SHA BIYAR

249 30 5
                                    


💔ALHUBBU DAYYI'AN👎

®NWA

©OUM-NASS

https://www.wattpad.com/story/234924568?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

Last free

 Mamakin da ke shimfiɗe akan fuskar Abba ya gaza ɓoyuwa, juya maganar yake yana ji kamar kunnuwansa suna masa gizo ne, ko kuma ya ji abun da ba dai-dai ba. "Kace me yaro?"

   Murmushi Aryan Sultan yayi yana shafa sumar da ta rage akan sa "Auren Nimrah nake so ka bani Abba. Idan har zuciyarka ta gamsu da nagartar da ke gareni. Wanan shine alfarmar da zaka min a rayuwa bayan ita kuma bana jin zan sake tambayarka wata alfarmar."

   "Har yanzu ji nake kamar kunnuwana na min gizo. Kamar majiyar da ke sadarwa a cikinta ta samu matsala.
  Yallaɓai ai ka yima Nimrah nisa sosai."
  "Abba ni ban yarda akwai nisa da wani fifikon da ke tsakanin musulmi da ɗan uwansa musulmi ba. Musamman da muka futo a jinsi guda na bil'adama. Kada ka tsaya ka duba matsayin da ke gareni, kayi tunani akan abun da ke zuciyata."

  "Buɗe min mota mu shiga gida yaro." Ƙofar ya buɗe masa, yayin da shima yake futowa daga cikin motar, yana riƙe da Abban a hannunsa, saboda rashin ƙarfin da ke tare da shi.
 
  A hanya duk wanda ya gansu sai ya tsugunna ya gaida Abba, da yawansu suna mamakin ganin yanda Abban Nimrah ya murmure yayi kyau.

  A hankali kuma yara suka farga da zuwansu, hakan yasa suka fara ihu suna murna da kiran sunansa.
  Kafin wani lokacin lungun nasu ya ɗauka, iyayensu kuma sun fara leƙowa suna ganinsa. Da yawan su suna masa barka da zuwa, sai dai ya gyaɗa musu kai yana murmushi, wasu kuma yana amsa musu.
  A haka har suka dawo gida, Nauwas ya zo da gudu ya rungume Abba, ya shafa kansa yana mai jin shauƙin sake kasancewa da autan ɗan nasa.
  Yaron da yake kwana da tunanin halin da zai shiga a duk lokacin da akace babu shi a duniya.

  Suna shigowa gida su Sa'adiyya suka tare shi ita da Zahra suma suka rungume shi "Ku masa a hankali kada ku kada shi ƙasa." Nimrah ta faɗa tana yamutsa fuskarta da kuma binsu da harara.

  Dariya Abba yayi mai sauti yana kallon yaran nasa da soyayyarsu ke buɗewa tana ratsa ko wani sashi na jikinsu "Kema da zaki zo ki yi abun da suka min bana jin zan kai ƙasa. Domin ƙafafuwana suna ɗauke da nauyin gaɓɓan jikina."
  "A'a Abba banda dai ni ɗin. Na tabbata da zan iso da tuni kayi baya kaima." Ta mayar masa da amsa dai-dai da maganarsa da ya mata cikin sigar tsokana.

    Ƙarasawa Abba yayi kusa da ita yana riƙe da hannun Nauwas  su zahra na gefensa kamar zasu shige jikinsa gaba ɗaya.

    Sai da ya matso kusa da Nimrah kamar zai wuce, sai kuma ya ɗan turata da kafaɗarsa, da sauri ta yi baya zata faɗi, ya tareta "Yo jarumata ya haka? Ko dai dama ƙafafuwan naki ne na jabi?" Abba ya faɗa yana tsayar da ita daga faɗuwar da ta ke shirin yi, fuskarsa ɗauke da dariya.

   Ƙafafuwanta ta fara bugawa ƙasa "Allah ban yarda ba wayo ka min Abba. Ai dai ba haka ake yi ba." Ta sake faɗa kamar za ta fashe da kuka.
   "Ahaf! Ko kin shirya ma sakamakon ɗaya ne." Ya faɗa yana dariya. Si Sa'adiyya ma suka saka mata dariya, itama Umma na taya su, dan wanan ke tabbatar musu da Abban nasu ya dawo da lafiyarsa. Domin duk lokacin da suka haɗu da Nimrah sai sunyi ɗan ƙaramin dirama. Saboda shaƙuwar da ke tsakaninsu.

   "Oh dan Allah ku bar min miji ya samu ya zauna, kun cika shi da surutu tun bayan zuwansa." Ummah ta faɗa tana dai-daita shumfiɗar tabarmar da  ta musu.

   Sai kuma suka ƙara sa dariya suna ɗaga hannunsu sama da matsawa Abba akan ya wuce ya zauna ɗin.
   Aryan sultan da tun bayan zuwansa gidan ya ke kallon su, hannayensa zube a cikin aljihunsa, da alamun basu lura da shi ba. Domin hankalunsu yayi kan Mahaifinsu, bai taɓa tsammanin a cikin talakawa za'a samu familyn da suke ƙaunar junansu ba kamar wanan, domin ko kaɗan babu gidadancin da ke tsakaninsu na wayewa.

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now