SHA UKU

214 26 2
                                    

💔ALHUBBU DAYYI'AN👎

®NWA

©OUM-NASS

https://www.wattpad.com/story/234924568?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

  Page 13

  Hannunsa ya bi da kallo yana jin zafin na ratsa sassan jikinsa, zafin ciwon da ke hannunsa da kuma zafin da zuciyarsa ke yi.
   Zama ya yi a bakin gadonsa yana ganin yanda jinin ke zuba kamar ansa gasar tseren zubarsa daga jikinsa.
 
    "Nimrah har yanzu kunnenki bai yi laushi ba! Har yanzu wanan hayaƙin na zagawa a kanki. Ni Aryan Sultan zan sauƙe miki shi." Ya gaɗa da amon muryarsa kamar tana gabansa.
 
  Tashi yayi akan ƙafafuwansa ya shige toilet ya sakarma kansa ruwa yana jin sauƙar ruwan na shiga ko wata ƙofa ta jikinsa, a hankali zafin da ke kansa ya fara sauƙa.
  Idanuwansa a lumshe suke hakan ya taimaka masa wajen hango abun da ya faru. Tunani yake da neman mafita guda ɗaya da zai sa ya sauƙar da kan Nimrah ƙasa, dole sai ya karya lagonta, karyewar da zai sa har ƙarshen rayuwarta ba zata manta da shi ba.
    Kashe ruwan yayi a lokacin da yaji ya samu mafita ɗaya tak. Dole ya kawar da tsarin da yake da shi ya cimma burinsa.
   
  ******

  "Nimrah kina ganin irin alkhairin da mutumin nan ya mana. Wai nikam a ina ma kika san shi har ya maida mu ɗaya daga cikin danginsu, ya hidimta mana da lafiyarsa da dukiyarsa." Ummah ta faɗa tana jujjuya abun a ranta da kuma aika kallon su Nimrah.

   Murmushi Nimrah ta yi tana shafa kanta da neman son faɗin abun da zai hau akan maganar ta ta "Abokin shugaban makarantar da nake aiki ne Ummah. Lokacin da naje nace a bani kuɗin aikina na watanni biyar shine ya nemi baya ni akan abun da zanyi da kuɗin na faɗa masa.
  Bai ce min komi ba har muka dawo ashe shi ya zo nan ya ɗauke ku?" Ta ƙarasa maganar tana dariyar yaƙe.

  "Lallai mutumin nan yayi nisa daga haɗuwa yayi irin wanan bajintar. Allah ya saka masa da alkhairi ya ji ƙan iyayensa."
  "Ameen." Suka amasa a tare idan aka ɗauke Nimrah da taji maganar ta gundureta.
  Kusan yini Ummah tayi tana magana akan Sultan wanda sai a lokacin ne su Nimrah suka san sunansa.
  A cikin kayan abincin da ya aiko mata sai da ta ɗiba ma gidan su Aziza aka kaimu mai yawa, sanan ta haɗa musu da kuɗi dubu Ashirin aka kai.
Ganin kaya da kuɗi yasa Mama ta zagayo gidan dan taji batu da bayani akan samuwarsu.

   Anan Ummah ta gyara zama ta shiga bata labari "Ikon Allah ashe dana a duniya yanzu ana samun masu irin wanan taimakon dan Allah?"
   "Ki bari kawai Maman Aziza ni kaina abun ya ɗaure min kai. Amma kuma da na tuna babu ta inda Allah baya taimakon bawansa sai naji a raina Allah ya ƙaddara haɗuwarsu da Nimrah ne dan ya taimake mu."
   "Haka ne kuma. Babu ta inda Allaha baya ikonsa. Muma gashi za mu ci albarkacin masu albarka." Ta faɗa tana kaɗa kuɗin da ke hannunta.

    Dariya Umma tayi cike da jin daɗi "Ki bari Maman Aziza ai abokin kuka shi ake faɗama mutuwa. Ni ba zan iya cinye wannan garar ba tare da kuma kun cita ba. Allah dai ya sauwaƙe ya rabamu da rowa."

   "Ameen ya Allah. Nagode sosai Ummansu lallai yau za mu sha romo." Ta ƙarasa maganar suna kashewa da hannunsu a tare.
  
  Daga haka suka ci gaba da hirarsu, kafin daga bisani kuma Mama ta tashi tana ƙara jaddada godiyarta ga Ummah.

   "Nimrah mutumin nan fa ya samu fada mai ƙarfi a wajen Ummah. Idan har ta fahimci abun da ke tsakaninki da shi karonku ba zai yi kyau ba." Aziza ta faɗa cikin sanyin murya tana kallon sashen da Ummah ta ke, wanda har a lokacin bata rufe bakinta ba.

   "Uhmm Aziza kuɗi ba abun da baya sawa mutum. Amma ina fatan kada kuɗinsa su ruɗar min da mahaifiyata, domin a yanzu babu mutumin da na tsana fiye da ARTAN SULTAN."

   "Idan kuma ya zo yace yana neman aurenki ba?"
  Dariya Nimrah ta yi mai sauti, irin dariyar da ta manta yaushe rabonta da yinta. Kallonta Aziza take tana mamakin abun da ya sa Nimrah irin wanan dariyar, domin a saninta da ita bata taɓa yin dariya mai kama da wanan ba, sai idan har abu ya kai maƙura.
  Nuna kanta ta yi da hannu "Ki bar wanan mafarkin Azizaty! Aryan Sultan ba zai taɓa zuwar min da magana makamanciyar wanan ba."
   "Ke ya kamata ki farka daga wanan mafarkin naki Nimrah. Abun da Aryan Sultan ke faɗa a kanki ba shine a zuciyarsa ba."

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now