BIYU

410 54 6
                                    

💔ALHUBBU DAYYI'AN 👎

  ®NWA

©Oum-Nass...

page 2

Gudun motarsa na tafiya da gudun da zuciyarsa ta ke, yana jin kamar zata yi tsalle ta faɗo daga maɗaukarta. Har a lokacin yana jin sabon ƙunci na ziyartar tasa zuciyar, anya tunda yake a duniya antaɓa nuna masa koda yatsa ne? Ya kasa ɗauke hannunsa daga kan kuncinta, raɗaɗin da ke kan fuskarsa ya ɗauke ya koma cikin zuciyarsa.

   A haka ya isa katsina mutane da yawa suna bashi hanya saboda ganin mahaukacin gudun da yake, da yawa sun san cewa ikon Allah ne ya kaishi gida lafiya ba tare da motarsa ta yi adungure ta kife da shi ba.
  Wata ƙatuwar unguwa ya shiga mai ɗauke da manyan gine-gine a cikinta, wanda kana ganinta kasan unguwar manyan mutanen da suka tara suka kuma jiƙu ce.
  Sai dai duk da haka, akwai ƙaton gidan da ya zama futula a cikin sauran gidajen, ya kuma zama na sama, abun kwatance a layin nasu. Anan ya tsayar da motarsa yana danna honn kamar zai cire shi daga ma'ajiyarsa.
  Da gudu mai gadin ya wangale masa bakin get ɗin hakan yasa ya kwashi motar a guje kamar zai hankaɗe mai gadin gidan, badan yayi tsalle ya zura da gudu ba to da babu abun da zai hana ya masa ɗiban karen mahaukaciya.
  Ajiyar zuciya ya sauƙe lokacin da ya tabbatar ya tsira da numfashinsa "Oh Allah ya so ni da rahamarsa! Ko wa ya taɓo wanan masifaffan miskilin? A haka ma ya muka tsira da wulaƙancinsa." Ya faɗa yana leƙa waje kamar zai ga abun da aka masa ɗin.
  Sai dai bai ga kowa ba, hakan yasa ya maida ƙofar get ɗin ya rufe, yana ƙara sauƙe ajiyar zuciya, yana dafe da ƙirjinsa, shi kaɗai yake huci kamar da ya shekara yana gudu.
  
  A fusace ya futo a motar ya shiga ainihin korudon da zai sada shi da gidan nasu, yanda yake takunsa da ƙarfi da kuma yanda fuskarsa ta ƙara zama ja, idanuwansa suka rikiɗai daga kalarsu na farare suka koma launin jajaye, ko kaɗan babu walwala a tare da shi asalima fuskarsa komawa tayi kamar hadari, hakan ya isa yasa mutum ya gane cewa ransa a ɓace ya ke.
  Ma'aikatan gidan suna faman gaida shi amma bai kalle su ba balle yasan da wanzuwarsu a wajen.
  
  Buɗe ƙofar palon yayi bakinsa na ɗauke da sallama a hankali, duk da yana cikin wani yanayi amma hakan bai hana shi yin sallama ba, a palo ya tadda iyayen nasa a zaune suna hira cikin walwala.
  "Sannu Mom! Sannu Dad!" Ya faɗa yana shige su.
  "ARYAN SULTAN!" Dad ɗinsa ya faɗa cikin muryarsa mai amo.
  Hakan ya sa shi ya tsaya cak, ba tare da ya juyo ba, dan yasan duk lokacin da Dad ya kira shi da wanan muryar akwai abun da zai faɗa masa, kuma abu mai muhimmanci wanda baya son wasa a cikinsa.

"Zo ka zauna anan." Ya faɗa cikin muryar bada umarni.
  Dawowa yayi ya zauna a kusa da shi, kansa a ƙasa, yana jin wani zafi na ƙara fitowa a ƙasan zuciyarsa "Ka je kaga yarinyar?"
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya girgiza kansa "Amma me yasa? Bayan kuma na jaddada maka muhimmancin da ke cikin wanan al'amarin. Ina son na ƙarfafa zumunci a tsakanina da aminina wanda zuciyarsa ta ke cike da wadatuwa, ya kuma gina yaransa akan kyakkyawar mu'amula da sanin ya kamata." Ya faɗa cikin faɗa daga bisani kuma ya koma lallashinsa.

