shine mijin da kake tutiyar ka yima Khadijatu? Bayan tun tafiyarsu har yau bamu da labarin inda suke balle mu gansu ma. Habaah wanan ai shirmen yarinta ne, shima ina da tabbacin ya manta."

   "Tabbas zai iya mantawa Habiba, amma kuma mu ai muna sane da alƙawalin da muka ɗauka akanmu? Kuma Allah zai tambaye mu akansa."
   "A'a Abban Nimrah, kada muyi haka da kai, domin Allah ba zai hukunta mu akan kuskure ba, inda ace Haitham na sane da alƙawarin nan to tabbas da ya nemo mu dan ya tunatar da mu."
  "Tunda shi ya manta mu ai sai mu tuna masa, domin har yanzu agogon ɗansa na hannunmu kamar yanda kuɗinsa ke ajiye a tare da ni."

     "Ta wata hanya zaka fara nemansa Abdallah?"

"Ta hanyar da muka fara." Ya ƙarasa maganar yana kwanciya da lumshe idanuwansa, hakan ya tabbatar mata da cewar ya gama magana da ita.

  "Turƙashi!"

🌷🌷🌷🌷
ALHUBBU DAYYI'AN NA KUƊI ne.
150 Singul group! Idan kuma VIP ne 300 ta bank!
acct no: 3051894647 Hajara Ahmad Hussain.
Skye/Polaris bank
Idan kuma katin waya ne 200 na singul group na VIP kuma 400 MTN.
Zaku biya shedar biyanku ta Number Whattsap ɗina. 08030990232 ko +234 703 513 3148

  Girmamawa

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now