TARA

253 34 4
                                    

💔ALHUBBU DAYYI'AN👎

®NWA

©OUM-NASS

https://www.wattpad.com/story/234924568?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

Page 9
 
   ARYAN SULTAN.

Tunda ya ja motar yake murmushi musamman ganin yanda Nimrah ke binsa da gudu tana ihun kiran sunansa.
  Yasan ko a yanzu ya karya mata da zuciya, ya mata abun da ya hanata samun nutsuwa, a kallon farko da ya mata ya ganta a birkice idanuwanta duk sunyi luhu-luhu kamar yanda fuskarta ta yi jajur, wanan shine burinsa! Wanan shine abun da yake muradinsa ganin faɗuwar Nimrah akan ƙafafuwansa.

   Fuskarsa ya shafa yana faɗaɗa murmushi akan kyakkyawar fuskarsa "Wanan ba komi ba ne Nimrah! Wanan wata sabuwar shimfuɗa ce a cikin ranakun baƙin cikinki na duniya." Ya faɗa yana ƙara gudun motarsa har ya shiga Katsina yana jin zuciyarsa fes da farin ciki.

  A hanya ya tsaya a wajen masu saida kayan marmari ya siyi dangin su lemo, ayaba, Abarba, da kuma tuffa, duka da yaso haɗawa da kankana amma kuma ta yi masa nauyi da yawa, dole ya haƙura ya karɓi waɗan nan da aka cika masa leda har guda uku da su.
Daga nan ya biya su kuɗinsa ya shige motarsa.

  Wani babban gini ya gangara da aka yi manyan rubutu a cikinsa *NAGARTA GENERAL HOSPITAL* Tun daga bakin get ma'aikata suka shiga duba shi har sai da ya ɗaga musu wani shuɗin kati, wanda yake alaƙanta shi da zuwa dubiyar da yayi.
  Da ace baƙon zuwa ne dole za su caje shi tsaf daga shi har motarsa, amma yanzunma sai da suka sake duba bayan motarsa sanan suka barshi ya wuce.
  Babbar asibitice ta masu kuɗi a garin, wanda ta haɗa manya likitoci daga ƙasashen duniya, daga turawa zuwa indiyawa kowa da sashen da yake kula da su.
   Wajen da aka tanada domin fakin Aryan Sultan ya shigar da motarsa, a hankali ya futo yana takunsa cikin ƙasaita, wanda yake ɗabi'arsa ne. Fuskarsa babu walwala ko kaɗan har ya shiga wani sashe, sai da ya hau saman bene sanan ya ci karo da jerarrun ɗakuna. 
   ROOM 114 ya tsaya, a hankali ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, sanan ya tura ta bakinsa ɗauke da sallama.
  Da gudu Nauwas ya taho wajensa ya rungume shi. Shima rungume shi yayi yana shafa kansa "Kana lafiya Abokina?"
  Ya faɗa da sassanyar muryarsa, kai ya Nawwas ya gyaɗa masa "Ina lafiya uncle Aryan." Ya faɗa yana amsar ledar da ke hannunsa, miƙa masa yayi yana shafa kan Nauwass ɗin, sosai ya ke jin yaron a zuciyarsa, domin bashi da wuyar sabo.

  Ƙarasawa yayi wajen su Umma da tun shigowarsa take murmushi, hannayensa na cikin ruƙon Nawwas.
Har ƙasa ya risina ya gaida Umma, ta amsa da yalwatacciyar fara'a akan fuskarta.
  "Ya jikin Abba?" Ya faɗa yana kallon gadon da Abban ya ke kwance, an saƙale ƙafarsa a sama wanda aka naɗeta da bandeji da wani ƙarfe a jikinta, yayi da shima hannun nasa yake naɗe da bandeji.
  "Da sauƙi sosai Sultan. Dan ɗazu ya farka har ruwan shayi ya sha. Maganin da ya sha ne kuma yasa shi komawa barci.
  Ya ƙoƙari? Baka gajiya da hidima muna da komi anan da ka siyo mana jiya bai ƙareba, dan wasu ma sai a firji Sa'adiya ta saka su. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi."

Murmushi Aryan Sultan yayi yana shafa fuskarsa, ba tare da ya amsa mata da maganarta ta ƙarshe ba yace  "Alhamdulillah! Allah ya ƙara masa lafiya."

  "Ameen suka amsa a tare."

"Ina yini Uncle!" Sa'adiya da Zahra suka faɗa a tare.

  "Lafiya lau." Faɗa yana kallon agogon dake saƙale a hannunsa, sanan ya kalli Umman.

  "Inaga ya kamata su Zahra su koma gida gobe saboda makarantarsu. Kema sai ki koma gida zan kawo wanda zai na kula da shi, kasancewarsa namiji, ciwon namiji kuma dole sai namiji ɗan uwansa.
  Duk bayan kwana biyu sai kina zuwa duba shi, hakan zai fi akan abar Neemrah ita ɗaya a gida." Ya faɗa yana nazartar Umman nasu, da tayi shuru tana jin maganar tasa da ƙamshin gaskiya.

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now