  Miƙewa Aryan sultan ya yi, ba tare da ya kalli Mahaifin nasa ba "Bana sonta ne Dad. Ni ban shirya aure yanzu ba." Yana gama faɗar haka ya wuce ya barsu baki buɗe.
  Mamakinsa ne ya ke son daskarar da su a wajen "Dama ai ba kai zaka shirya aurenba, mu ne zamu shirya maka, haka kuma mu muka san abun da ya dace da kai ɗin." Dad ya faɗa cikin muryar da ta cika falon nasu da amo, zai iya cewa wanan shine karo na farko da ya taɓa yima ɗan nasa faɗa mai ƙarfi haka, shi kansa ba zai ce ga dalilinsa na dagewa akan ya auri 'yar amininsa ba, amma kuma wani sashi na zuciyarsa na nuna masa girman al'amarin.

   "Haba mana Alhaji! Ka yi haƙuri kabi lamarin a hankali, na tabbatar da zai haƙura ya bi zaɓin da ka masa. Aryan bai taɓa tsallake umarninka ba." Mom ɗinsa ta faɗa cikin muryar lallashi da kuma son ganin ta sauƙo da mahaifin nasa daga dokin zuciyar da ya hau.
   Murmushi yayi a lokacin, kana ya shafa sajen da ke kan fuskarsa da ya zama da ratsin fari a jikinsa.
   "Nima bana son na matsama Aryan akan maganar yarinyar nan. Amma kuma zuciyata ta ƙi haƙura, gani nake wanan ne abun da zan ma Mu'az na saka masa akan kyautatawar da ya min. Ina kuma kwaɗayin samun jikokin da za su fito daga tsatsonsa."
   Itama murmushin tayi "Na sani Alhaji, na daɗe da haddar wanan burin naka, ina fatan kuma Allah ya cika mana shi.
  Ba naje na duba Aryan ɗin." Ta faɗa tana tashi akan ƙafafuwanta, yayin da ya bita da rakiyar ido cike da soyayyarta a zuciyarsa.
  A duniya ba abun da yake so da ƙauna kamar iyalinsa, da kuma yara, sai akayi rashin sa'a yaransa biyu daga Aryan sultan sai ƙanwarsa Nasreen. Wadda tazarar da ke tsakaninta da Aryan ta kai ta shekara goma, dan har sun fidda rai akan wata haihuwar amma kwatsam sai ga ciki farin cikin da suka yi ba zai musaltu ba, tunda ga wanan lokacin kuma sai haihuwar ta tsaya musu cak, basu ƙara yinta ba, wanan yasa suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗorata akan yaran nasu.

  ***
Tun bayan shigarsa ɗaki ya rasa me yake masa daɗi, abun duniya ya taru ya masa yawa, shi maganar Dad bata dame shi ba, kamar yanda ya damu da sanin wacece wanan yarinyar?
  Tambayar da take damun zuciyarsa kenan, fuskarsa ya ke gani a gaban madubi yana shafa sashen da ta mareshi a cikinta, ganin wajen yayi ya sauya kala ya ƙara zama ja fiye da kalar fatarsa.
   Idonsa ya runtse kafin ya kaiwa madubin nasa naushi, nan take ya tarwatse ya ji masa ciwo a hannunsa, amma kuma bai ji wanan zafin ba, bai kuma ji a hannunsa cewar ya raunata kansa ba.
  Kwanciya yayi akan gadon da ke ɗakin yana ganin komi na ɗakin na juya masa da fuskar yarinyar, kunnuwansa kuma suna masa amsa kuwwar maganarta _'Saboda titin ba na babanka ba ne! Ba a liƙa allon sanarwar akan hanyar babanka ce ba!'_ Wanan maganar ita ke ta dawo masa da yi masa yawo akansa.
  Kansa ya buga da hannunsa yana jin takaicin barinta da tayi ta tafi, bai san komi a kanta ba, bai san labarinta ba.

  "Subhanallah! Aryan me nake gani haka a hannunka?" Mom ta faɗa cikin ruɗewa saboda jin da tayi shuru tana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma yaƙi kulata, shi yasa ta shigo. Sai kuma idanuwanta suka mata mummunan gani, jinin da ke ɗiga a hannunsa yana malale ɗakin nasa, da kuma tarwatsattsen madubin da ta ke da tabbacin shi ya da ke shi.
  Girgiza shi ta shiga yi tun ƙarfinta amma kuma bai san me take ba, jinin da ya ke zuba ya fara ɗaukansa.
Da gudu ta sauƙa ƙasa ta kira Dad cikin tashin hankali ya koma ya kira direbansa, haka suka kama Aryan suka sashi a mota aka wuce da shi asibiti.
  Wata haɗaɗɗiyar asibiti suka je, wanda idan har ba cikinta ka shiga ba, ba zaka ɗauka cewa asibiti ba ce, haka kuma duk ma'aikatan da ke asibitin turawa ne, kaɗan ne a cikinsu hausawa.
  Wanan itace Asibitin da suke zuwa ana duba lafiyarsu. Cikin hanzari likitocin suka janyo gado aka ɗaurasu akai, suka shigar da shi emergncy.
  Dad da Mom sai kai kawo suke yi, a tsakanin wajen, ita kam Mom banda kuka ba abun da take, akai-akai take matse hawayen kan fuskarta.

  Bayan mintuna talatim likitocin suka fara futowa a ɗakin, anan su Dad suka tare su suna tambayar su "Ya ɗanmu ya ke?"
  Kallonsu likitan yayi sanan ya tambaye su su waye ɗin marar lafiyar "Iyayensa ne mu?"

"Ku biyo ni office."
Binsa suka yi ofishin nasa, yana nuna musu kujerar zama, duk jikinsu a sanyaye yake hakan yasa suka zauna.
  Sai da likitan yayi 'yan rubuce-rubuce sanan ya ɗago kansa yana kallonsu.
   "Ya akayi kuna iyayensa kuka barshi cikin damuwa? Wani abu ya faru da shi na firgici wanda ya haddasa masa ɓacin rai. Sanan kuma jini ya zuba a hannunsa da yawa, wanda ya kusan salwantar da rayuwarsa, da baku kawo shi akan lokaci ba da komi zai iya faruwa da shi.
Mun cire masa gilashin da ke hanunsa an masa ɗinki a wani wajen in sha Allah muna sa ran zai farka nan da awanni biyu.
  Dan haka ku kiyayi duk wani abun da zai sake ɓata masa rai, dan zuciyarsa na da saurin tashi."

   "In sha Allah Dakta mun gode ƙwarai." Dad ya faɗa duk jikinsa yayi sanyi, sai yake ga kamar shine silar faruwar komi, shine ya janyo ma ɗansa ɗaya tak wanan matsalar saboda dagiyarsa.
  "Ko za mu iya ganinsa Dakta."
Kai Dakta ɗin ya gyaɗa musu "Zaku iya shiga, amma kada kuyi abun da zai tada shi."
  "Mun gode Dakta." Suka faɗa a tare suna miƙewa akan ƙafafuwansu.
   A haka suka fito a office ɗin likitan suna jin ko wata laka ta jiknsu na sanyi.

   Lokacin da suka shiga ɗakin da yake yana kwance, hannunsa a saƙale da bandeji, fuskarsa ta ƙara yin fayau da ita, wanda yake nuna raunin jinin da ke ga hannun nasa.
    A hankali suka ƙarasa kusa da shi, Dad ya shafa kansa "Indai akan maganar aurenka ne ka shiga wanan halin, to na haƙura na janye. Allah ya baka wata matar ta gari wadda xata so ka da dukkanin zuciyarta.
  "Ameen." Mom ta amsa cikin tausayawa yaron nata.

  Sai da suka yi kwana ɗaya sanan aka sallamesu, a cikin wanan kwana ɗayan iyayensa sai nanna-nannan suke da shi, duk wani abun da zai ɓata masa rai kawar da shi suke.
  Tun anan kuma Dad ya ce masa ya haƙura akan maganar aurensa duk sanda ya shirya dan kansa sai yaje ya nemo matar da ransa ya ke so.
  Wanan labarin ya ƙara sanyaya ma Aryan zuciya, a cikin kashi 100%  na damuwarsa yanzu ya koma 60%, damuwarsa shine inda zai je ya nemo yarinyar nan, ya kuma san wacece ita.

*****
Bayan kwana biyu.

  Jikinsa ya warke har ya koma bakin aikinsa, shi ke jan ragamar kamfanonin mahaifinsa.
  Amma kuma ya kasa manta yarinyar, haka yasa ya yanke shawara ya tafi FASKARI dan ya samu amsar sa, ya kuma san wacece yarinyar dan ya ɗauki fansar abun da ta masa, fansar abun da zai shafe rayuwarta yana caccakar ruhinta har ƙarshen rayuwarta.
  Zai haƙa dogon ramin da ya san ba zata iya futo a cikinsa ba......

🌷🌷🌷🌷🌷

Tofah me zaku ce a wanan chaftar?

#AD
#CMNTS, LIKE AND SHARE
#NWA
#GIRMAMAWA
#DABANNE

   OUM-NASS

ALHUBBU DAYYI'ANWhere stories live. Discover now